← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 168

Sashe 103

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ake nema, nakasa fahimtar komai, komai sake ruɗar dani yake da dilmiyani a kogin ruɗani..... a daren jiya wani ya shigar min gida domin cutar da Miemaa, lokacin inacan wajen kama ɓaleru”.
       A tare suka ɗago suna kallonsa fuska cike da tashin hankali. Har haɗa baki suke wajen tambayar baidai cutar da itaba ko?.
      Kansa ya girgiza musu yana miƙewa tsaye sasai, “Babu abinda yay mata, sai itacema ta jijji masa ciwo, ta faɗamin a bubuwa da yawa masu kamanceceniya da yanda akaima matar Jabeer fyaɗe.
      Jabeer yace, “Boss da gaske?”. Kansa ya sake jinjinawa kawai yana mai datse haƙwaransa waje guda saboda azabar zafin da zuciyarsa ke masa.
      Su duka ukun tsaye suka miƙe, suma cikin zafin ran da akan daɗe ba'aga Jabeer da shi ba yace, “Boss anya ba Qaseem bane?”.
      Kafeshi da idanu Jay yayi kafin ya janye yana wani ɗan murmushi mai ƙona zuciya,  “Jabeer! Ba Qaseem bane, a yanzu bashi nake zargiba sam, tako wace siga na auna Qaseem bai hau mizanin bincikena ba, Idan har wanda nake zargi ya zama shiɗinne da gaske to lallai ƙungiyace dasu, dan adaren jiyan Miemaa ta samu nasarar cirar zobe daga hanun wanda ya shigo gidannan, kuma zoben tabbas na taɓa ganinsa a hannun kusan mutum huɗu, abinda ya kuma ɗauremin kai basuda wata alaƙar zahiri dake a bayyane su duka huɗun kuma”.
         Aliyu ne yay ƙarfin halin cewa, “To boss indai basu da alaƙar zahiri tayaya zamuyi tunanin haɗasu a kamanceceniyar laifi?”.
        “Ƙyaƙyƙyawar tambaya Aliy” Jawaad ya faɗa yana fuskantarsa da ƙyau, hannayensa duka biyu ya zura cikin aljihun wandon sa ya zagayo ya sake zama a kujerarsa. suma duk komawa sukai suka zauna.
      Jay ya ɗauki coffee ɗin da Hafiz ya ajiye masa yakai baki yana faɗin, “Akwai kamanceceniya mai yawa Aliy, musamman idan muka saka abubuwa da yawa da suka faru a tsakanin nan a mizani guda, babu abinda yafi ɗaukar hankalina wajen kamantasu sai maganar fyaɗen nan, dan haka zamuyi amfani da wannan damar mu canja salon bincikenmu. Fyaɗen da akaima Amina, Matar Jabeer, Nazifa, yayar Ummie, da ƴar mai aikin gidansu Nazifa daya faru kwanannan duk basu da banbanci, a tunani na hankali da yazo a zahirance zai bama mai nazari wahala wajen fahimta musamman daya kasance ba'a guri ɗaya al'amarin ya faruba, hasalima ba lokaci gudaba, idan har zamuyi aki da hankali kuma amsar ƙarshe itace ba mutum ɗaya ke aikatawa ba kenan. Da akwai aikin dana shirya dunƙule yaran suyi da, dan a jiya harma na sakasu zuwa gidana zamuyi magana sai ban koma gida akan lokaciba, to yanzu zamuyi amfani da wannan damarne, saboda su abin ya faru da wasunsu, sunsan zafi da raɗaɗin da akeji”.
           Cikin farin ciki Hafiz yace, “Wannan tsarin yayi wlhy Boss, amma nima ga tawa shawaran”. Gaba ɗayansu hankalinsu suka maida ga Hafiz ɗin, ya gyara zamansa sosai yanda zai faɗi komai dalla-dalla. “Kunsan a yanzu bazai yuwu kai tsaye mu iya binciko waɗanda akaima fyaɗe irin nasu ba, fitowarma fili zaisa masu aikatawar su ɗauki mataki suma, haka bayyanar yaran kai tsaye zai dawo da hankalin masu aikatawar kansu”.
      “Ƙwarai kuwa hakane Hafiz”.
“Yauwa to mizai hana mu taimakama yaran su buɗe wata ƙungiya haka ta ƙarɓar ƙorafin waɗanda akaima fyaɗen koma a wane yanayine, matanmu su zama sune masu ƙungiyar a bayyane, mukuma mu koma ta bayan fage wajen tsayawa tsayin daka ga masu shari'a su ringa yanke hukuncin daya dace cikin ƙanƙanin lokaci, na tabbata hakan zaisa mu sami dukkan damar da muke buƙata kodan sakacinma da kotuna keyi akan wannan matsalar, kunga mun jefi tsuntsu biyu da dutse guda, zamu sami abinda muke buƙata, zakuma mu taimaki yaran da ake zalinta musamman waɗanda iyayensu basu da ƙarfi akan tsaya masu bayan an cutar musu da ƴaƴansu”.
        Tafama Hafiz suka shigayi dan shawarar tashi tamusu yanda suke buƙata. A take kuma suka tsara komai yanda ya kamata. Suna cikin tattaunawar su Zuhrah suka iso office ɗin kamar yanda Jay yay kirasu tunkan ya baro gida akan su samesa nan.
       Ummie ce tai musu jagora har office ɗin na Jay, Sai da suka gaishesu duk cikin girmamawa kafin su basu izinin zama. Shine ya fara magana cikin dakewar nan tasa da

kowa ya sani musamman akan abinda ya shafi aiki, “Inason ku bani dukkan hankalinku nan”. A take duk suka sake nutsuwa garesa fiye ma da yanda yake buƙata.
         “Ku dukanku a yanzu zaku kasance wajen aiki ɗayane, ina mai gargaɗarku da bama buƙatar wasa, daga yau zaku ajiye wani ƙawancenku gefe kuyi aiki tamkar bakusan kankuba, zaku fito a ƙungiyance domin karɓar kukan iyayen da akaima ƴaƴansu fyaɗe. Wannan itace hanya ta farko da zaku iya fahimtar dukkan abinda kukai buri. Sunan ƙungiyarku, lauyoyin da zasu taimaka muku, harma da alƙalai mun tanada, ku naku kawai sauraren duk waɗanda matsalar ta shafa. Baku kaɗai bane a ƙungiyar, akwai matan su Jabeer, dan irin matsalar data faru da ke Nazifa da sister ɗin Ummie data rasu da Amina itace irin hanyar da akabi akaima matar Jabeer fyaɗe kafin aurensu da wasu ƙawayenta biyu data sani”.
        Duk kallonsa sukai cike da ɗunbin mamaki, Nazifa dake sharar hawaye tace, “Yaya kuma suma ba'a gane wanda yay musunba har yanzun?”.
       Cikin tsananin takaici Jay yace, “Ba'a ganeba, hasalima daga ƙarshe a lalace shari'ar ta ƙare tunda babu wasu hujjoji da zasu tabbatar da wanda ya aikata ɗin. Abinda yasa mukai tunanin kufito a ƙungiyancan dan bazai yuwu mu iya gane waɗanda akaima irin wannan kalar fyaɗen ba saita siyasa, suma waɗanda akayima ɗin ta wasu hanyoyi wasu rashin gata ya sakasu sunyi shiru, wasu kuwa sakacin shari'a yasaka zancen wucewa tamkar ba'ayiba. Ku jami'an tsarone shiyyasa muke fatan ƙungiyar da zata fito daga ƙarƙashinku ta banbanta da sauran ƙungiyoyin, mukuma zamu tsaya a bayanku mu baku dukkan gudunmawa ta ɓangaren shari'a dan acanne ake ruguza komi da make ƙwarin gwiwar ƙungiyoyin dake faɗi tashi akan wannan matsalar. Dan haka aikinku zai kasance da manufa biyu....”
            Kasancewar hakan burinsune sai duk suka amsa cike da farin ciki da zumuɗi.
       A nutse Jay ya ƙarayi musu bayani suma su Aliyu suka ƙara musu da nasu.

★★★★★★★

           Ring ɗin wayatane yasa na farka, na buɗe idanuna da ƙyar ina tashi zaune, saman mirror ɗinsa na hango wayar, dan haka na sauka a kan gadon ina cije baki, duk da Alhmdllh naji daɗin jikina bakamar a daren jiya ba da ɗazun da safe, ganin Ummu ce da kanta tai kirana na ɗan zaro ido waje na ɗauki wayar da har ta katse, ina ƙoƙarin kiranta kiran ya ƙara shigowa, cikin ladabi na ɗaga tamkar ina a gabanta na gaisheta Ina hawaye.
     Daga can gimbiya tai murmushi tana gyara kishingiɗar da tayi jikin mai martaba, “Haba ɗiyata, miye kuma abin kukan, baki da lafiyane naji muryarki haka? Ayi haƙuri to, shiyyasa naƙi kiranki ai sai yau, duk kuna lafiya ko?”. Kaina na ɗaga tamkar ina gabanta nace, “Lafiya lau Ummu, barci na tashi ne, sai kaina dake ciwo kaɗan, inasu Safah? Tun jiya naketa zuba idon zuwansu amma shiru”. “kisha magani to, ALLAH ya ƙara sauƙi, Karki damu zasuzo insha ALLAHU, yanzuma na kirakine akan zuwansu Anuwar anjima kaɗan dan zasu wuce gobe idan ALLAH ya kaimu”. Cikin jin daɗi na share hawayena Ina faɗin, “ALLAH ya kawosu lafiya Ummu, to suzonan su kwana dan ALLAH”. “A'a babu batun kwana ɗiyata, ai ba'a kwana gidan amarya, zasuzo dai zuwa dare su dawo, ki tabbatar mijinki da Anuwar sun haɗu dan munyi waya dashi ɗazun yace baya gida”. “Insha ALLAHU Ummu zanyi ƙoƙari”. “To shikenan, sai anjima na kiraki kinji, kidage da shiga ruwan zafi karkiyi son jiki”. Kunyace ta kamani, a raina ina tunanin kodai shine ya sanar mata..... “Kina jina” magarta ta maidoni hankalina. “Eh Ummu”. “Bawai ina nufin ki shiga ruwan zafi idan babu abinda ya faru ba, tunda nasan kina fashin salla, bakuma saina buɗe miki abinda nake nufiba, ayita haƙuri danshi zaman aure haƙurine, allah yay miki albarka”. Hawayena na share nace, “Amin Ummu nagode”.
           Rashin ganinsa a ɗakin ya sakani jin daɗi bayan na ajiye wayar, cikin dauriya na gyara ɗakin tsaf, na fito ɗaukar kayan shara naga Nabeelah, sosai naji daɗin ganin nata, itace tace nabar sharar ita zatayi, ban musa mataba na shiga nai wanka da sake gasa jikina sosai, hakan ba karamin nutsuwa ya ƙaraminba. Koda na fito saina koma ɗakina nai shiri, ina cikin shirin Nabeel

ah ta kawomin abinci, dan tunda taga yanayina ta tambayeni lafiya nace mata banida lafiya duk sai naga jikinta yayi sanyi. Yunwa nakeji sosai shiyyasa na zauna naci abincin. ɗakinsa na sake komawa ɗaukar maganin dan naji daɗinsa, ina buɗe box ɗinne Nabeelah ta shigo da sallama da waya a hannu, a kunne kawai ta sakamin batare da tayi maganaba. Ɗagowa nai zan tambayeta wanene? Muryarsa ta shiga dodon kunnena.
       Saida na lumshe idanu na buɗe sannan na amsa masa sallamar tasa,
          “Amarsu kin tashi?”. Ya faɗa cikin zolaya.
       Jinai tamkar na nutse dan kunya, dukda bana gabansa, nai saurin saka hannuna na rufe fuskata ina murmushi da faɗin, “Nidai ALLAH a'a”. Ina jiyo sautin murmushinsa shima, yace, “Nidai nasan amaryata amaryace ƴar gaske, yaya jikin naki?”. Batare dana buɗe fuskarba nace, “Da sauƙi”. “Alhmdllh ai haka akeso, kinci abinci ko?”.
     “Uhm naci”.
  “Tom kisha magani ki sake kwanciya ki huta karki biyema surutun Nabeelah, Gimbiya ta kirani akan baƙi zasuzo kuyi sallama, zanyi ƙoƙari na dawo da wuri nima insha ALLAH. ga Sadiq nan zai kawo cefane Nabeelah tayi girki”.
        “ALLAH ya dawo dakai lafiya to”.
“To nagode, amma mizan ɗan samune Noor-Jahan?”. A marairaice nace, “Mi kake so?”. yace, “Komai aka bani inaso mana”. Duk da ina tsananin jin kunya nace, “To rufe idonka”. “Na rufe ruf Matar Jay”. Yay maganar cikin sanyin murya kamar ba shiba.  da saurin na yanke kiran ina dariya, ina gani ya sake kira naƙi ɗagawa, saima maganin na ɗauka na fita falo wajen Nabeelah.
Chapter 103 · 0% Book details