← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 168

Sashe 135

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

           Hankali tashe Anum ta ƙwala kiran sunan Abbu da Anuwar dake falo suna jiran shayi, har rige-rige. isowa suke cikin kicin ɗin, ganin Umm-Anun yashe a ƙasa yay masifar ɗaga hankalinsu, Anuwar ya tallafo kanta ya aza bisa cinyarsa yana mai fashewa da kuka, Abbu ne yay ƙarfin halin komawa ya ɗakko goran ruwan zam-zam ya dawo, a hannu ya zuba ya shafa mata a fuska. Ta kawo wani irin nannauyan numfashi da gurnani, ƙara ɗiba yay ya zuba mata a fuskar, nanma tagwayen ajiyar zuciya ta sauke a jajjere. Matsawa yay sosai yana ambatar ainahin sunanta, BILKEESU! BILKEESU!!, BILK...... Da sauri ta buɗe idanunta tana amsawa da “Na'am BAB......” sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa ta kafe Abbu da ido, saurin janyewa tai ta maida kan Anum, sai kuma ta kalli Anuwar da take a jikinsa. Cikin ɗan rawar baki tace, “Jawaad!”. Abbu da Anuwar suka kalli juna, sai kuma suka kalleta, zaune ta tashi tana raba idanu a kansu, sai kuma tai saurin dafe kanta tana faɗin, “Ya ALLAH”. Riƙe mata kan Abbu yayi yana faɗin, “Sannu, kinga tashi muje ɗaki”. Bata musaba ta yarda ya taimaka mata suka fita, sai faman lumshe idanu take saboda jiri.
     Kwantar da ita yay a saman gado ya ɗaura kanta bisa cinyarsa, umarni ya bama Anuwar ya ɗakko masa wani magani a ɗakinsa, babu jimawa Anuwar ya dawo, cayay ya zubashi a abin turare, nan danan hayaƙi mai ƙamshi ya fara tashi a ɗakin, shi kuma ya shiga karato addu'oi yana tofa mata. Cikin mintunan da basu gaza biyarba barci yay awan gaba da ita. Duk ajiyar zuciya suka sauke, kafin Abbu ya gyara mata kwanciya suka fito falo suka barta.
     Cikin ɗaurewar kai Anuwar yace, “Abbu Yah Jawaad fa ta kira”. “Naji Anuwar, amma lallai akwai wani abinda ya faru inaga, dan yanayinta yayi kama dana wadda ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, dan a farko sunan baba zata kira ganin nine yasa tai shiru”. “Abbu to kona kira Yah Jawaad ɗin muji?” kansa ya ɗaga masa alamar eh.

★★★★★★★

         Su Jawaad na zaune a falon Alhaji babba sun rufu kan bilkisu da keta juye-juye a ƙasa da kukan kanta suna mata addu'a kira ya shigo wayarsa da Numbers ɗin ƴan saudiyyane kawai a ciki, ɗagawa yay yana miƙewa, daga can Anuwar ya gaishesa, sama-sama ya amsa masa da tambayar “ina Ummuna?”.
      “Gata a kwance barci ya ɗauketa, dan tana kitchen zata haɗa mana shayi kawai sai ta faɗi, ALLAH yasa Anum na tare da ita, sai dai abin mamaki ana saka mata ruwa ta kawo numfashi saita fara ambatar Baba saboda Abbu da ya kira sunanta, ni kuma tana kallona saita kirani da sunanka”. Lumshe idanu Jawaad yayi hawaye masu zafi suka ziraro masa saman fuskarsa, kafin yace wani abu yaji maganar Alhaji babba a bayansa. “Mi kuke ɓoyemani?”.
     Duk da gabansa ya ɗan faɗi sai ya matsa ya rungume Alhaji babba ya saki wani irin kuka mai tsuma zuciya wanda bai taɓa sanin ya iya irinsaba. Cikin matuƙar tsorata Alhaji babba shima ya riƙesa hannu bibbiyu, “Muhammad karka rikitar dani, minene ya faru dan ALLAH? Kai ne da kuka kuma?”. “Abubuwa da yawane suka faru baba, sai dai dan ALLAH kaimin alfarmar yimaka bazata a kansu daga nan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”. “Namaka Jawaad, ALLAH yay maka albarka”. Ɗagowa Jay yayi yana jinjina kai, Alhaji babba ya share masa hawayen, da ƴar tsokana yace, “Yau maza sun koma mata kenan?”. Murmushin ƙarfin hali kawai Jay yay masa, amma bai iya cewa komaiba.
      Ciki suka koma inda suka samu Bilkisu taɗan samu barci, tana jikin Batool da bata wuce gida ba. Kallonsu yay sannan ya kalli Bilkisun, “Baba bara mu wuce gida, shi baba zai kwana nan gidan kafin zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu, kema Batool ki tashi kije gida dare nayi, amma dan ALLAH karki gayama su Ummah komai sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zakuji koma mike faruwa”. Kanta ta jinjina masa, tace “To ya ya za'ai da mai sunan hajiya, bai kamata a tada taba tunda yanzu ta samu barcin”. “Karki damu bara na ɗauketa kawai”.
         Cak ya ɗauki bilkisu duk da yana jin nauyin su Alhaji babba, sai dai babu yanda zaiyi idan ba haka ɗinba. Sallama yay musu ya fito, Batool dake biye da shi ta buɗe masa baya ya kwantar da ita, sannan ya koma mazaunin driver ya zauna, ita kuma ta nufi inda driver ke jiranta. Kusan tare suka bar anguwar. Sai da ya isa gidane yama tuna da Sadiq da ya baro a office, hankalinsa a tashe ya ɗauka waya yay kiransa, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, “Sadiq badai kana nan kana jiranaba har yanzun a station?”. “Ina nan wlhy Oga, harma dasu oga Aliyu”. “Ya salam, kayi haƙuri kaji, ka tafi gida kawai dare yayi, suma kace musu ina gida karsu damu”. Daga can Sadiq yace, “To oga”.
     Bayan ya ajiye wayar ya buɗe ya fito, sake ɗaukar Bilkisu yayi zuwa cikin gidan, ya shinfiɗeta a gadon ɗakinsa sannan ya koma motar ya ɗauka wayoyinsa. Kiran Anuwar ya sakeyi, ya tabbatar masa har yanzu Umm-Anum barci take, Abbu ya bama wayar sukaɗan yi magana sannan ya kashe, ya zauna a bakin gadonsa ya tsirama Bilkisu dake barci ido, gani yay harma taɗan rame masa a kwana biyun nan, wani tausayinta ya kamashi, matarsa ta isa a kirata jaruma a ko ina, shi harma baisan yanda zai musalta yaya ya keji a kanta ba, gadon ya hau ya rungumeta a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya a jajjere kamar wanda ya haɗiyi wuta.

          DAREN ALKAIRI KO RUƊANI?.

     Dolene mu ambaci wannan dare da sunaye masuma yawan da sukafi haka a ɓangarorin mutane masu yawa. Jawaad, Alhaji babba, baba maigadi, Maman Amina, Yaya sule, Abbu, Abu-Siddiq, Anuwar, Anum, aunty Mahfuzah, da wasu gungun mutane sun ƙare wannan dare daga farkonshi har ƙarshensa wajen miƙama UBANGIJI godiyarsu da kukansu, a tsakkiyarsa ALLAH ya bama bilkisu da Umm-Anum damar farkawa suma sukabi ayarin masu bautar ALLAH da raya wannan dare da ƙiyamul laili.
          A ɓangaren Alhaji kokino kuwa da duk mai alaƙa da wannan tunkuya wannan dare ya kasance daren tashin hankali da ruɗani a garesu. Babban tashin hankalinma shine kowa ya gaza fasalta kamannin bilkisu a gidan balle ai maganar samun hotonta, sannan baba maigadi tunda suke dashi basu taɓa tambayarsa garinsu ba, abinda kawai suka sani daga ƙauye yake, wane ƙauye? Shine basu saniba, bayan kuma ya kai kusan shekara ashirin yana musu aiki, tsabar bashi bane a gabansu ba basu taɓa bibiyar komai nashi ba a rayuwa, dan shi Alhaji kokino wani irin mutum ne da abinda ke damuwarsa shine kawai mai muhimmanci  a garesa. Bai taɓa takaicin wannan baƙar halayyar tasaba sai a yau ɗin nan.
            Tun a daren aka baza jami'an tsaro neman baba maigadi, sai dai shiru kakeji, sudai sunce suna kan aikinsu. Daga can kuma tushen tsafinsu sam an kasa ganin inda su Bilkisu suke, abinda kawai suka gani shine an fasa tukunya.
      A daren duk wani mai alaƙa da wannan ƙungiya aka sanar masa gobe akwai mitin, duk inda kake dolene ka dawo dan gagarumin mitin ne mai muhimmancin gaske.

SAUDIA

          Tunda aka idar da sallar asubahi a ƙasar Abbu ya zaunar da Umm-Anum ya zayyane mata komai da ya sani game da ita dan su gwada suga ko hankalinta ya dawo jikinta sosai. Aiko a take ta shiga rairai masa kuka da roƙon Abbu akan ya kaita wajen ƴan uwanta, tanason tagasu, ita ba zata sake kwana a saudia ba sai ta dangana da ƙasar haihuwarta.
     Da ƙyar suka lallasheta shi da Su Abu-Siddiq da su Anuwar. saboda gudun zuwan irin wannan ranar a bazata yasa Abbu bai taɓa sakaci da duk wani abinda zai taimakesa akan fita ƙasar ba idan Umm-Anum ta dawo hayyacinta, dan haka ya bata haƙuri akan ta kwantar da hankalinta zasu tafi a yau ɗin nan komai dare insha ALLAH.
           Gari na ƙarasa wayewa suka fita shi da ɗan uwansa Abu-Siddiq, abinka da manyan mutane cikin amincin ALLAH sai gashi cikin awa uku sun kammala dukkan wani abinda ya dace, jirginsu zai tashi ƙarfe sha ɗaya na agogon ƙasar. cike da farin ciki suka kirasu a waya tunkan su ƙarasa akan su fara shirin tafiya. Ai Umm-Anum da Anum sunfi kowa ɗoki, Anuwar kam ai ba'a cewa komai, kayansa ya loda na fitar hankali, a cewarsa saiya more ƙasarsa da ƙyau, ya kuma more ƴan uwansa da bai sani ba. Sudai dariya sukaita masa kawai.

__________________________________

         Da safe na tashi Alhmdllh, dan babu ciwon kan sam sai rashin jin ƙwarin jiki, ganin gidan yay ƙura naɗan tashi na fara gyarawa, amma yana shigowa sai ya hanani yace na barsa anjima Nabeelah zatazo ta gyara, yanzu muɗan sake kwanciya zuwa goma saimu fita zuwa gidan Dad zan ɗakko ɗayan wuri ɗin nan da nace na taɓa tsinta.
    Haka kawai sai na samu kaina da faɗuwar gaba mai tsananin gaske, dan kuzarin dana tashi da shi ya ida kakkaɓewa gaba ɗaya. Barcin da yaso muyi sai ya ƙauracema idanuna, harma shi yayi nasa ni idona biyu inata saƙawa da kwancewa, ga mafarkin danayi a daren jiya kafin na tashi naga yana salla nima nayo alwala sai dawomin yake a cikin rai. Da tunane-tunane na cinye nawa lokacin barcin, harma goman tayi ya farka. Kallon tuhuma yayta bina da shi akan banyi barciba, na dai fuske abina bance da shi komaiba. Tare mukai wanka, hakama shiri da taimakonsa na shirya dan duk bani da wani ƙarfin zuciya balle akai gana jiki kansa. Muna gama kimtsawa mun fito sai ga Nabeelah da breakfast.
         Zama mukai mukaci, koma nace yaymin ɗura, dan ko lauma ɗaya ban iya kaiwa bakina ba, sai da taimakonsa, daga ƙarshema sai na ringayin yunƙurin amai, dole ya ƙyaleni da iya abinda naɗanci muka fita muka bar Nabeelah a gidan akan bazamu jimaba zamu dawo, dan dama ai yau juma'a ce..
Chapter 135 · 0% Book details