← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 168

Sashe 141

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Cikin mintuna ƙalilan sai ga Dad a hargitse kamar zai tashi sama, yanda yake buga ƙofar kawai kasan babu lafiya, Aamilah ta buɗe masa tana matsawa ta bashi hanya, da sauri ya shigo. A gaban Shahudah ya durƙushe tare da maido kanta jikinsa idanunsa na kaɗawa lokaci guda dan ɓacin rai. “Shine ya kawota?”. Yay tambayar yana kallon Mom. “Nima ban saniba Dadynsu, shigowarta kawai muka gani ita kaɗai. Leɓe Dad ya taune da ƙarfi, ya kalli Salman dake tsaye cikin damuwa shima, “Kai Salman kiramin Dr Tayyib, ke kuma Aamilah kiramin maigadi, ai bazai rasa sanin wanda ya ajiyeta ba”.
         Babu jimawa maigadi da Aamilah suka dawo falon, cikin girmamawa Maigadi ya rusina yana gaida Mom. Bata amsa masaba, sai Dad ne ya jefa masa tambaya, “Yaya akai Mamana ta dawo gidan nan?”. “Wlhy Alhaji ban saniba, kawai naji nishin mutumne a jikin gate, shine na leƙa nama zata ko yaran nanne masu addabama mutane, sai naci arba da ita kwance jikin gate ɗin, sai kuma ƙurar mota da nake zargin a ita aka ajiyeta”. Ran Dad ya ƙara digunzuma sosai, yay ma maigadi nuni da hannu alamar ya tafi kawai.
     Maigadi na fita Dr Tayyeb na isowa gidan, bai zaman ɓata lokaciba ya shiga bama Shahudah taimakon gaggawa bayan an kaita ɗakin Mom an kwantar a gado. Duk wani taimakon da ake buƙata Dr Tayyeb ya bata, ya kuma tabbatar musu da cewar babu wata matsala normal zata farka insha ALLAH, ruɗanine ya sakata shiga wannan halin kawai. Hakanne ya basu ƴar nutsuwa, har suka kira su Mama Atika suka sanar musu dawowar Shahudah ɗin.

          Normal Shahudah ta farka a safiyar yau kamar yanda Dr Tayyeb ya sanar musu, kasancewar ɗaki ɗaya, gado ɗaya ta kwana da Dad da Mom sai suka baibayeta da tambayoyi akan abinda ya faru da ita?. Tsaf ta kwashe yanda akai ta sanar musu.
         “Dad ashe shiɗin ba mijina bane, tunda ya tafi dani wani gida ya kaini kawai ya ajiye bamma sake ganinsaba sai bayan kwana huɗu, ya sanarmin a randa aka ɗaura mana aure a ranar Bb ya saka shi ya sakeni, yace dan kawai yana ganin mutuncinsa yay hakan, amma badan Bb bane wlhy ko za'a kashesa bazai sakeni ba, kuma koda ya sakeni badan na taɓa zama matar Bb ba da bazai ƙyaleniba sai ya ketamin mutunci, wai Bb yana da kimar da bazai iya mu'amulantar abu shima yayi hakanba, Mom wlhy Bb mutumin kirkine, dan ALLAH ku bashi haƙuri mu koma aurenmu kamar da, ALLAH yanzu na amince zan haihu ko nawa yake so”.
     Mom da Dad da mamaki ya cika suka kama hannayenta cikin nasu, cikin zafin rai Mom tace, “Zaki koma gidan Jawaad kuwa Shahudah, zaki koma kodan shegiyar yarinyar can tasan asirinta ai

kin banzane, namiki alƙawarin a yau ɗin nan basai gobe ba za'a maida aurenku da Jawaad”. “Mom da gaske? Dad kaima kuma ka yarda da hakan?”. “Ɗari bisa ɗarima kuwa mamana, duk abinda kikeso a duniyarnan saikin samesa ko minene shi, duk abinda Momynku ta faɗa kisa a ranki ya gama tabbata”. Rungume Dad tayi tana fashewa da kukan jin daɗi, suma suka rungumeta cike da so da ƙauna harma da tausayinta.
          Gari na ƙarasa wayewa Mom ta ɗauki Shahudah suka tafi family house ɗinsu.

______________________________
      BEEJAY
______________

           Da ƙyar muka iya tashi sallar asuba, musamman ma ni da jikina ke ciwo ta ko ina, idanuna sunmin nauyi sosai na rashin barci da kukan da na sha. To nidai bansan randa zan zama jarumar ba, duk yanda zan fasaltama mai saurarona zai ga kawai nacika rakine da ragwanta, amma ni kaɗai nasan sirrin al'amarin kawai.
     Da taimakonsa mukaje bayi badan bazan iya tafiya da kaina bane, hakan kawai shi yaso shiyyasa ya kamani muka shiga tare. Tare mukai wankan da bamu samu damar yi ba saboda tsabar barcin da yaci ƙarfin idanunmu, muna fitowa ya fice daga ɗakin.
      Tsaye nai ina tunanin ta'ina zan fara ne? Bani da wani kayan sakawa a ɗakinsa sai abinda baza'a rasaba, tunanina ne ya katse jin motsin mutum da sallama ciki-ciki, ya ajiye kayan dake hannunsa kusan kala bakwai, sai leda da alamu ya nuna kayan barci dana cikine a ciki, ajiyar zuciya naɗan sauke, bai jira cewataba ya sake ficewa.

           Ana idar da sallar asuba ban zaunaba, ina ƙoƙarin tashi ya shigo ɗakin da sallama, da alama ko azkar bai zauna yiba balle ai maganar motsa jiki, jallabiyar jikinsa kawai ya zare ya ajiye ya haye gado, matsawa nai na gaishesa, batare da ya amsa minba ya jawo hannuna na faɗo kansa, “Ouch” ya faɗa a hankali alamar yaji zafi, ɗan kallonsa nai sai kuma na kumbura baki. Hancina yaja yana wani lullumshe idanu, ya birkiceni na koma ƙasa fuskokinmu daf da juna muna shaƙar iskar numfashin junanmu. Cikin yin mar-mar da idanu na tsoro nace, “Ina kwana?”. Shiru yay kamar bazai amsaba yanzunma, yanata ƙarema fuskata kallo, ya sumbaci goshina yana sake ɗagowa da ƙoƙarin saka idanunsa cikin nawa amma naƙi yarda da hakan. Saima ɓata fuska nai ina faɗin, “Abinci zan ɗora fa”. “Da wane ƙarfin?”. Ya faɗa a ƙasan maƙoshi, dan koni dake daf dashi badan ina kallon lips ɗinsa ba ba lallaine na fahimtaba. “Da nawa mana” na bashi amsa nima ciki-ciki. Nauyinsa ya ɗan sake sakemin yana faɗin, “Oh ni kika raina kikema raki dama kenan?”. Tuni idanuna sun fara tara ƙwalla, “ALLAH zaka kasheni”. Nai maganar a rarrabe dan na fara sauke numfashi da ƙyar. Yi yay kamar zai ƙarasa sakarmin nauyin sai kuma ya ɗagani yana dunguremin kai. Nannauyan numfashi na sauke ina lumshe ido irin na ALLAH na gode makan nan. Na yunƙura zan tashi ya maidani ya sake kwantarwa. “Barci” ya faɗa a cikin kunnena. “Idan nayi barci sukuma mi zamu basu suci?”. “Shiiii!!” ya faɗa batare da ya bani amsata ba. Shirun kuwa nayi ina masa kallon mamaki, yaja bargo ya lulluɓemu da shi tare da sakani a cikin jikinsa, a hankali ya furta, “Thanks you Miemaa”. Bansan dalilin godiyarba, dan haka na sake lafewa a jikinsa nace, “For What?”. “For Everything Zinaran” Ya bani amsa da wani irin salon da yasa tsigar jikina tashi. Sake lafe masa nai a jiki ina shaƙar mayataccen ƙamshin turarensa da akwanakin nan yakemin daɗi fiye da komai. barcin mukeji, dan haka kafin wani dogon lokaci yayi gaba da mu.

            Barcin da su Umm-Anum suka gagara yinsa a daren jiya yau suna idar da salla suka nema yinsa, koda Jay da Anuwar suka shiga gaishesu sama-sama suka amsa musu, Jawaad da yasan za'a rina yaja hannun Anuwar suka fito. Dama yasan ai wannan barcin sai sunyisa dan shi ba'a cin bashinsa daman.

        Kasancewar na kwanta da maganar abincin a raina sai barcina baiyi tsahoba na tashi, a hankali na zare jikina daga nasa na sauka a gadon, badan barcin ya isheniba na tashi, zuciyatace kawai bata aminta dana kwantaba bayan gida cike da baƙi. Ina fitowa babban falo naci karo da kulolin abinci, da mamaki na isa garesu na bubbuɗe, lafiyayyen breakfast ne a ciki wa

nda ya fito shar kamar ka zauna ka cinye kai ɗaya. Mamaki ya kamani na inda ake kawo wannan abincin? Sanin bani da mai bani amsa sai kawai na shiga kwashesu zuwa kitchen, na dawo nahau gyaran falon zuwa falonsa da nawa da duk inda dai bazan takurama masu barciba. Kafin su tashi na shirya abincin a falona na koma nayi wanka na na shirya tsaf cikin zani da riga na atanfa da sukaimin ƙyau.
      Jinai kamar ana kallona, na juyo da sauri na kalli gadon batare dana ƙarasa ɗaurin ɗan kwalin ba. Boss dake kwance idanunsa a kaina ƙyam ya ɗan lumshesu ya sake buɗewa a kaina cike da salo. “Dama ka tashi?”. Kansa ya jinjinamin kaɗan batare da yace komaiba. Ɗan kwalinma sai naji na kasa cigaba da ɗaurasa saboda idanunsa duk sun takurani, haka dai na daure na ƙarasa na miƙe har lokacin idanunsa a kaina. Toilet naje na haɗa masa ruwa na fito, yanzu kam zaune na iskesa a bakin gado da waya a hannu. “Ga ruwan wanka can”. Kansa kawai ya girgiza min, batare da yace komaiba. “ba yanzu zakayi ba?”. ajiye wayar yay ya ɗago yana kallona, “Barshi idan naci abinci zanyi, bara na duba saƙon nan da Jabeer ya turo min” yay maganar yana miƙewa ya nufi Computer ɗin dake a ɗakin inda ya gyara a can gefe tamkar wani ɗan office. Da kallo kawai na iya binsa, danni mamaki yake bani yanda sam bai gajiya da aiki. Komai banceba na gyara gadon kawai na fice daga ɗakin.
            A falo na iske Aunty Batool ta fito cikin shirin fita, na bita da kallon mamaki da alamar tambaya. Murmushi tamin kaɗan tana gyara mayafinta, “Zanje gida saboda abincin Alhaji babba, naga Ummah ganin ƴar uwarta yama mantar da ita”. Murmushi nayi, “Ah haba aunty Batool itama nasan ba mantawa tayi ba, kawai dai tana cikin yanayine mai wahalar fassara, to mizai hana ki ɗiba masa na nan? Idan kuma wani ya keso daban ai saina girka masa yanzun nan insha ALLAH”. “A haba, wahalan ai sai yayi yawa, bara kawai naje can ai zan dawo, koda yake nama san acan kuma yau za'a yini ma”. “A'a dan ALLAH, muje kiga na nan ɗin dai aunty Batool, shima idan yaji kin tafi can dan kawai dafa abincin baba ai bazaji daɗiba”. Nai maganar ina marairaice mata.
       Da ƙyar na samu ta amince mukaje kitchen ɗin, duk abinda tasan zai iya ci shi ta ɗiba masa, ta zuba a kwando ta fice riƙe da key ɗin motar da sukazo a ciki.

        Coffee na haɗa na koma kaima Boss, yanata aikinsa hankali kwance, na ajiye ɗan tray ɗin dana ɗora ƙaramar butar shayi da kofinta sai cokali a gabansa, tsiyayawa nai na miƙa masa, batare da ya kalleni ba ya amsa yana faɗin, “Waye ya fita da mota?”. “Aunty Batool ce” na bashi amsa a taƙaice. Baice komaiba yakai kofin bakinsa, ɗayan hannunsa kuma yana amfani da mouse.

★★★★★★
Chapter 141 · 0% Book details