← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 168

Sashe 86

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

            Yau ta kasance ranar da zan koma ƙasata ta haihuwa tare da tarin alkairan Umm-Anum da mijinta da Aunty Mahfuzah, sai su Anum da nakejin ƙololuwar farin cikin tafiya tare da su, gefe guda kuma na zuciyata najin ɗacin rabuwa da Umm-Anum tare da matsananciyar kewa. Munfi awa uku zaune da ita tana sake tisamin abubuwa masu dama, daga ƙarshe ta roƙeni akan karna manta da ita, zata kuma ringa kirana akai-akai, idan kuma nasamu lokaci na daure muzo gareta wataran tare da mijina, haka kawai takeji a ranta tanason ganin mijin ƴarta. Murmushi kawai na iyayi ina share hawayena kaina a risine, ta rungumeni a jikinta tana jeromin addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya a gidan aurena. Da ƙyar ta barni na fito, tana kuka nima inayi tamkar zan shiɗe, da ƙyar Aunty Mahfuzah taja hannuna ita da Anum.
       Har jirginmu ya ɗaga ban daina kukan kewar Umm-Anum ba, ina ƙaunar matarnan matuƙa a cikin jinina da tsokar zuciya harma da ruhi.
      Kasancewar tafiyar yamma mukayo dukda ba time ɗinmu ɗaya da nanba munyi saukar dare ne, inda mukaci karo dasu Amaturrahman ƴan tarba, sosai muke murnar ganin juna, sai santi suke wai na canja matuƙa, sunata zubamin shaƙiyanci nadaiƙi kulasu, dan bana cikin mood ɗin farin ciki sam.
     Koda muka isa masarauta Ummu ma rungumeni tayi, sai taɓani take tana jerama Umm-Anum addu'oi na musamman, ga daɗin da taji na barin su Anuwar da akai suka biyomu. A ƙasan raina inata mamakin ganin yanda suketa shirye-shiryen bikin tamkar zasu aurar da ƴarsu ne ta cikinsu ko ƴar uwa ta jini, kai waɗanan mutane sun cancanci zama shugabbani, domin duk mai fuskantar al'umma da maida al'amarinsu nasa to lallai shine shugaban da yafi cancantar zama shugaba.
         Ɗaki guda aka waremin dan Ummu tace bazan zauna ɗakinsu Amaturrahman ba wannan karon, akwaima sauran kayan gyara da Umm-Anum ta bayar a ƙarasa min a kwanaki biyun da suka rage mana. Babu wanda yaymin maganar Boss nima kuma bamma kowa ba, da yake darene bayan anɗan gaggaisa duk muka kwanta.

WASHE GARI.

         A safiyar yau nakejin wai za'a kai lefena gidan Dad ne, haka kawai naji gabana ya faɗi, amma sai na danne zuciyata na cigaba da addu'oi, har yanzu Yah Qaseem na ƙasan raina, inason nasan halin da ya ke ciki shi da Dad fiye da kowa a gidanmu, sai dai hakan ta gagara dan boss ya toshe ko ina da ina da zan iya jinsu. Su Amaturrahman sunata shirin tafiya can gidan domin amsar lefen suma, sai a yau naga sauran manyan ƴaƴan Ummu ƴan uwan tagwaicin Amaturrahman. Abdul-Raheem da Abdur-rahman, sai Ameen ɗan uwan tagwaicin Meenal, sai Uncles ɗinsu huɗu, Sauban da matarsa ƙyaƙyƙyawa mai kirki da yaransu huɗu masha ALLAH, sai Aryaan shima da matarsa da yara biyu, Aiyaan ma matarsa da yarinyarsu ɗaya sai ciki ƙarami da matarsa keda shi, sai Khalil shima da tasa matar da yara biyu, dukansu suma a jiya suka iso daga India. Gida ya cika yanda akeso tamkar bikine daya shafesu na jini, washe gari sai ga wadda naji suna kira Aunty Samha itama da nata ƴaƴan, sai kuma babbar mace suna kiranta Aunty Mimi. Wlhy bansan sanda hawaye suka faramin gudu a kumatuba, duk wani kewar ahali sun toshemin ita ta ko ina, sun mayemin gurbin dangin da suka nisanceni.
       A wajen Amaturrahman nakejin wai Boss yazo masarauta wajen Ummu yau da safe, bai nemi inda nakeba har ya wuce, banji komai a rainaba game da hakan, sai daga baya suke bani labarin Ummu ce tace an daina ganina har da shi kansa bazai ganniba. Ni saida abinma yaso bani dariya amma na kanne.

_______________

          A gidan Dad kam shirye-shiryen karɓar lefe suke, duk da dai ran Momy a ɓace yake matuƙa tana dai ƙoƙarin dannewane, shi dai Dad baka gane yanayinsa, dan yamafi maida hankali ga lallashin ƴar lelensa da suka cikama zuciya

da alƙawarin komawarta gidan Jay nan bada jimawaba.
     Kusan sha biyun rana su Amaturrahman suka iso gidansu Hudah, Hudah dai bata fitoba zamanta tai cikin ɗakinta, Aamilah kuma an fito ayi rainin wayo saita iske waɗanan sunci uwarta aduk iskancin da take taƙamar ta tara kota iya. Dole fa ta nutsu waje guda ta kama kanta, harta je ta ƙwanƙwasama Shahudah dake ɗaki gulma da cewar lallai Bily ta shahara a asirin nata har ƴan gidan sarki taimawa. Cikin takaici Shahudah tace, “Tsinanniya jikar matsafa, ai nayi alƙawarin randa na koma gidan Bb wlhy bazata kwana a gidanba, shi kansa saina sakashi yin nadama wlhy, kuma a banza zata shiga ta fito Hajiya (mama Atika) tamin alƙawarin ko hannunta bazai riƙeba dan Uban da ya haifeta”. Dariya Aamilah ta sanya da sake tunzurata akan hakan da zatai shine dai-dai, kuma taji daɗin matakin da mama Atika tace zata ɗauka akan kar Bilkisu ta raɓu Jawaad, (dan sufa har iyanzu tunaninsu nakan asiri Bilkisu taima Jay bawai sonta yakeba😂). “Mtsooww kamar kin manta da aikin matsafa kenan” cewar Shahudah cike da takaici. Haka dai sukaita aikin zagin Bilkisu da Alhaji Babba harda su Ummah basu tsiraba, kai gidan sarki ma saida suka samu rabonsu😂.

       Oho su bama susan da zaman wata Hudah ba a duniya balle a cikin gidan, sun ɓararraje abinsu sunata harkokinsu tamkar gidansu (😂Wani aiki saisu Samha) hankalinsu kwancefa yake a gidan Dad dukda sunga cika da batsewar da Momy keyi basu nuna ta damesuba.
     Ƙarfe biyu da wasu mintuna na rana matan Uncles ɗin Jawaad dasu Ummah suka iso da lefen Bilkisu. Kayane gwargwadon iko na gani na faɗa babu fariyya a ciki balle nuna anfi kowa. Sai dai fa tsarin kayan da nagartarsu dolene ta girgiza zukatan mahassada da masu ganin wadda akai dominta bata cancancesu ba. Inna zainabu sai haɗiyar zuciya akeyi, hatta da Lawisa da ayanzun basa faɗa da bilkisun kuma itama mijinta Alhmdllh sun sami sauyi saida taji ɗaci a ranta, hakama sauran dangin kowa dai ta ciki na ciki, su kansu matan Uncles ɗin Jawaad da suka kawo kayan kowa dai sai murmushin saman fuska tunda suma sai yaune suke ganin kayan tunda su Ummah ne suka haɗa abinsu. To kowa dai ya danne an gama komai lafiya, an kuma bar kayan anan sai Dad ya gani sai a kaisu masarauta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suma su Gimbiya su gani.
        Tukuyci mai tsoka ƴan masarauta suka saukema su Ummah, wanda ya girgiza kowa hatta momy da take ganin wanda Dad ya bada a bayar yayi yawa da.

      Aikam tunda su Safah suka koma masarauta babu abinda suke sai labarin lefe, suka addabama Bilkisu da tsokana musamman su Amaturrahman da matansu Aryaan da suke biye musu suma dayake mashiriritan ne. Sai da gimbiya ta fito da kanta ta korasu daga kan Bilkisu sannan suka sama mata lafiya.

_____________

                 Gayya taban mamaki su Jabeer sukayo a wannan biki, al'amarin har ba'a cewa komai, tun a yau baƙin nesa kuwa suka fara sauka, irin su Abbati ma duk yau suka kawo matansu gidan Ummah babba, su kuma suka yada zango a masaukin da su Hafiz suka tanada musu.
        Ango kuwa yau alhamis yana zuwa office Sir Ahmad ya korosa akan ya tafi sun bashi hutu, karya ƙara ganin ƙafarsa sai nan da sati biyu ciff, shidai murmushi kawai yayi baice komaiba. Ƴan station ɗinsu ma dai zuwa yanzu sunsan boss ya auri Bilkisu, masu gulmar dama soyayya yake da ita sai bakuna suka buɗe aka samu nayi, yayinda masu goyama Rose baya suketa angizata da maganganun ɓatanci ga Bilkisu da Jay ɗin kansa, masoyansu na ƙwarai kuwa murna suke tayasu da ganin sun dace da juna.

MASARAUTA

           Tunda garin ALLAH ya waye an tashine cikin shirye-shiryen kamu da aka haɗashi da Hausa fulani day baki ɗaya, su Ummie, Nazifa, Zuhrah, Rebecca, Amina, Nabeelah, duk suna can suma tare dasu Amaturrahman, abin birgewa kuma duk ƙawayensu na Boarding skull sai da su Ummie suka gayyatosu suma duk sunata isowa masarauta a safiyar yau, hakan saiya saka Bilkisu hawaye da tuno iyayenta, inama da ransu wannan rana tazo mata, inama suna jingine da ita har zuwa yau ɗinta, ina firdausin ta, ƙawar amana ko tace ƴar uwa rabin jiki, kullum addu'arta ALLAH ya

sadata da Firdausi da iyayenta kafin tabar duniya.
Chapter 86 · 0% Book details