Sashe 151
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar Qaseem daya samo bullets da ƙyar cikin office ɗin nasa ya ƙara azama wajen ɗurasu cikin bindigar yana kuka shaɓe-shaɓe da hawaye. yana gama zuba bullets ɗin cikin bindigar Jay na buɗe ƙofar ya shigo da gudu, saurin ɗaurawa a kansa yay da rawar jiki yana ƙoƙarin saka ɗan yatsansa saman kunamar bindigar jikinsa sai tsuma yake.
Da matsanancin ƙaraji Jay yace, “Qaseem!!! Karkayiii!!!!!” yay maganar cikin wani irin doka mahaukacin tsalle ya dire gaban Qaseem ɗin da wawurar hannunsa yay sama da shi harsashin da Qaseem ɗin ya harba ya samu p.o.p ɗin dake office ɗin. Yanda Jay ya riƙe haka Qaseem ma yaƙi saki, sai da suka ƙarar da harsasan duk biyar sannan Jawaad ya ɗauke fuskar Qaseem da mahaukacin mari cikin gushewar hankali.
Wannan harbi shine ya maido hankalin su Sir Ahmad wajen, yayinda ƴan jarida da sauran mutane suka fara gudu sun zata hari aka kawo.
“Baka da hankali ne!!!? Wace riba kake tunanin samu a kashe kanka da zakayi Qaseem? Kaifa musulmine! Taya zaka bari tunanin aƙidar yahudu da nasara har takai mizanin tasirin zama a zuciyarka irin haka? kai ƙoƙarin salwantar da rayuwarka da kanka!!! Kasan kuwa hukuncin wanda ya kashe kansa a addinin musulunci?. To sunansa KAFURI!!! kuma wlhy WUTACE zata zama sakamakonsa!!!”. Jay ya faɗa yana huci da nuna Qaseem ɗin da hannu.
A zabure Qaseem ya hankaɗa Jawaad yay baya yana faɗin, “Bani da hankali Jawaad, wlhy da gaske na haukace, tabbas na haukace, minene amfanina idan na zauna a raye a wannan duniyar da babu komai a cikinta sai ruɗani?!!” ya finciko rigar Jay jikinsa na rawa, hawaye na zuba masa babu ƙaƙƙautawa, “Idan ka hanani kashe kaina mi kakeso nayi Jawaad? Wacce irin amsace dani da zan bama duniya akan mahaifin da nake kallo babu kamarsa a da? Matsayin suruki kawai ya taɓa amsawa a gareka amma akai maka gugar zana da halayyarsa yanzun, to inaga ni da yake mahaifina!!, da wane idan
un kakeson na sake kallonsa Jawaad?! Dan ALLAH na roƙeka ka barni na kashe kaina na huta!!”.... Ya ƙare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya da ya saka jijiyoyin kan Jawaad sake mimmiƙewa shima hawayen na taruwar masa a idanu. Jawo Qaseem yay ya rungume a jikinsa suka fashe da kuka a tare.....😭
(Kai jama'a, wlhy zuminci ya wuce gaban wasa komai lalacewarsa😭😭)
Dalilin go-slow da Mom ta riska a hanya yasa ta iso station ɗin a wahale cikin dogon jinkiri, da kutsa-kutsar shiga cikin ƴan jarida ta samu shiga ciki da ƙyar, inda shigar tata tai dai-dai da harbin harsasai biyar da Qaseem da Jawaad sukayi. Da wannan ruɗanin da jama'a suka shiga ta samu damar bin ayarin su Sir Ahmad zuwa office ɗin Qaseem dan ta sani, bata fahimci can su Sir Ahmad ɗin ke yunƙurin zuwaba saida taga sun isa tare da su inda itama ta dosa.
Itace farkon shiga office ɗin, sai tai tsaye turus tana kallon Qaseem da Jawaad dake rungume da juna da dauraren kalamansu.
“Qaseem hakan ba mafita bane ɓata ne, ba'a samun hutu da saɓon UBANGIJI bisa ganganci, ka daina irin wannan tunanin”. “Dolene nayi Jawaad, ƙo Bilkisu da tazo a ƙarshen ƙaddarar kunyarta nakeji balle kai da sauran mutane, nayi nadamar kasancewata jininsa wlhy Jawaad”.
Da sauri Momy tazo ta fincike kafaɗar Qaseem ta matsar da shi baya daga jikin Jawaad, batare da ta tsaya ta gama fahimtar matsalarba, jin sunan bilkisu kawai da tai a bakin Qaseem ya sakata harzuƙa da fassara matsalar akan bilkisun ne komai ke faruwa ma kawai, hawaye na zirar a kumatunta tace, “Qaseem wai mi kakeyi hakane? akan tsintacciyar mage, kake wannan hanƙoron da tura mana ƴan sanda gida saboda cin zarafinmu? Akan butulu da ya wulaƙanta ƴar uwarka har kake iƙirarin mahaifinka ya shirya tarwatsaka? TSINTACCIYAR MAGE! YARINYAR DA MUKA ƊAKKO A TSAKKIYAR RANA! YARIYAR DA......”
“Da haɗin bakinki kenan mijinki ke aikata komai!!” Qaseem ya faɗa cikin matsanancin fushi tamkar zai haɗiye Mom, baya tai da sauri jikinta na rawa, cikin rawar murya tace, “Qaseem anya kana cikin hankalinka kuwa? Miya samu kanka? Ko an sauya mana kai ne?”.
“Komai ma ya sameni fiye da yanda tunaninki ke baki ke da shi. Tun bansan kaina ba ke da shi kuketa nunamin banida wani maƙiyi a duniya sama da Jawaad, Why?. Mom! Nace Why? Shiɗin baɗan ɗan uwanki bane?, shi ɗin ba mijin ƴarku bane? Miya aikata mai zafine wai a gareku da har yau ban taɓa saninsa ba ni?......”
“Qaseem!!” Mom ta faɗa cikin tsawa tana fashewa da kuka.
Cikin ficewar hayyaci Qaseem yace, “Eh ki kira sunana koma sau dubune, gaskiyace bazan taɓa fasa faɗaba, to idanma baki saniba yanzu zan sanar miki, idan kuma kin sani bara na maimaita miki. Ita wannan tsintsiyar magen da kike magana MIJIN naki ya tsintota daga ranar ne dan ya jefata cikin abinda yafi ranar zafi, cikin wuta yay niyyar jefa mata rayuwa saboda cimma burinsa, mahaifinane shi amma nasha zarginsa da aikata abubuwa marasa ƙyau a cikin gidan nan, amma da naso ɗaukar mataki saina gaza hakan, na tabbata dukkan ƴan aikin da akai raping a gidannan shine yay musu.....”
Tsawa Mom ta daka ma Qaseem jikinta na matuƙar rawa, “Qaseem!! Mahaifinka zaka ƙullana sharri irin wannan saboda Jawaad da Bilkisu?”.
Da ƙarfi Qaseem ya daki tebir ɗinsa, kayan sama suka tarwatse, ya matsa gab da Mom yana nunata da ɗan yatsa ƙirjinsa na sama da ƙasa na kumburar zuciya. Ya cigaba da faɗin, “Tun kin nuna bakisan komaiba bara na faɗa miki to, tun lokacin da akaima ƴar matarnan Amina fyaɗe a cikin gidanmu na gaskata hakan a cikin raina, domin kuwa lemon da aka ajiye ta sha lemo ne da kaf gidan nan shi kaɗaine ke shansa, hakanma yasa ba'a ajiyesa a fridge ɗin kitchen sai na falonsa kawai, ko a falon ƙasa inhar baya ƙasar kwashewa kike ki maida masa sama, to tayaya akai ranar yaje kitchen har yarinyar ta gani ta ɗauka ta sha bayan shi mai shan ma baya nan? Abu na biyu sai da na ɗauki kwalin lemon a bola naje nai bincike akan ɗan sauran cikinsa na gane magani ne mai ƙarfi aka saka a ciki kuma a ƙalla ya kai kwanaki biyar da zubawa, abu na uku na zaun