← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 168

Sashe 115

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lallashin Jawaad Alhaji babba yay tayi cikin hikima, tun yana baɓɓata fuska na shagwaɓa harya sake yana masa murmushi, gida suka maida Alhaji babba, batare da sun shigaba Sadiq yay reverse suka sake barin anguwar. Daga nan inda ya ajiye ɓaleru suka nufa kuma.
Tun shigar Jay ɗakin da ɓaleru yake jikinsa ya fara ɓari, ya ajiye abincin da yake ci gefe yana zazzare idanu, da hannu Jawaad yay masa nuni da abincin alamar ya ɗauka ya cigaba da ci. Babu musu ɓaleru ya ɗauka teakaway ɗin yana cusawa kamar yanacin maɗaci saɓanin yanda abincin ya fara masa daɗi da farko.
Ɗauke kai Jawaad yay daga garesa, saida ɓaleru ya cinye abincin tas ya ajiye batare da yaci kifin cikiba, ”Shikuma wannan waka barwa?”. Jawaad ya faɗa yana tsatstsaresa da idanu murya a kausashe. Ɗauka ɓaleru yay da sauri ya hau ci, ALLAH dai ya taimakesa ƙaya bata maƙale masaba ya gama lafiya. Hannu yaje ya wanko ya dawo, ya maƙure jikin bango hantar cikinsa na kaɗawar tsoro, dan har yanzu baibar jin ciwon jikin dukan daya shaba ranar. Jawaad ya ajiye wayarsa yana kallon ɓaleru da ƙyau. “Ka shirya faɗamin gaskiya ko sai mun sake kalar wasan ranar?”. “Wlhy duk abinda kake buƙata inhar na sanshi zan faɗa maka oga”. “Tunani mai ƙyai” Jay ya faɗa yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. “A gidan wa kake aiki?”. “Mr Gebrail”. “Waya sakaka ka ɗauki Gimba a mota?”. Inda inda ɓaleru ya nema farawa Jay ya daka masa tsawa, “Wlhy ko sau ɗaya kamin ƙarya saina karyaka a wajenan na ɗauraka”. Sanin Jay zai iya aikatawa yasa ɓaleru haɗiyar yawu muƙutt, “Uh.. Uh... Uhmm ni dai kawai wata safiya ne aka kirani da kwatanta mini shi, bammayi zaton shi bane saida naje zan ɗaukesa”. “Waye ya kirakan?”. “Mr Gebrail ɗin”. “Ina ka kaishi?”. “Wlhy acan titin ƙatshen gari ya tareni ya amshesa?”. “Kenan dama ka saba musu irin wannan aikin? Koma shi kake musu?”. “Oga Wlhy.....” “Amsa kawai nake buƙata, duk abinda yazo a saɓaninta kai kuka da kanka”. Kansa ya ɗaga da sauri yana karkarwa. “Shi da waye suke sakaka? Kuma wanene ya kaika aiki gidansa?”. “Ɓaleru ya share hawayen da suka cika masa idanu, “A anguwar da gidan drama ɗin nan yake yake gini, wataran yazo wajen shine ya ganni”. “Sai kawai yace zoga aiki na baka?”. “A'a nine da kaina naje na tambayesa saboda a lokacin aikin nake mema, to da yake ina ɗibo yashi daga can wani rafin dake ƙasan anguwar ina kawoma masu gini na saya, lokacin ana aikin gininsa kuma nine mai ɗebo musu yashin, sai naji yana tambayar Engineer ɗin ko yasan wani driver? Dan yanason ɗaukar driver, drivernsa ya ajiye aiki saboda tsufa, to ahinefa nace zanyi da yake na iya mota. Da farko yayi kamar bazai ɗaukeniba sai kuma ya bani key yace na gwada ya gani, a take na amsa na shiga motarsa naɗan zagaya wajen, a lokacinma bai amsa zai ɗaukeniba ya tafi, sai bayan kwanaki biyu harma na fidda rai sannan yazo yace ya ɗaukeni”. “Daga nan sai ya maidaka kidnapper ko? Har takai kuɗi ya rufe idonka aka haɗa baki dakai aka kashe abokinka ɗan garinku?”. “Wlhy oga bada ni aka haɗa baki aka kashesa ba, hasalima nima mutuwarsa kawai naji, wlhy tunda gimba ya rasu ban sake samun kwanciyar hankaliba, oga ina tsaka mai wuya”. “Ai bama ka shigaba tukkunna indai tsaka mai wuya ce. Ya akai ka tuƙa Alhaji Kokino ranar kuma?”. “Alhaji Kokino kuma? Wlhy ni bamma sanshi ba”. “Humm kana wasa dani ko?”. “Wlhy oga da gaske nake maka”. Jay baice komaiba ya ɗauka wayarsa, hoton da yay musu lokacin da traffic light ya tsaidasu ya nuna masa, ɓaleru yace, “Aiho, ai yaje office ɗin Mr Gebrail ne sakan kasuwanci sai motarsa ta samu matsa, shine drivernsa ya ɗauka ya kai wajen gyara, to bai dawo da wuriba shi kuma ya gaji da jiransa shine yace na kaisa gida, wannan shine dalilin da yasa ka ganmu tare”.
Kafesa da kallo Jay yayi cike da nazarin maganarsa, bai sake cewa komaiba ya miƙe, fitowa yay abinsa. Ɓaleru ya bisa da kallo, daka ganshi kasan

a tsorace yake. Securitys ɗin dake kula da ɓaleru ya korama winning akan su kula dashi da ƙyau, duk kuskuren da aka samu sune zai fara hukuntawa. Daga haka ya shiga mota suka bar gidan.
Ganin lokacin sallar la'asar yayi saiya saka Sadiq tsayawa sukayi sannan suka ƙarasa gida.
★★★★
Bily na zaune da ƴammatan maƙwafta da suka shigo mata dan a gaisa asan juna ya shigo. Sannu da zuwa tai masa, suma suka shiga gaisheaa suna binsa da kallo tamkar wasu mayu. Kallo ɗaya yay musu ya amsa Sau ɗaya yay shigewar, miƙewa nayi, dan haka suma duk suka miƙe, sallama sukai man suka tafi, nai musu godiya nima sannan naje kicin na ɗauki kunun ayar da nayi na nufi ɗakin nasa. A bakin gado na iskesa zaune ya dafe kai, koda nai sallama bai ɗagoba yadai amsa mani. Naja ƙaramin table ɗin na ajiye. “Su wanene waɗanan?”. Ya faɗa batare da ya ɗago ba. “Nima ban sansuba, basu fi mintuna talatin da shigowaba, sunce min nan gidan maƙwaftan nan namu suke”. Amsar kofin dana miƙa masan yayi, yaɗa lumshe idanu sannan yasaka a bakinsa ya shanye gaba ɗaya alamar yanajin ƙishi sosai, kofin ya ajiye yana miƙewa, “Kidaiyi a hankali”. Ya faɗa yana cire maɓallan rigarsa. “Insha ALLAH zan kiyaye”. Na faɗa ina miƙewa.
Hannunsa ya miƙomin yana min nuni da rigar, dukda dai inajin nauyinsa haka na kama na taimaka masa muka cire, dan na lura shifa komai yafison ai masa. Na juya zan ajiye rigar naji kawai an kwasheni anyi sama dani, ina mamakin yanda ya ƙware da iya ɗaukar mutum babu ko ɗar, shi ko nauyina bayaji ma.
Ganin ya nufihanyar bayi nai saurin cewa, “Bandaɗe da yin wankaba fa ALLAH”. “Ke kika san wannan”. Ya shige toilet ɗin yana faɗa. Nidai balki naga ta kaina, inaji ina gani dole akai wankan nan, ni gaba ɗayama ya fara busarmin ido da salonsa. Haka mukai wankan muka fito, bayan mun kimtsa muka fita domin cin abinci.
★★★★★★★★
Yau kwanakinmu shida kenan da tarewa, zuwa yanzun bansan yanda zan lissafo muku abubuwan da boss ya koya minba, gaba ɗaya ya fetsarar dani, duk da dau bana fiddo zaƙewat dan akwai sauran lokaci, kunyarsa kuwa inajinta tamkar babu gobe, dan duk abinda zai sakani na masa inayi ina rufe idanu, mu'amular gadoce fa na kasa sabawa, dan duk sanda zaizo min babu fashi sai nayi kuka, har fargaba nake ya nuna buƙatarsa, duk da hutun amarci da aka bamu hakan bai hana boss aiki tuƙuruba a gida, ni kaina bai barni na hutaba, matan su Jabeer sunzo sun yinarmin, hakama su Safah an kawosu, Amina ma tazo ta yini randa matan su Jabeer sukazo, da yamma sai ga su Nazifa ma, maganar da muka tattauna ta sakani fahimtar sun shirya zuwanne dama, nayi farinciki sosai ganin maganar ƙungiya ta kankama, komai an kammala na shirye-shirye a satinan za'a fara fidda komi ta kafafen yaɗa labarai da yanar gizo kamar yanda aka tsara, dan aomuke mu fito da zafinmu, ga bikin Nazifa nata matsowa ita, dan ƙarshen wata mai kamawa ne.
Bayan tafiyarsu na gaji liɓis dan dan suma su Aliyun anan suka kusan yinar mana tare da boss, sauƙina ma basu bar gidanba saida suka tayani na gama komai tsaf gidan ya dawo normal, sanin ko nayi wanka idan ya dawo saina sake dole tare da shi dan kullum tare muke wankan dare sai kawai naƙiyi na dafa masa shayi na gyara fruit. Falonsa nakai komai sannan na shiga haɗa ruwan wanka, ina ciki kuwa ya shigo, sai kawai jinai an ringumeni ta baya. Murmushi kawai nayi na juyo muna kallon juna, murmushin shima yamin da kai hannu a.................🙄😣✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share

[1/14, 6:29 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Bilyn Abdull 📚:
Page 49

..............Kamar yanda Umm-Anum ta saba duk sanda takawa yazo Saudia ya kanzo har gidan su gaisa, domin dai a halin da take ciki su kaɗai takema kallon ƴan uwa, su kaɗai ta sani a yanzu sai mijinta sai ƴaƴan guda biyu, ta mance ita wacece? Ƴar wacece? Daga ina take? Daga ina ta fito?. Wani lokaci hikimar UBANGIJI kan sakata kawo wannan tunanin a zuciyarta, musamman ida tunaninta ya karaɗe ko ina a cikin duniya ta ga babu wanda ta sani sai ƴan Masarautar gagara badau, sai mijinta da danginsa dake anan, hakan kan ɗaure mata kai, sai dai duk yanda taso ta furta da baki kota tambaya bata iyawa. Idan hakan ta kasance takan zauna tasha kukanta ta share hawayenta.
Chapter 115 · 0% Book details