← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 168

Sashe 41

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kanta taji kukan ya isheta ta share hawayenta ta tashi ɗauke da rigarsa a hannu ta nufesa. A tsorace zuciyarta take, amma wani sashe na bata ƙwarin gwiwa akan abinda take shirin yi. Gaban Jawaad taje ta durƙusa kanta a ƙasa. Jawaad da yaƙi ɗagowa ya kalleta dukda yanajin motsinta ya cigaba da aikinsa.
         Karan farko a rayuwar Bilkisu data shirya ambaton sunan Jay a harshenta harma da ƙarfin halin furtawa a gabansa, sai dai tayi imanin bazata iya ambaton sunansa da kallonsaba a yau, dan haka ta duƙar da kanta tana durƙushe akan gwiwoyinta, rigarsa riƙe a hannunta ajiye akan cinya, tace, “Yah Jawaad!.…….”
     Cak Jay dake rubutu a wasu takardu ya tsaya tamkar wanda aka tsaida da remote, shi bai kalleta ba, kuma bai cigaba da abinda yakeba, saima lumshe idanunsa da yay yana sauraren sarawar da kansa ke masa da harbawar jijiyoyinsa harma da gudun jininsa daya tsinke a lokaci ɗaya. Bilkisu daba kallonsa takeba ta cigaba da faɗin “Dan girman ALLAH Yah Jawaad kayi haƙuri karka wofantar da magiyar Dadynmu, wlhy ni shaidace aunty Shahudah na matuƙar sonka, duk da bansan ainahin matsalarkuba inada yaƙinin zaka iya amfani da son da take maka ka canjata, matsalar da duk kake ganinta da ita ƙirƙirarriyar matsalace dakeda tushe a gareta tun tana tsumman haihuwa, ba laifinta bane ita kaɗai haka ta tashi taga kanta itama, bata isa banbance baƙi ko fariba a buƙatar jin zafi saboda an nuna mata hakan shine dai-dai da rayuwarta kuma nasararta, Mahaifina yasha faɗamin, {Bilkisu, aduk lokacin da zama ya haɗaki da mutane ki fara nutsuwa ki fuskanci halayyarsu da tsarin rayuwar da suka rayu, dan babu wata zuciya dake gogayya da ƴar uwarta akan hallayya iri ɗaya, lokacin da k tarbiyyarki ta baki dai-dai a wajen wani shi kuskurene, abinda yake kuskure a yaƙininki a wajen wani dai-dai ne, idan har kika kasance cikin mutane masu fahimtar ilimin duniya ina mai tabbatar miki zaki zama nasararki sama data kowa koda ace ke kaɗai kike kallon kanki a wannan nasarar,  daga lokacinda ilimin sanin hallayar ɗan adam ya dawo tafin hannunki inada yaƙinin zaki gyara ɓarna da yawa, domin zakibi mutum da halinsa ki ɗorashi akan hanyarki mai nagarta batare dashi yasan ya afkaba ma, munzo zamanin da halin ɗan adam dashi ake cinsa da yaƙi bada takobiba, zauna dame ƙinki da zuciya ɗaya, ƙyautata masa kuma da yaƙinin neman sakamo wajen mai badawa ba ga shiba, koda shi a kullum zai kasance mai bibiyar bayanki da sharri, karki zama mai damuwa da zama gwana a duniya, dan wani lokacin nasarar duniya faɗuwace gamai ita, koda idanun duniya na kallonsa a saman kowa, mai kuma sa'a fiye da kowa}, Yah Jawaad ba soyayyarka kawai aunty Shahudah ke buƙataba, a yanzu tafi buƙatar ka jingina da soyayyar tata ka ɗorata a hanyar tsira domin kaikaɗaine zata iya saurara, saboda girmamaka a matsayin gwaninta, na yarda dakai ta kowanne fanni koda banida ilimin sanin ɓoyayyun halayenka, ina sake roƙonka a matsayin Yaya ba shugabana a wajen aikiba, dan ALLAH ka ceto rayukan bayin da zukatansu suke a rufe ruf akan sanin gaskiya da makomar bin hanyarta, yahudanci da nasaranci duhune, wannan duhun kuma shike mamaye da jama'ar gidanmu, sai dai hasken ruɗani da gushewar banbance mai tsafta ya hana ijiyarsu ganin kowanne tsani sai wanda suka hau, kullum fatana ALLAH ya kawo musu drivern dazai fidda rayukansu a kwale-kwale saboda ni nayi ƙanƙanta ƙarancin matsayin yin wannan jagorancin, kaiko inada yaƙinin zaka iya, domin son da sukema aunty Shahudah gyaruwarta tamkar gyaruwar kaso mafi yawane daga ahalin gidan, ciki kuwa harda Dad da tuni ya fahimci gaskiya, sai dai ƙarfin riƙonta a garesa da tafi ya hanashi nunawa ko a fuska, ya gwammaci ya haɗiyeta a rai yacigaba da rainon ƴaƴansa tamkar ƴaƴan agwagi da basa bin uwa sai dai ita ta bisu” na ɗago kai a karo na farko tunda na fara maganar na kallesa, sai dai a mamakinna shi ba ni yake kalloba, gashi yayi kicin-kicin da fuska irin yanda ban taɓa ganiba a tun sanina dashi, na raya a raina saitna dire abinda na fara, dan haka nace, “Dan ALLAH Yaya Jawaad ka yarda a maida aurenku da aunty Shahudah a karo na b....i...y...u.”
         A yanda y

a juyo ya sauke rikitattun idanunsa a kainane yay masifar hargitsani na ƙarasa kalmar ƙarshe da ɗai-ɗai.............✍

Tab wlhy badaniba nayi nan, idan ya huce na dawo na ƙarasa muku yanda aka ƙare🚴🏼🚴🏼🚴🏼🚴🏼🚴🏼kuma bily addu'ar fitowa lafiya itama, dan inaga ba'a taɓa karyata ba😂🤣.

Barkanmu da dawowa, inafatan kowa yayi weekend cikin ƙoshin lafiya?.😍😍
[12/31/2020, 9:31 PM] Abubakar Saleh Kurami: Ƙwai Cikin Ƙaya
.
BOOK TWO
.
Bilyn Abdull 📚:
Page 20

.................“Ya salam” Jawaad ya faɗa tare da ranƙwafawa ya ɗaga frame ɗin da hoton ke ciki, a bisa tsautsayi ya ɗaura hannunsa kan glass ɗin da ya maƙale kaɗan bai ida fitaba, yay tsini siriri, “ouch!!” ya faɗa yana yarfe hannunsa saboda shigar zafin bazata. Alhaji baba ya taso da hanzari garesa, hannun da yake yarfewar ya kama, abinka da jiki babu wahala tuni jini sai rige-rigen fita yake, abin mamaki har yana neman wuce girman ciwon da yajin. Daga Alhaji baba har Jawaad sai fitar jinin da yawa ta basu mamaki, dan sosai yake ɗiga a ƙasan tiles ɗin tamkar wanda yay wani uban yanka, Jawaad yay ƙoƙarin ajiye hoton saman drawer batare da ya kallesa ba sai kawai ya sake ɗora ƙafarsa akan glasess ɗin dake zube ƙasa. Da sauri ya ɗaga ƙafar tare da sake damƙe hoton a hannunsa yaja da baya yana faɗin,  “Yah ALLAH”. 
        Alhaji baba yace, “Subahanallahi sake takawa kayi?, to kaga zauna ina zuwa”. Zama Jawaad yayi ya ɗora fasashshen frime ɗin da ya rage katako da katin hoton kawai a cinyarsa yana tarbe ɗigar jinin hannunsa da ɗayan hannun wanda tuni jinin ya ɗiɗɗiga a hoton ma. Sai dai hankalinsa bai kaiba, har Alhaji baba ya dawo ɗauke da ruwan ɗumi a roba mai ɗan faɗi da guntun towel, a hannun kujerar ya ɗora ya kama hannun Jawaad ya saka a robar tare da jiƙo towel ɗin da ruwan zafi ya goge masa hannun tas dukda dai jinin yaƙi tsayawa har yanzu yana ɗiga, kamar yanda sukai hasashen ɗan yankan bawani mai yawa baneba,  tissue ya warwaro ya ɗora masa dai-dai yankan yana mai tsokanarsa da cewar, “Lallai cin kayan daɗinka yay yawa na wajena, kaga ɗan yanka kaɗan amma jini yayi rabin botiki”. Babu shiri Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya, “Oh ALLAH, tsohon nan kana hawa kaina da yawa wlhy, idan yakai rabin botiki ai saidai a ɗiba naka a ƙaramin kenan”. Dariyar alhaji baba yake shima, ya durƙusa tare da kamo ƙafar Jawaad ɗin itama dake jinjin ya saka a robar, kwalbar data sokesa anan tana ciki, hakan yasa Alhaji baba shammatarsa ya cirota, “Ouch!!” Jawaad ya faɗa yana rintse ido dan yaji zafi, ciwon ƙafar yanada ɗan girma, Alhaji baba ya ɗaure masa dan su samu jinin ya tsaya.
         Batool ce ta shigo da sallama ɗauke da abincin kakan nasu. A tsorace take kallon jinin da ƙafar Jawaad ɗin, “Ɗan uwa garin yaya haka?”. Fuska yaɗan yamutsa yana kallonta, yace, “Tsautsayi mana”. Sannu ta shiga jero masa, ta ajiye basket ɗin ta ƙaraso ta amshi tsintsiyar hannun Alhaji baba danta share kwalban kamar yanda taga yana niyyaryi. Jawaad ya sake kai hannu zai ɗauke hoton daga cinyarsa dan yanason ya tashi yaje yay wanka, sai idanunsa suka sauka akan waɗanda ke jikin hoton, dukda jininsa dukya ɗan ɗiɗɗiga a jiki, hakan bai hanashi ganin fuskar mahaifiyarsaba ras a jiki, tayi ƙyau sosai tana murmushinta mai birgewa, ya maida idonsa akan ta kusa da ita, autarsuce da suke kira aunty Mammah, itama ALLAH yay mata rasuwa shekaru masu tazara bayan ɓatan mahaifiyarsa, haka kawai ya samu kansa da tsura musu ido harna tsahon lokaci, sai da Batool ta ɗauke hoton daga hannunsane ya dawo hayyacinsa. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke yana miƙewa. Batool dake kallon hoton tai murmushi da share guntayen hawayen da suka cika mata ido saboda tuno da Gwaggonnin nata guda biyu da suka rasa a ƙaddarar mutuwa da ƙaddarar taɓin hankali.
            Koda Jawaad yay wanka ya kimtsa ya fito bai zauna cin abincin da Batool ta kawoba, sai ya ɗauki hoton daya fasa zai tafi dashi akan zai sabunta masa glass, babu yanda Alhaji baba baiyiba amma yaƙi ya ajiye. Cikin tsokana Batool tace, “ALLAH yasa ba sace maka zaiyiba Alhaji baba”. Harararta Jawaad yay ya fice, batare da ya jira amsar da Alhaji baban zaiba Batool ba.
     Maimakon ya nufi gida kamar yanda yay niyya sai kawai ya wuce office, ta waya ya kira Gimba yasanar masa shi yana office anjima yazo ya samesa zasu fita. Cike da girmamawa gimban ya amsa masa sannan suka ajiye wayar.
      Koda Jawaad ya shiga station kai tsaye office ɗin Jabeer ya nufa, shima da alama bai jima da isowarba, ya ɗago yana kallon Jawaad daya shigo office ɗin da sallama, murmushi yay masa, shikuma Jay ya hararesa yana ƙarasowa ya z
Chapter 41 · 0% Book details