Sashe 117
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Saida sukai zaman awanni biyu cikin kuka da tashin hankaki sannan suka sami labarin farfaɗowar su, atake duk murmushi ya suɓuce musu, Bily ta saka gyalenta itama tana share hawaye kamar yanda Anum keta faman yi. Ba'a basu damar shiga ba dan duk ance suna buƙatar samun hutu musamman ma Umm-Anum da jikinta ya manyanta.
Da wannan albishir ɗin suka sami ƙwarin gwiwar tafiya yin sallar la'asar da lokacinta yayi, kowa ya shiga miƙama UBANGIJIN al'arshi kukansa dan shine masanin duk wani sirri dake a binne tare da rahama ga bayin da aka zalunta kuma suka jurema jarabawar rayuwa batare da nuna ƙosawarsu ba. Sosai yin sallar ya ɗan basu ƙwarin gwiwa suka dawo asibitin, Abbu ya roƙa takawa akan suje su huta haka nan tunda ance sun farfaɗo ai. Daƙyar Ummu ta yarda, Bilkisu kam ƙasa tai da kai tana hawaye alamar batason tafiya. Takawa yay murmushi da yima Ummu alamar a barta anan ɗin da ido.
Hakan kuwa akayi, bayan sun shiga sun duba su Jawaad da Umm-Anum suka tafi akabar Bilkisu da Anum da Anuwar anan, sai Aunty Mahfuzah, takawa kuma da Ummu da Amintacciyar baiwar Ummu da Abu-Siddiq suka tafi, sai Anuwar da Abbu suma suna nan. Suma dai bayan wucewar su takawan duk sai suka shiga suka dubasu suka sake fitowa suka zauna zaman jiran farkawarsu da musu addu'oi.
Kasa haƙuri Abbun su Anuwar yayi yaɗan farama Bilkisu wasu tambayiyi game da Jawaad da ita kanta, danshi tabbas yana kallon wasu abubuwan na Bilkisu masu mugun kamanceceniya da Umm-Anum, tafiya, murmushi dama abubuwa da dama tun a wancan zuwan nata, hakan sai yasa kansa ya ƙara kullewa ya shiga tambayarta ko auren zuminci akai musu ita da Jawaad?. kanta a ƙasa ta bashi amsa da “A'a”. Ya tisa (a'a) ɗin nan ta bilkisu a ransa yafi sau dubu, dan shidai gaskiya bai yardaba akwai abinda ita Bilkisun bata saniba maybe, musamman yanda yake mata tambayoyin da amsoshin da take bashi. Anuwar dai da Anum da Aunty Mahfuzah na binsu da kallone da saurarensu.
A haka lokacin sallar magriba yayi itama suka tashi suka gabarta, sun dawone suka iske Jawaad ya tashi, Abbu ne yace Bilkisu kawai ce zata shiga, badan Anuwar da Anum sunso ba suka haƙura.
Tunda na shigo ɗakin idanuna a kansa suke, shiko nasa a lumshe tamkar mai barci har yanzun, yana kwance ne, amma yanzu an ɗago gadon sama ta wajen kanshi yanda kwanciyar ta bada style kamar yana a zaune. Na cigaba da takawa a hankali na ƙarasa garesa, Zama nayi dai-dai saitin fuskarsa tare da ranƙwafawa na sumbaci goshinsa, hawayen da suka cikamin ido suka ziraro suka ɗiga akan fuskarsa. Buɗe idanun yayi a hankali tare da riƙo hannuna cikin nashi, kallon cikin ido mukaima juna, wasu hawayen suka sake silalo mani na tausayinsa, abinda ban taɓa gani daga garesaba sai yau, (kuka) Boss ne gwanin dauriya da shanye abu yay kuka, kai mahaifiya dabance a rayuwar kowanne ɗan adam, mahaifiya tafi gaban wasa, mahaifiya mutum mafi daraja sama ga komai ga ƴaƴa. Na ayyana a raina ina matsawa jikinsa na kwantar da kaina a ƙirjinsa ina fashewa da kuka, dan nima haka kawai sai naji ƙaunar tawa mahaifiyar da kewarta, Innat
a gatana, innata abar alfaharina da tinƙahona harma da taƙama a dukkan daƙiƙa ta rayuwata.
Jawaad da shima wasu zafafan hawayen da babu zato suka silalo masa ya ɗaura duka hannayensa saman bayanta ya rungumeta a jikinsa. Sunkai tsahon lokaci Bilkisu na kukan da shashsheka ta kasa ɓoyesa, Jawaad na kukan zuci da hawaye masu zafi da raɗaɗi. Buɗe ƙofar da akaine ya saka Bilkisu saurin ɗagowa dan ta zata su Abbu ne, shima babu musu ya saketa ta miƙe yana share hawayensa, itama nata ta shiga sharewa da bakin mayafin jallabiyar. Nurse ɗin daya shigo ya nema afuwarsu, dan ya jima yana sallama da knocking babu amsa, hakanne ya sakashi shigowa direct, dan tun daga can waje ta cctv'n da suke amfani dashi na ganin duk wanda ke a sashen da suke kula da shi ya gano ruwan da suka sakama Jay ya ƙare har jininsa ya fara zuƙa yana komawa cikin robar ruwan, shikam sam baima luraba saida Nurse ɗin ya kama hannunsa yana cirewa sannan suka gani shi da Bilkisu. Idanu taɗan ware waje na alamar mamaki, shikam sai ya lumshe nasa idanun ya maida bayansa ya jinginar kamar yanda yake da.
Nurse ya kammala komai sannan ya fita su Abbu suka shigo duba Jawaad ɗin. Sannu sukaita jera masa da addu'oi, shi kuma yana amsa musu da kai dan harshensa ya masa nauyi sosai har yanzu baijin zai iya furta wata kalma ga kowa idan ba Umm-Anun ba. A rikice Nurse ɗin dake tare da Umm-Anun ta shigo tana sanar musu ta farka itama amma bata cikin hayyacinta.
Rige-rigen fita aka dingayi a tsakaninsu, dan hatta da Jay ba'a barsa a baya ba shima. Tashin hankali kenan, yanda Nurse kusan biyar ke riƙe da Umm-Anum zai baka matuƙar tausayi, a take duk suka rufu a kanta banda Abbu dake tsaye kawai yana kallon yanayin nata cike da nazari, ajiyar zuciya ya sauke kafin yayma Nurse ɗin Umarni akan su sallamesu zasu koma gidan ciwon nata addu'a yake buƙata. Basu musaba dan sunsan shiɗin babban likitane mai bada magungunan musulunci wanda akema ɗakko marasa lafiya daga wata ƙasa mai nisa a kawo garesa balle matarsa kuma.
A take aka shirya musu maidata gida. Hankalin Jawaad yay matuƙar sake tashi ganin mahaifiyarsa ta koma cikin asalin halin hauka kamar yanda tabar gida a wancan lokacin, su kansu su Anuwar ɗin hankalinsu a tashe yake dan basu taɓa ganin Ummunsu a wannan irin halinba, sundai san tanada wani rashin lafiya da takan fita hayyacinta lokaci-lokaci amma basu taɓa sanin dalilin motsawar ciwon nataba suma, da kuma Abbu ya dage kanta saita dawo normal kamilar mace. Anuwar yasha tambayar Abbu amma bai taɓa sanar masa komaiba sai yace lokaci na zuwa da zai sani.
Da isarsu gida Abu-Siddiq da Abbu suka rufi kan Umm-Anum da karatun Al-Qur'ani mai tsarki, hakanne ya ja hankali su Jawaad suma duk sai suka ɗaura al'awa suka zauna sunayi su duka har Bilkisu da Anum, kai harma da ama'aikatan gidan da Aunty Mahfuzah da yaranta itama dukda ƙanana ne ba'a barsu a baya ba. A hankali Umm-Anum ta fara lafawa daga bige-bigen da takeyi, ta buɗe idanunta dake jajur tamkar garwashin wutane a cikinsu tana binsu da kallo. Ba ƙaramin tsorata idanunta suka basu ba, amma hakan baisa sun dakataba suka cigaba, maidawa tai ta sake lumshewa tare da kwanciya jikinta na wani irin masifar rawa, sai kuma ta fashe da matsanancin kuka. Turaren magani Abbu ya tashi ya kunna, hayaƙi ya fara fita yana baje ɗakin. Wani irin gunjin kuka ta fara maiban tsoro tana magana cikin muryar da dagaji kasan ba tata bace. “Ku daina ƙonamu, dan ko zaku shekara dubu kuna ƙonamu bazamu bartaba, zamu gama jiyyane a jikinta batare da mun bar aikinmu ba, alƙawarine rubutacce zamu kasance da ita har ƙarshen rayuwarta, dan haka kuma bar wahalar da kanku babu inda zamuje, bazamu taɓa saɓama shugabanmu ba har abada dan shima bai taɓa saɓa manaba bisa umarninmu...!!”. Sam su Abbu basu sauraresuba suka cigaba da abinda sukeyi, hakama su Anuwar basu fasa nasu karatunba, yayinda Abbu ya cigaba da zuba magani kala-kala na hayaƙi a cikin Burne. Tun suna ihu har suka koma kuka da magiyar a daina ƙonasu kar'a halakasu suba laifinsu bane sakasu akayi. Zuwa wani lokaci kuma sai tayi shiru sai uwar zufa take tamka
r an jiƙeta da ruwan zafi. Abbu bai dakata da abinda yakeba har saida yaji ta kirayi sunansa cikin sanyin murya. Ajiye abinda ke hannunsa yayi ya ƙarasa gareta ya ɗago, faɗawa tai jikinsa ta fashe da kuka mai ban tausayi. “Abu-Anuwar yau cikin mafarki naga wani abu maiban mamaki da al'ajabi, naga mai kama da Anuwar wanda tabbas inada alaƙa dashi”.
Tashi Abu-Siddiq yay ya fita dan ya basu waje.
Abbu dake shafa bayan Umm-Anum yana murmushi yace, “Ba mafarki kikeba zahiri ne”. Zumbur ta miƙe zaune tana kallonsa, sai kuma tai saurin dafe kanta da taji ya sara mata. Kamata yay ya kwantar yana faɗin, “Kiyi haƙuri ki kwanta ki huta zuwa anjima ko da safe idan ALLAH ya kaimu sai muyi magana, Alhmdllh nafahimci mun samu wani haske saɓanin da da bama ki taɓa makamancin wannan maganarba”. Umm-Anum dai batace komaiba hannunta na dafe da kanta, ahaka barci mai nauyi yay awon gaba da ita, dukda anata kiraye-kirayen sallar magriba bai hanataba.
Sai da ya tabbatar barcin ya ɗauketa sosai sannan ya fito falo, Bilkisu da Anum yace su shiga suyi salla a ɗakin dansu dinga kula da ita, shi kuma suka fita tare da su Abu-Siddiq salla masallaci. Tunda suka fita salla Abbu ya fahimci Jawaad bayajin daɗi, dan daya kama hannunsa sai yaji zafi alamar zazzaɓi na neman rufesa. Baice komaiba sukai salla suka zauna har isha'i itama suka gabatar sannan suka koma gida. Har lokacin Umm-Anum nata barci, su Bilkisu da suma suka idar da salla suna zaune sun zuba mata idanu cike da damuwa.
Sashin baƙi Abbu yasa aka gyara, aka kaima su Jawaad abincinsu can, Abbu yace Anuwar yaje ya raka Jawaad itama Bilkisu Anum zata rakota.
________________________________
★★★★★★★★★★★★★★★★★★★