Sashe 70
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Bayan an dawo daga kaisa su Jawaad basu tafiba, suna a cikin garin har gabanin magriba ana amsar gaisuwa dasu shi dasu Hafiz, Jabeer, Aliyu, sai Bilkisu. Sojojin da sukai musu rakkiya da Baba ƙaura sun wuce tun bayan da aka dawo daga binnesa. Rose ma lokacin da su Sir Ahmad zasu tafi dasu Alhaji babba bayan sallar la'asar Jay yace ta bisu. Bilkisu kuwa tana ciki tare da matar Gimba, batasan yaya akai sukasan ita matar Jawaad baceba, sai kawai ganitai anata nunata da faɗin itace matar ogan marigayi Gimba. Haka zasuyita jera mata addu'a da yabon halin Jawaad bisa ɗawainiya da taimakon da ƙauyen yake samu daga Jawaad ɗin ta dalilin gimba. Haka sukaita mata komai a girmame tamkar tafi kowa. Ita harma kunya ta komaji akan yanda suke matan.
Wajen ƙarfe shida saƙo ya iso mata akan ta fito inji boss zasu wuce. Haka ta tashi ta kimtsa jiki a saɓule dan ta amshi hijjab ɗin matar gimba ta saka tun ɗazun saɓanin da da take da baby hijjab kawai. Sunata mata godiya da addu'a, ƙannensa suka rakota har waje inda motar da zasu tafi take.
Sau ɗaya na kalli Boss na ɗauke idanuna saboda wani irin tausayi yake bani, na ƙaraso inda yake tsaye na gaishesu tare da sake musu gaisuwa, murya cike da damuwa ya amsa mani yana min nuni dana shiga motar daya buɗemin. Ni da shi da Jabeer ne a baya, ina jikin ƙofa yana tsakkiya Jabeer kuma a ƙarshe, sai Aliyu da zai ja motar Hafiz na gefensa. Haka muka wuce sunata mana addu'oin sauka gida lafiya.
Sosai Aliyu ke sharara gudu kasancewar garin yay wani irin ɗaurewar hadarin farkon damina mai cike da iska a ciki, babu mai magana a motar sai zancen zuci, cikin awa ɗaya da mintunan da bazasu gaza ashirin da bakwaiba muka iso cikin gari, zuwa lokacin garin ya sake yin duhu, gana hadari gana magriba, anata salloli a masallatai. Nayi zaton masarauta zasu kaini, sai naga an nufi gidansu Boss, koda mukazo gate sai yace basai Aliyu ya shiga da motarba bara mu sauka anan su wuce kar hadarinan ya riskesu..................✍
(Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka kashe ɗan fir'auna, miyasa suka kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba.)
dolene jiya kushiga ruɗani akan mutuwar ɗan fir'auna bayan farkon page na nuna bai mutuba, nima sai a Comments ɗinku na fahimci kuskuren danayi na koma na duba page ɗin, wlhy hankalina sam bai kaiba ko'a wajen editing, rayuwace abubuwa sunma ƙwaƙwale yawa, kana gabas tunaninka na yamma, amin afuwa ɗan fir'auna bai mutuba🤦🏻. anahin abinda naso sakawa a
wajen shine (Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka so kashe ɗan fir'auna, miyasa sukaso kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa masu son kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba).🤗🙏🏻
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/18/2020, 3:50 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Ƙwai Cikin Ƙaya
.
Book Two
.
Billyn Abdul:
.
Page 31
.................Daga can akace “goro yaron alkairi”. Ya cigaba da faɗin, “Da alamafa damunar bana zatai ɓarna, dan na hangi ɗakunan mutane da yawa sun buɗe ta sama batare da sun fargaba, kuma lallai bular zata zubda yoyon ruwan da zai iya haifar da ambaliya”. dariya ta tuntsure dashi daga can, tace, “Ɗan alkairi kana nufin dai dara zataci gida kenan, ɗan zaki yafara buɗe idanunsa ga rundunar kuraye masu gudun tseren neman abinci koda bai kasance halalinsu ba?”. “Ƙwaraima kuwa mamana, bana sanar miki wani ƙwai dake cikin ƙaya ya bayyana ba kwanakin baya, kuma duk haɗarin maciji ya gama shawaginsa ya barsa dan ya gagara haɗiya”. “ƙwaraima kuwa ka sanar min da wannan, a farautar zaki yaci karo dashi kenan matsayin abinci?”. “Hhhhh mamana kina birgeni da saurin ramfo zance, to wlhy ina mai tabbatar miki da hakaɗinne ta kasance, tsagerun dawa na tunanin Zaki yafi ƙarfin ruwan ƙwai sai gashi harma yana ƙoƙarin damƙosa cikin ƙayoyi”. “Kai ɗan alheri karka sa farin ciki ya karni yau ɗinan ban kalmashe bakin buhun dana farama ɗureba, yanzu dai ina fatan kana hanyar gidane?”. “Hasashenki baya zama kuskure mamana, mu haɗu acan na baki sauran bayani, dan kuwa garin bita da ƙullin ƴaƴan kura sun rufta damisa da ƴaƴan fadarta a ramin ɗan zaki, shiko ya afka musu ƙasa yasa ƙafa yatake harma da share wajen kwanciya domin buƙatar hutu”. Wata irin dariya ta shigayi mai cike da nuna tsantsar farincikinta data daɗe da mantawa da samunsa, yau ɗan nata ya biyata da daddaɗan labari. tace, “Ɗan albarka wannan zinaran kalamai naka sunfi ƙarfin saurare a salula, garzaya gida nima ina gab da iskoka, dan tun safe na nema alfarma ga Uwargida sarautar mata akan zuwa na duba mai babban suna”.
“Babu damuwa mamana ina tsumayenki acan, alkairin ALLAH ya cigaba da baibayeki tare da nasarar cigaba dayin haƙo a ramin azzalumai batare dasun fargaba har sai kinkai musu wuya lokacin sungama shiga tarko”.
Murmushi tayi daga can tana faɗin “Amin ɗan albarka” kafin ta yanke wayar, shima ya tura tasa a aljihun yana murmushi. Cigaba yay da tafiya harya fito titi, napep ya tara takaisa inda motocin ƙauyensu ke tsayawa, duk da garinsu ba ƙauye bane sosai dole muce dashi ƙauye, dan kuwa a ƙarƙashin wata ƙaramar hukuma yake, saidai yamafi l.g ɗin dukkan abubuwan cigaba, gashi a bakin titi kuma babu nisa da babban birin jiharsu. A mamakinsa ana saukesa falletsetsiyar mota na cin birki a gabansa, baiyi mamakin hakanba, dan kasancewarsa drivern boss yanada alaƙa da sanin mutane manya sosai ta fannoni da dama, lokaci-lokaci kuma yakanci karo da wasunsu koda ace shi ya mantasu dan dama dalilin shige da ficin boss na aiki yake sanin nasu. Wanda ke ciki ya sauke gilashi yana murmushi, sosai gimba ya zaro ido irin na bazatar ganin wanda bai zatoba, “Lah Ɓaleru! Dama rai kanga rai? wane mai gangancine yay kasadar baka idanunsa kaketa haska hanya dasu cike da ɗaukar faɗi?”. Dariya na cikin motar yay har yana bugun sitiyari, yace, “Gimba kaidai baka rabo da shaƙiyanci, kasan ɓalerun naka da shige-shige, ko iska ta shafamin lafiya. Daga ina haka zuwa ina?”. Gimba yace, “Wlhy gida nai, zamuje hutun ƙarshen mako domin ganawa da iyali”. Ɓaleru yay ƴar dariya da faɗin, “Mutumina baka wasa da gona, shiyyasa kullum gatanan cikin yabanya take, banga laifinkaba, yi birgimarka ka more mata sune jin daɗin duniyar ai dama. Shigo mu haura dan nima dai can na nufa ɗin”. Babu musu Gimba ya shiga yana maida masa murtanin shaƙiyancinsa, saida suka ɗauki hanya ɓaleru yace, “Nifa mamaki oganka ke bani, gashi jinin manya, ɗan tsohon shugaban ƙasa mai tarin dukiya, shi kansa ƙwaron kansane dan ya tara bayan wanda aka tara masa, amma abin mamaki kamar shima baya mora balleku ƴan muna jira ALLAH ya baka mu samu”. Murmushi gimba yayi, cikin son kare boss ɗinsa yace, “Ai abin nagartace, sai dai irinku ƴan ƙwanta ka mutu mu haye basa ganewa, komai boss yake da tsari a cikinsa, shi bai ɗauki wannan dukiyar da ta tsolema kowa idanu wata tsiyaba, marasa nasaba da itama amfanuwa suke da tagomashinta amma ta ƙyaƙyƙyawar hanya, bai yarda da almubazzaranci ba, amma shi kogin
e maiba na kus