← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 168

Sashe 113

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

..................A harabar gidan suka iske Alhaji babba zaune alamar isowarsu daman yake jira, kafin ma Sadiq ya fito ya buɗema Jay shi harya buɗe da kansa ya fita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙarisa ga kakan nasa da tun shigowar motar gidan ya ajiye jaridar dake hannunsa. Cike da zolaya Alhaji babba yace, “Kai angon nanfa kamin wayo, gaskiya nima azo a nomin ƴar bana bakwai auren nan zanyi ko kaurin wuya na ƙara da jar fata”. Sosai Jay ya ƙyalƙyale da dariya, ya zauna akujerar robar dake gefen Alhaji babba yana faɗin, “Duk gasarka dai ba zaka samo cancaɗeɗiya kamar tawaba Alhaji, domin tawa fa ta musamman ce”. “Ni dai banason cika baki, kar nan da wata biyu inga ka faramin zarya a gida ehe”. “Ai bama zanyin ba, sai dai kai ka ringa mana saboda zuwa cin tuwo”. Dariya suka sanya a tare, Jay ya rissina ya gaidashi cikin girmamawa, kafin su miƙe cike da farin ciki. Sadiq da shima tuni ya fito a motar ya rissina ya gaida Alhaji babba. Cike da kulawa ya amsa masa tare da sanya masa albarka. Jawaad ya buɗema kakansa mota da kansa, sai da ya shiga ya maida ya rufe sannan ya zagaya inda Sadiq shima ya buɗe masa. Kasancewar tun fitowarsu Jay ya bama Sadiq address ɗin inda suka nufa sai kawai kaka da jika suka cigaba da hirarsu, yayinda Sadiq keta aikin tuƙi abinsa.
Tun a farkon shigowa layin Sadiq yay tambayar gidan Malam ɗan inna. Kasancewar sanannen gidane kuma anga mota mai ƙyau dan danan suka samu rakkiya har ƙofar gidan. Gidane irin da ɗin nan, dan daga ƙofar gidan zaka iya kallon babban zaure dake da ƙatan murfi ja wanda wahaka ta sakashi komawa mai roɗi-roɗin baƙi. Sadiq ne kawai ya fita, cikin alnajiran dake zazzaune bisa dakalin gidan wasu na karatu wasu na rubutu a alluna wasuma hirarsu sukeyi ya ƙarisa. Duk idanu suka zuro masa, ya ɗaga musu hannu alamar sannu sannan yace, “Ƙannena dan ALLAH ko malam ɗan inna na nan?”. Babban gardi dake karatu da sauri-sauri tamkar zai haɗiye harshensa ya dakata yana kallon Sadiq ɗin. “Malam baya nan, amma ba nisa yayiba”. Sadiq dake saurarensa yace, “To masha ALLAH, dama baƙine muke tare dasu gasu a mota, idan babu damuwa ko za'a aika wani ya kira mana shi ne?”. Gardin baice komaiba ya gyara zaman allonsa ya sakko daga dakalin, zauren gidan ya shiga, babu jimawa sai gashi ya dawo. “Ku shigo” ya faɗa kawai yana kallon Sadiq. Sadiq baice komaiba ya juya ga motar, a saitin Jay yay knocking glass ɗin, Jawaad da gaba ɗaya hankalinsa na'a tattaunawa da Alhaji babba ya juyi tare da sauke gilashin motar. “Oga yaronsa yace baya nan amma bai nisaba, yace kushiga ciki inaga zaije ya kirashi ne”. “Okay” Jawaad ya faɗa a taƙaice yana maida kallonsa ga Alhaji babba dake saurarensu.
Kusan a tare suka fito, a take dukkan almajiran dake wajen suka zubo musu idanu, sannu kawai suke musu babu batun gaisuwa, su dai suka shige cikin zauren dake ƙaton gaske, sai dai ko'ina mulmule yake da suminti, sai alluna masu yawan gaske dake jijjingine da kowacce kusurwa ta bangon zauren. Zama sukai a tabarmar da aka shinfiɗa, Sadiq dai dama bai biyosu ba sai Gaddin nan kawai. Saida yaga sun zauna sannan ya shige wata ƙofa alamar cikin gidanne, babu jimawa sai gashi ɗauke da kofin silba babba. ya ajiye a gabansu sannan ya gaishesu. “Bara naje na kirashi yana nan ƙasan layi suba wata mata mara lafiya”. Alhaji babba ne kawai ya amsa masa, ahi Jay ma dai kallon Gaddin yake cike da nazari.
Kusan mintuna talatin da fitar gaddin nan sai gashi ya dawo tare da Dattijo, daka gansa kasan akwai wahalar rayuwa tattare da shi, dan tsufan nasa yafi shekarun yawa a zahiri. Tun shigowarsa Alhaji babba ya shaidashi tsaf, dan kamanninsa na ƙuruciya duk suna a tare dashi, ya ɗan murmusa yana sake girmama buwayar UBANGIJI.
Sannu da zuwa shi dai malam ɗan inna keta zuba musu, ya zauna saman buzunsa dake fuskantar su Jawaad, shima dai kallon sani yakema Alhaji babba, sai dai ya rasa a ina yasan fuskar ne?. Hannu ya fara bama Alhaji babba suka far gaisawa, sannan ya miƙama Jawaad shima suka gaisa. Cikin ɗan tsantseni yace, “Sai dai kuma ban gane baƙin nawa ba duk da

ina musu kallon sani sai dai na rasa a ina?”.
Murmushi Alhaji babba yayi yana gyara zamansa, yace, “To bazan musa makaba, sai dai nasan ƙila kamanni kake gani kawai. Da farko dai sunana Nuhu. wannan jikanane sunansa Jawaad, munzo neman wani bawan ALLAH ne mai suna Adamu”.
Malam ɗan inna ya kafe Alhaji babba da kallo, dan yanzukam ya gano ta inda ya kema Alhaji babban kallon sani, to amma abin tambaya shi wanene? Haɗiye wannan tambayar yayi a ransa, a fili yace, “To Adamu dai biyu ke garemu, ɗaya muna kiransa Ado, yanzu haka yana can balaguro kudu damu, shiɗin babban ɗanane, yanada iyalinsa duk suna man cikin gida tare damu, sai kuma ɗan ƴar uwata shima sunansa Adamu, amma ana kiransa Adamu makaho, shikam dai ALLAH yay masa rasuwa shekara kusan ta takwas kenan, matarsa ma ta rasu kafin shi”.
Su jay suna jira suji yace yana da ƴa sai sukaji yay shiru.
Alhaji babba daya haɗiye mamakinsa ya gyara zama yana faɗin, “Masha ALLAH, mu munzo neman Adamu makahon ne, ashema ALLAH yay masa rasuwa?”. “Tabbas ya rasu dalilin mota data bigesa”. Ƙwallar data cika idon Alhaji babba yasa bakin rigarsa ya share yana ɗan murmushi, “ALLAH ya gafarta masa shi da matar tasa”. Amin ya rabbi, da Alhaji ɗan inna suka faɗa a tare.
“Mahaifiyarsa fa ko ita tana raye? Sannan shi baibar zuri'a ba ne?”. Alhaji babba ya faɗa cikin ƙarfin hali.
Alhaji ɗan inna ya jinjina kansa, “Mahaifiyarsa ta jima da rasuwa, dan dalilin jinyane ma ya maidota gida saboda shekaru da dama ba'asan inda takeba ita da ɗan nata, sai kawai rana tsaka muka ganta tare dashi, adalilin jinya ya matsa suka dawo gida, dan shi makanta ta samesa ta idi ɗaya tun ƙuruciya dalilin ƙyanda, to ganin inda suke babu mataimaki sai ALLAH ya matsa mata harta faɗa masa tushenta suka dawo, kowa ƙin yarda ta raɓesa yay a cikin dangi, sai nine na bata masauki a gidana, na kuma riƙe shi Adamun tamkar sauran ƴaƴana har nai masa aure, bayan aurensa da shekara kusan huɗu ALLAH yay ma yaya Sa'a rasuwa. Shi adamun da anan cikin gidan nawa suke zaune shi da matar tasa mai suna Asiya, itama tanada nakasar ƙafa dan gurguwa ce. Daga baya kuma sai suka tashi”.
Kafin Alhaji babba yay magana Jay yay saurin faɗan, “Miye dalilin tashin nashi? Sannan kuma basu da yarane? Naji baka amsa wannan tambayarba”.
Malam ɗan inna yaja fasali yana sake gyara zamansa a karo na babu adadi. “Mudai a saninmu Adamu baida wasu ƴaƴa, amma kuma al'amarinsu dalilin wata ƴa ƙwallin ƙwal yazo ma mutane da ruɗani musamman lokacin da tai girma kamanninta da nashi suka fita. Tun aurensa da Asiya bata taɓa ko ɓatan wata ba a gidanan, danni da kaina nan nasha basu taimako akan hakan ko za'a dace, amma har bayan rasuwa yaya Sa'a da kusan shekaru uku babu wani bayani daga matarsa, hakanne ya saka muka fara masa kwaɗayin kozai ƙara aure. Amma ya murje idonsa yace baisan wannan zanceba shi yana son matarsa. Munta lallaɓashi akan inma kuɗin auren yakeji karya damu zamu haɗa muyi masa, tunda dai maganar ciyarwa daga iyalina ake basu abincin dare da rana, na safe kawai yake samowa da yake yana ƴar sana'arsa ta gyran tsummokara. Sam bai saurari kowaba, dama yaga an takura masa da zancen sai kawai rana tsaka yazo mana da maganar zai tashi ya samu ɗakin haya a wata anguwa dalilin abokinsa. Munsha mamaki sosai da al'ajabi, dan bamuyi zaton gatan da muke masa har yakai abin zafin da zaiyi tunanin yin nesa damu ba. Hakan ba ƙaramin sqkamu ɓacin rai yayiba ainun, musamman ma ni da nake ganin na taimakesu shiga mahaifiyarsa a lokacin da kowa ya gujesu. Cikin fushi nace yaje abinsa, amma karya sake tunawa dani matsayin ƙanan mahaiyarsa tunda ya zaɓi mace sama damu. Suma sauran dangi duk sukai masa wannan furucin.
Baiko nuna yaji ko ɗarba ya tattara matarsa daƴan komatsansu sukabarmu zuwa can nesa damu sosai. Tunda suka tafi bamu sakejin ɗuriyarsu ba sai bayan shekara biyu sukazo mana nan matar tasa da ciki ƙarami, da farko kowa yaƙi saurarensa, amma ni saina sauraresa ganin abin farin cikin da matarsa ke tare dashi, shima ya nema gafararmu dukda wasu a cikinmu basuce dashi sun yafe ɗin ba. Matarsa ta cigaba da rainon ciki lokaci-lokaci sukanzo gaishemu, hak
Chapter 113 · 0% Book details