← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 168

Sashe 32

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

batare da ya kalli waye ba ya ɗaga da hannunsa na haggu yasa a Hans free, daga can akai sallama, ya amsa cikin ladabi tamkar bashiba, “Ya mukai da kai ranar juma'a akan zuwa meeting ɗin nan Jawaad?”. yay saurin dafe kansa da faɗin, “Oh ALLAH, kayi haƙuri Uncle, naɗan fita wani wajene amma insha ALLAH gani nan zuwa”. “To ALLAH yasa” daga can aka faɗa ana yanke wayar. Huci ya furzar yana ɗan bugar sitiyarin, Na ɗan saci kallonsa na ɗauke kaina, sai kawai naga ya canja hanya saɓanin inda muke. Nidai ban iya cewa komaiba, domin ko wainar dake cikin tanda a yau ta fini samun freedom ɗin kanta. Sai da naga ya shigo layin gidansune na iya kallonsa tamkar zanyi kuka. “Sir wlhy nifa akwai inda zanje”. bai kulaniba, yay fakin a waje batare da mun shiga cikin gidanba, sai da ya kashe motar sannan ya juyo ya kalleni.
A bazata kawai naji yace, “Inga kitson”. “Uhyim!” na faɗa ina ɗago kai da sauri da waro masa idanu cikin tsagwaron firgicin jin abinda yace. Banga alamun shi ya fuskanci abinda yay ɗin kamar yanada ban al'ajabiba, dan ya wani sake haɗe fuska fiye da da.
“Karki cinyeni da idanunkin nan malama, ɗaukesu a kaina, zan ganine idan sun iya sai nake kai matata can”.
Fuska na kumbura cikin suɓutar baki nace, “Aunty Shahudahr da batason kitso ɗince zataje?”. Saukar yatsun hannunsa kawai naji kan laɓɓana ya ɗallamin da ƙarfi, azabar zafin danajine ya sakani saurin dafe bakin idanuna na cika da ƙwalla na kalleshi, ya dallamin uwar harar tamkar zai haɗiyeni da idanun, saurin maida kaina nayi gefe hawayen da suka cikan ido suka sami damar silalomin, dan da gaske naji zafi. kafin nagama fita daga zafinne, naji hannunsa saman kaina ya zame gyalen dana yana da hular, ya saukesu saman kafaɗata, yana faɗin, “Magulmaciya waye ya tambayeki to?”. Maybe idan nace muku kaɗan ya rage zuciyata ta fito ta baki a wannan lokacin bazaku yardaba, jikina kansa tsuma yake, lokaci ɗaya dukkan ilahirin gashin jikina ya miƙe domin jin ya ja jelar gashina dake ɗaure da ribbon yana faɗin “Ashe ba ƙwaiƙwaido bace?” yay maganar a can ƙasan maƙoshi yana ɗauka hular yana ƙoƙarin maidamin a kai, na rintse idanuna ina fisgar numfashi da ƙyar tamkar mai Asthma, ya ɗauka gyalenma ya naɗamin kamar yanda ya gansa sannan ya kalleni fuska a matuƙar ɗaure, yace, “Kalleni nan”. Daƙyar na iya juriyar ɗagowa na zuba idanuna cikin nashi, yanda ya kafeni da idanu sai na kasa jurewa nai ƙasa da kaina saboda wasu abubuwa danaga suna fitowa a idanunsa waɗanda ban taɓa ganiba, ga idon ya kaɗa da jaa kaɗan tamkar wanda yake cikin fushi. Cikin ɗacin murya da saukemin wata harara mai firgitarwa da ban mamaki yace, “Hankalinki ya kwanta waɗanda kika fitama tallan jikin sun gani harsun tanka, Saina sauyama wannan fuskar taki kamanni idan na sake ganin kin fita ba hijjab”. Yana gama faɗa ya buɗe motar ya fice abinsa batare da ya sake kallona ba.
Tamkar sokuwa haka na bisa da kallo, shiko ko waiwayena baiyiba har ya isa jikin ƙaton gate ɗin ya tura ƙaramar ƙofar ya shiga. Baya nai luuu na faɗa jikin kujerar na jingina bayana, ina sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanu, nace, ‘Na shiga uku ni balkisu’. naja kusan mintuna uku a haka kafin na samu numfashina ya dai-daita. Gaba ɗaya man kaina ya gama tsiyayewa, nama rasa yanda zan fassara abun nasa, nakai hannu na shafa laɓɓana da har yanzu sukemin zafi, sai kuma na buɗe ido na kalli mirror, har laɓɓana sunyi ja, a fili nace, ‘Mugu, aiko Yah Qassem dake dani bai kafan wannan dokarba saishi daga mijin Auntyna’. Sai kuma nai saurin dafe bakin na kalli inda ya tashi sai kace ancemin gashi ya dawo. Da sauri na sake rintse idanu da dafe kai, a fili na sake faɗin, ‘Ya rabbi ka kawomin ɗauki, Mutumin nan zai kasheni’. Sai kuma na harari ƙofar gate ɗin na buɗe motar da sauri na fice abina,
★★
Jawaad kam Haka kawai ya tsinci kansa dayin murmushi lokacin daya buɗe gate ɗin ya shiga gida, sai kuma ya taɓe baki tare da jan ƙaramin tsaki ya nufi sashen mama Atika yana ƙwafa mai nuna takaicin wani abu da har yanzu yake cimasa rai. yasan dai taron meeting ɗin bai wuce can ɓangaren mama Atika ba saboda shegen fitinar tsohuwar. Da sallama ya s

higa, suka amsa kusan su duka alamar shi ake jira, wani iri yaji a ransa saboda ganin harda kakansa dasu Umma, yadai samu waje ya zauna sannan ya gaidasu.
★★★★★★★
A LADIES MIRROR kuwa lokacin da abinda ID cards ɗin Bily suke ciki ya faɗi akan idon Safah ne, amma sai taƙi magana, sai da ta tabbatar bily ta daɗe da barin wajen sannan ta ɗauka tana faɗin, “Lah Aunty Meenal diba kiga auntyn nan da nace amin irin kitsontace ta yarda”. Duk kallonta sukayi, Amaturrahman ta dalla mata harara da faɗin, “Shine dan iskanci bakiyi maganaba sai yanzun?”. Baki ta tura gaba tana langaɓe kai gefe, “To ai mantawa nayi ko”. Amatullah tai dariya da cewa, “Kai Safah lamarinki sai ke wlhy, saiki bada a ajiye mata dan nasan zata dawo nema”. Da sauri tace, “A'a aunty Ama mu kai mata dai”. Marwah da tun ɗazun bata kula kowaba tanata game a ipad ɗinta ta harari Safah. Ramawa Safah tai, cikin tsiwarta data gada wajen Munaya tace, “Miye kike wani hararana ke kuma malama?”. Lips Marwah ta cije like Sarki Sameer, ta ɗauke kanta batare data tanka mataba.
Duk yanda sukaso Safah ta bada a ajiyema bily saboda idan ta dawo nema ma'aikatan wajen su bata fir taƙi, daga ƙarshe Amaturrahman tayi kiran Ummu ta sanar mata, Sarauniya Munaya dake kishingiɗe a kilisarta ana tausa mata ƙafa ta girgiza kai kawai da lumshe ido, babu abinda Safah ta bari na halayyarta, ta tabbatar kuma akwai dalilin da yasata yin hakan, a hankali tace, “Kubarta tazo dashi, sai a nema yarinyar”. Amaturrahman tace, “Ummu yanzu nan biye mata zakiyi?” yanke wayar Munaya tayi batare da ta bama Amaturrahman amsaba. Dole badan sun soba akabi abinda Safah keso sukatafi dashi bayan an kammala musu kitso su duka kamar yanda Ummu ta korosu suyi badan sunso hakanba..............✍

Maison zuwa gagara badau ya shirya muje gaida Sarki Sameer Saifudden da gimbiya Munaya😉😉lol.

ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/31/2020, 9:31 PM] Abubakar Saleh Kurami: Bilyn Abdull 📚:
Page 14

Guys ɗinan anya kunaso na mutu da idanuna?, kusan words dubu uku nakeyifa a kullum amma sai naji kuna farautar ƙari🤔, aradu inason ƙulla shekara ɗari da idanuna kuyi haƙuri😂🤣😂. Ga zaɓin lokacin posting, 11pm ko kuma 6am. Waɗanda naga sunfi rinjaye sai abi ra'ayinsu. Amma masu cewa dama Jay yana dariya?? nima kun bani dariya wlhy sosai, waye baya ya dariya a duniya, sai dai idan bata kamaba😂. Harda ƙyaƙyƙewa zakuji yayima wataran🚴🏼🚴🏼👌🏼.

Ina muku fatan alkairi😍😘😍😘😘😘.
Chapter 32 · 0% Book details