Sashe 102
Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Bayan sun idar fita yay daga ɗakin, babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke da madaidaicin kofi daketa fidda turiri. Kwance ya sameta a inda tai sallar ta ƙudundune da hijjab, tea ɗin ya ajiye ya ɗakko magunguna ya ajiye sannan ya ɗagota jikinsa harma ta fara barci, “Sorry, tashi kisha tea da magani saiki kwanta”.
Duk yanda na marairaice masa akan na ƙoshi bai saurareniba, sai da ya tabbatar nashaye tas sannan ya bani maganin nasha. Da taimakonsa na koma saman gado, harna fara lumshe idanu naji yana buɗemin jiki, sauri buɗe ido nayi da riƙe masa hannunsa ina ɓata fuska, dan nazata ƙarawar zaice zaiyi. “Na shiga uku, dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy ka maimaita mutuwa zanyi”.
Dukda ta bashi tausayi saida yaji dariya na neman kufce masa, ya dai daure ya haɗiye kayansa yana wani binta da kallon ƙasan ido, harta fara hawaye. Ɗauke idonsa yay daga fuskarta batare da yace komaiba ya maida inda yake son ganin.Ya kuwa ji mata ciwon da yay hasashe, sai dai bamai ɗaga hankali bane, amma zaiso a dubata gudun kuskure, tsabar son ya tsokane saiya ranƙwafo kanta kamar da gaske abinda take gudun zaiyi. jiyay kawai ta fashe masa da kuka jikinta ya fara rawa kamar wadda ta hango dodo. Dole ya danne dariyar da keson ƙwace masa ya rungumta. “Wasa nake miki niba ƙarawa zanba yi haƙuri”. Da ƙyar ya samu tai shiru har barci yay awon gaba da ita saboda maganin daya bata yana saka barci, ga kuma dama bawani isashen barci sukaiba. Sai da ya tabbatar barcinta yay nisa sannan ya gyara mata kwanciya ya sauka daga gadon bayan ya lulluɓeta da bargo. Dukda shima barcin yake buƙatar yi bai kwanta ba, wayarsa dake a drowan gefen gadon ya ɗauka ya fita falo.
10:30am
Ring ɗin wayarsa ne ya sakashi farkawa daga barcin daya ɗaukesa anan falon bisa doguwar kujera, kwance yake a rubda ciki, hakan ya sakashi miƙa hannu bisa centre table ɗin dake gab dashi ya lalubi wayar batare da ya buɗe idanunsa ba, guntun tsaki yayi sannan ya buɗe idonun da ƙyar ya kalli wayar. Ganin Jabeer ne ya sakashi ɗagawa yasa wayar a kunne, cikin muryar barci ya amsa masa sallama suka gaisa. Daga can Jabeer ya sanya dariyar shaƙiyanci, “A lallai boss Mamin mu batazo da wasaba, ka kalli agogo kuwa? Kaine da barcin safe har goma da rabi?”. Idanu Jay ya lumshe ya sake buɗewa akan agogon falon, kafin yace, “Kai ka sani dai ɗan sa ido” yay maganar yana tashi zaune da ƙyar. Dariya Jabeer yayi daga can, “Bari nakira anjima, dama akan maganar da mukai dakai jiya ne”. Jawaad ya ɗan sauke numfashi a hankali, “Karka damu gani nan zuwa station ɗinma”. Kafin Jabeer yace wani abu ya yanke wayar.
Ɗakinsa ya nufa inda ya tarar bily na barcinta har yanzu, sai da yaje gareta ya taɓa goshinta, zazzaɓin yaɗan sauka amma ba duka ba. Baice komaiba ya ƙarisa bayi domin yin wanka.
Shiri yayi cikin ƙananun kaya da sukai mas
a ƙyau, yana fesa turare ya jiyo ana knocking turaren ya ajiye ya fita, yasan bazai wuce Nabeelah ba, dan ya kira Ummah yace ta turo masa ita, Ilai kuwa itace ɗin tsaye a bakin ƙofar, Nabeelah da Ummah ta sakata zuwa akan dole kawo breakfast taja baya ganin Yah Jay ne ya buɗe ƙofar yau da kansa, saurin durƙusawa tai ƙasa tana faɗin, “Yayanmu dan ALLAH kayi haƙuri, na tuba wlhy bazan sakeba, ranarma suɓutar bakine”. Shi dai baice mata komaiba ya bata hanya ta shigo, juyawa yay ya koma ɗakinsa. Ta sauke ajiyar zuciya da ƙarisa takowa cikin falon sosai, basket ɗin hannunta ta ajiye saman centre table ta zauna tana waige-waigen ta inda Bilkisu zata fito, zamanta babu jimawa ya fito daga ɗakin yana waya, basket ɗi data ajiye ya yaye ɗan ƙyallen da aka rufo a kansa, kulolin ya buɗe duka, baice komaiba ya zauna a kujera da faɗin, “Tashi Ki haɗa min coffee”.
Nabeelah da aka nutsu kamar ba itaba tace, “to” tana miƙewa, tasan wannan ƙyaletan da yay ba yana nufin ya bartaba, akwai abinda yake shiryawa, Ummah ce dukta jamata, tayi alƙawarin bazata bari su sake haɗuwaba har sai bayan wata biyu, amma aunty Batool ita da Ummah yau suka zuga Abbah yace itace zata kawo breakfast. Ummah bata wasa wa yaranta akan aikin gida da girki, duk taɓarar Nabeelah da shegen surutu komai ta iya na mata, sai dai son jikin jaraba, wani lokacin sai Ummah tai mata wuju-wuju akan aiki take tashi tayisa. Kitchen ta nufa ta haɗa masa coffee mai daɗi kamar yanda tasan yanaso sannan ta kawo masa. Har yanzu wayar yakeyi, dan haka yaymata nuni da abincin da hannu. Komawa ta sakeyi ta ɗakko filet tazo ta haɗa masa abincin shima ta koma gefe ta zauna, tana son tambayar Bilkisu tana tsoron sake yin laifi a garesa.
Abincinsa ya cigaba da ci yana wayar har zuwa wani lokaci, kafin ya ajiye ya maida hankali ga cin abinci kaɗai. Ita dai tana zaune ne tanata satar kallonsa da gulmarsa a zuciya harya kammala ya miƙe yana goge baki da tissue, yay magana batare da ya kalleta ba. “ki tabbatar kin gyara gidan nan, idan kin tashi karki nutsu kiyi da ƙyau kinji, ki kuma tasheta da rawar kankin nan kiga yanda zan sauya miki kamanni”. Fuska Nabeelah ta kumbura tana faɗin, “ALLAH kuwa yayanmu ni yanzu na daina rawar kai”. Juyawa yay ya zuba mata harara ya nufi hanyar fita, harya kama handle ɗin ƙofar kuma sai ya juyo, “Idan ta tashi ki kirani”. “To yayanmu”.
Sadiq da tun ɗazun yazo gidan saboda kiran da Jawaad yay masa akan yazo zasu fita, ya taso daga wajen maigadi da yake zaune suna hira ganin Jawaad ya fito, sai da suka gaisa sannan ya buɗe masa ƙofar ya shiga ya zauna. Zagayawa yay shima ya tada motar suka fice a gidan bayan sun gaisa da maigadi daya buɗe musu gate.
Duk da ba aikine ya kawosa office ɗinba saida ya shiga suka gaisa da Sir Ahmad da yayta tsokanarsa. Office ɗinya ya buɗe ya shiga, komai tsaf babu wani datti sai ƴar ƙurar da ba'a rasaba. Yana zama babu jimawa su Aliyu na shigowa.
Yanda suke wani binsa da kallon shaƙiyanci ya sakashi haɗe fuska yana harararsu. “Malamai miye namin wannan kallon ƙurullar?”. Dariya duk suka sanya masa hatta Aliyu da bai cika tsokana ba. Jabeer yace, “Kuji kama kaifa jama'a, waya ce da kai wani abu anan dan ALLAH?”. Jay ya sake zuba masa harara yana ɗauke kansa, “Ai nasan zakuce ɗinne musamman ma kai da babu abinda ka iya sai shegen gulma ko mace ta shafa maka lafiya”. Yanzunma dai dariyar suka sanya suna cigaba da masa sherin wai ƙyallin angwaci yake kamar wata ɗan daren sha biyar.
Shiru yay musu sukai sherinsu suka gama sannan suka zauna.
Hafiz ya maida dubansa ga Jay dake duba file ɗin da Jabeer ya basa, “Boss wai mike faruwane haka? Gaba ɗaya mun kasa banbance komai tun daga yinin jiya har safiyar yau ɗin nan? Gashi kuma kazo office bayan munsan kana hutu?”.
Jawaad ya ajiye takardun yana sauke nannauyan numfashi, miƙewa yay ya ɗakko wani file a drawer bayansa, yana daga tsaye ya ranƙwafo ya dafe tebirinsa da duka hannayensa, dara-daran idanunsa da tun daren jiya haskensu bai gama dawowa ba ya zubamasu Aliyun, cikin ɗacin murya yace,“Hafiz nima wannan amsar n