← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 168

Sashe 142

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

          Zuwa goma da rabi duk mun hallara gaban abinci, bayan gaishe-gaishe da tambayar lafiyar juna mukai zaman karyawa, kowa nacin abinci cikin salama bandani da naketa tsakurarsa, badan rashin daɗiba kuma, haka kawai dai nakeji bana sonci kuma yunwa nakeji.
       Jay ya lura bily batacin abincin sam, sai dai kunyar iyayensa ta hanashi cewa komai. Ummah babba ce ta lura da hakan, saita kira Bilkisu. Tashi nai na nufeta dan nazata wani abun zata sakani, sai dai ina zuwa ta jani ta zaunar kusa da ita, da kanta ta shiga ɗuramin abincin duk da nace mata na ƙoshine, ina kallon sanda boss ya sauke ajiyar zuciya. Daurewa kawai nake ina amsar abincin.
          Boss ne ya fara miƙewa alamar ya ƙoshi, yaɗan kalli iyayen nasa yana faɗin, “Bara naje na watsa ruwa kafin time ya ƙure, jirgin su Abbu ƙarfe sha biyu zai sauka”. Cikin kulawa Ummah babba da ƙarama suka amsa masa.
      Shigewarsa babu jimawa muma duk muka kammala, da taimakon su Anum na gyara wajen, gudun kar kwanikan su bushe sai mukai zaman wankesu, muna wanke-wanken ina tunanin abinda ya kamata na dafa mana da rana, dan koma daga ina ake kawo wannan abincin bana buƙatar a cigaba da kawosa, ya kamata nima in-lows ɗina suci girkina ai....

★★★

         Jay na fitowa daga wanka ya samu wayarsa na haske kasancewar a silent take, matsawa yay gaban mirror ya shiga shafa mai batare da ya duba mai kiranba ma, bayan ya kammala yana gaban Wadrobe zai ɗauka kayan d

a zai saka ya kuma hangar wayar tana haske, guntun tsaki yaja, ya ɗauka kayan da yake bukata ya fara sakawa, sai da ya shirya tsaf sannan ya nufi wayar yana idasa saka maɓallan rigarsa. Gabansa ne ya ɗan faɗi ganin Batool ce ta jera masa har missed calls kusan talatin, sai kuma number sojan da sukanyi magana da baba ƙaura idan hakan ta taso. tabbas wannan kiran bana lafiya bane, dan kaf cikin ƴan uwansa babu wanda ya kai Batool iya zama da shi da halinsa, inhar tai masa kira ɗaya tai na biyu taga bai ɗaukaba bazata sake kiransaba sai idan shine ya kirata. Yana ƙoƙarin kiranta sai gashi ta sake kira, ɗagawa yay da sauri....
         Daga can Batool ta sake fashewa da kuka jin an ɗaga, a cikin tsananin ruɗani tace, “Yayanmu akwai matsala, wasu mutane sunzo har gida sun tafi da Alhaji Babba da baƙon mutumin nan”.
         Wani irin yankewa ƙirjin Jawaad yay ya faɗi, furicin Batool ya jisane cikin kunnensa tamkar saukar guduma, cikin rawar baki yace, “Su su.. Su wanene?”. “Ban sansuba Yayanmu, ina ɗakin Alhaji babba ina gyarawa suka shigo. fuskokinsu duk a rufe suke da facemask, nima nasan da sun ganni bazasu barniba, tun shigowarsu nake kiran wayarka amma baka ɗaukaba, ina tsoron na kira su Ummah su ruɗar da kansu shiyyasa ban kiraba.....” Bai bata amsaba ya katse kiran, ƙirjinsa na wani irin lugude tamkar ana gasar dakan fura a kansa. Da sauri ya fice daga ɗakin, harya nufi sashen Bilkisu sai kuma ya jiyo dariyarsu a kitchen ita dasu Nabeelah, can ya juya ya nufa......
          Muna tsaka da yima Anum dariya boss ya faɗo kitchen ɗin, yanayinsa kawai ya sakani faɗuwar gaba, Anum da Nabeelah kam duk ɗauke numfashi sukai dan tsoro, baice komaiba yaja hannuna muka fice, har munje ƙofa ya juna yana watsama Nabeelah kallon gargaɗi, “Kucigaba da aikinku, idan kuma ƙafar wani ta fita a kitchen ɗin nan saina ɓallata”. Kai kawai suka jinjina masa, ya ja hannuna muka ƙarasa ficewa zuwa bedroom ɗinsa.
       “Boss lafiya kuwa?”. “Babu lafiya Miemaa, yanzu Batool ta kirani........ Akwai matsala ace su Ummuna susan wannan maganar, musamman ma ita da nasan yanzu babu wanda ta ƙagu ta gani kamarsa, dan haka kiyi shiru da bakinki yanzu zan tafi can, kosun tambaya kice nafita amma zan dawo yanzun k.......”. Da sauri na katsesa da faɗin, “Boss tare zamu tafi, nima bazan zaunaba”. “Bazai yuwuba Miemaa, idan muka fita mu duka zasu iya tunanin wani abu”. “Dan ALLAH kayi haƙuri mutafi tare, koba komai nima zanyi wani amfanin ai, zamana anan zaisa na kasa jurewa na tona asirin komai”. “Miemaa!....” “Please boss”. Nai azamar katsesa. Bakinsa ya cika da isaka ya furzar da ƙarfi yana ɗaga wayarsa dake haske. Ban saurari amsarsa ba nashiga ƙoƙarin canja kayana.

        Ta kitchen muka fita, bayan boss ya jama Nabeelah dogon gargaɗi akan ta kama bakinta wlhy, idan har sukace mun fita sai yay gutsi-gutsi da ƙasusuwanta yanda babu mai iya shaida itace harma Anum ɗin kanta. Daga haka muka fice, Sadiq baizoba, saboda weekend ce, dan haka boss da kansa zaiyi driving ɗin.
         Mahaukacin gudu ya ke zubawa tamkar shi kaɗaine da titin, to dama yaya lafiyar giwa balle....., dama can shi ɗin ɗan babu sauƙine wajen gudu da mota, balle yanzu data zamto na ƙare numfashi. Ko gezau banyi da gudun nasaba yau, gani nakema tamkar baya gudun, sai faman kaɗa yatsun hannuna nake jikinna na wani irin tsuma. Yayinda boss kuma yana tuƙi yana waya da su Oga Hafiz.
    Cikin mintuna ƙalilan muka iso gidan, mun iske tawagar su Jabeer a gidan harma da ƴan sandan zahiri, sai wasu daga cikin ƴan anguwa da abin ya faru akan idanunsu su Hafiz nata musu tambayoyi.
      Aunty Batool ta iso garemu da gudu tana kuka, riƙo hannunta boss yayi idanunsa na sake kaɗawa suna sake komawa jajur fiye da yanda muka fito gida. Bayanin duk yanda yanda al'amarin ya faru ta shiga yimasa kamar yanda tayima su Sir Ahmad ma. Kasa cewa komai yay, sai jikinsa dake wani irin rawar bala'i, ƙwanjinsa da jijiyoyin kansa na sake buɗewa, yanda ƙirjinsa ke sama da ƙasa kawai zai tabbatar maka zuciyarsa na gudu maiban tsoro dake neman fin ƙarfin gangangar jikin nasa. ya saki hannunta ya nufi inda su oga A

liyu suke. Matsawa nai na rungumeta muna hawayen tare, sai dai ni saɓanin ita ina ƙarfafa zuciyata yau ina lallashinta, sai da naga ta tsagaita da kukan sannan na ɗagota na share mata hawayen. “Ki kwantar da hankalinki aunty Batool, insha ALLAHU zasu dawo, kosu wanene ALLAH bazai basu dama akan ƙudirinsu ba”. “ALLAH yasa haka mami” ta faɗa wasu hawayen na sake jiraro mata. kiran da oga Jabeer yaymin ne yasa na taimaka mata ta zauna a cikin motar.

        Tun a yanda Jawaad ɗin ya taka birki sanda suka iso gidan su Sir Ahmad sukasan ransa a matuƙar ɓace yake fiyema da yanda sukai hasashen ganinsa. ganin Batool ta nufesa sai duk suka dakata daga yunƙurin zuwa inda yaken, bayan yabar wajen ya nufesu ne, Sir Ahmad yay saurin tararsa cikin zafin nama yana riƙe hannunsa “Jay! Ka kwantar da hankalinka, insha ALLAHU zamu gano inda suke, koma su wanene suka aikata hakan basuyi nisa damuba a halin yanzu tabbas, yanzu haka har su Jabeer sun fara ƙoƙarin gano inda suke. Ka nutsu banason ka fusata kanka da yawa, domin nutsuwarka ce abar buƙatarmu fiye da komai a yanzu. shin akwai wani da kake zargi ne?”.
          Jawaad dake tsaye kawai yana kallon yanda su Aliyu da sauran ƴan sandan keta kai kawo akan al'amarin ya lumshe idanunsa yana busar da zazzafan numfashi, “Sir! Kowama zan iya zarga a halin yanzun, sai dai hakan bazai saka na kasa fidda ɗaya a cikin dubu ba”. “Nasani gwarzona”. Sir Ahmad ya faɗa yana ɗan bubbuga kafaɗar Jay ɗin cike dajin ƙarin alfahari da ƙwazon yaron.
          Jabeer ne ya ƙaraso wajen riƙe da tab.. A hannu, yay salute ɗin Sir Ahmad sannan ya kalli Jay dake kallonsa shima. “Boss ƴan iskan mutanen nan basu bar wani alama ko kaɗan da za'a iya bibiyarsu ba, bayanan dake hannunmu ma a yanzu haka ko motar da sukazo a cikinta babu Number ma, abinda bayanan mutanen anguwa suke faɗa mana kawai motar baƙa ce, suma mutanen kuma baƙaƙen kayane a jikinsu, fuskokinsu a rufe”. Shiru yay yana kallon Jabeer cike da nazarin maganganunsa, kafin kuma ya kallesa yana ɗan cije lip ɗinsa na ƙasa, “Dama bana tunanin zasu bar wata alama ta zahiri, sai dai dolene za'a samu ta baɗini Jabeer. Zamanmu anan gidan baida wani amfani, inaga mu wuce office kawai”.
      Jabeer yace,  “Okay nima nayi wannan tunanin, dama isowarka muke jira muji ta bakinka, dan yanzu haka dai Number shi Alhaji Babba muketa ƙoƙarin bibiya saboda Batool tace tana zaton da ita ya tafi a jikinsa batare da suma maharan sun sani ba. a yanzu haka dai wayar na nuna tana titin gambari gab da babban titin ƴan robobi na gabashiya. Jami'anmu suma suna gab da isa wajen harda Aliyu”. Amsar Tab ɗin Jay yayi daga hannun Jabeer da sauri....
       Hakan yay dai-dai da isowar Bilkisu da wani tunani yazo mata a zuciya inda suke. Sai da tai Salute ɗin Sir Ahmad itama sannan taɗan matsa kusa da Jay da hankalinsa kega Tab... ɗin da ya amsa a hannun Jabeer, amma yasan da zuwanta, dan ƙamshin turarenta ma ya ishesa shaidar tana wajen. “Sir anya kuwa wannan aiken ba daga gidancan bane?”. Da sauri Jay ya ɗago yana kallonta, “Wanne a ciki?” ya faɗa cike da ƙaguwa. “Inda na dawo daga farauta shekaran jiya”. Kafeta yay da ido dan maganarta na tafiya bisa ƙamshin gaskiya. Ta ƙara risinar da kanta cikin girmamawa a garesu, cigaba tai da faɗin, “Bazai yuwu ace dama ya barmu ba, dolene zai bibiyemu kodan maigadinsa, sai dai bamu da tabbas, hasashene kawai nayi Sir”. Jawaad yay wani ɗan murmushi yana maida duka hannayensa biyu ya goya a bayansa, taku ɗaya biyu yay sai kuma ya sake juyowa, hannunsa ɗaya ya sauke daga bayan ya tura cikin aljihu, ɗayan dake riƙe da tab... Kuma ya ɗagosa yana goga tab... Ɗin akan hancinsa. Daga Jabeer har Sir Ahmad da bilyn duk kallonsa sukeyi. Wani murmushin ya sakeyi da tsayawa cak, bily ya nuna da tab... ɗin hannunsa yana faɗin, “Maganarki akwai ƙamshin gaskiya, dolene a cikin biyu a samu ɗaya, idan kuma nai wani nazari zan iya ɗaurasu a mizani guda ya zama aikin haɗaka ne”. Ya ƙare maganar yana maida dubansa ga sir Ahmad da ke binsu da kallo kawai. Kafin yace wani abu Hafiz ma ya iso riƙe da waya alamar magana ya gamayi. “Mutanen nanfa inaga sun farga da
Chapter 142 · 0% Book details