← Book details Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 168

Sashe 121

Kwai Cikin Kaya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da muka gama shirin barci muka kwanta, ina jikinsa a lafe kamar wata mage yana shafa bayana a hankali, fitar numfashinmu yana dai-daitane da sautin bugun zuciyarmu, “Miema kinyi barci?” ya faɗa a hankali cikin kunne na. Kaina na girgiza masa da ɗago fuskata dake cikin ƙirjinsa na kalli fuskarsa, shima kallona yakeyi. Murmushi mukaima juna, ya ɗan sumbaci goshina kafin ya sake maida idanunsa cikin nawa. Maida nawa nai na lumshe dan nakasa jurar cigaba da kallon cikin idanun nasa. Baice komaiba sai sake turani da yay jikinsa ya rungume da ƙyau. A haka barci yay awon gaba damu.
★★★★★★★
Mun cigaba da kasancewa a cikin Saudia tare dasu Umm-Anum cike da tsaftatacciyar soyayya da tarin ƙauna mai daraja daga garesu, tattalinmu take tamkar wasu ƙananun yara ni da boss, yayinda a koda yaushe ƙannensa ke nane da shi, yanayin waya sosai dasu Oga Hafiz musamman akan aikin da a yanzu mukasa gaba na ƴan fyaɗe, a yanzu haka dai su Jabeer suna ƙoƙarin miƙa wasu samari kusan goma sha uku kotu akan case ɗin fyaɗen, sannan sunce sun samu case huɗu masu kamanceceniya da nasu Amina. Duk da muna nan saudia muma aikin mukeyi musamman ma boss, danni wataranma A wajen Umm-Anum nake yini komu tafi makarantarta. Har gidan Uwargidanta an kaimu, abin ya birgeni sosai yanda aka tarbemu tamkar ba kishiyoyi ba, a raina nace ‘kaga inda ake kishin ilimi, ba irin na ƴan ƙasarmu ba na hauka’.
Randa muka cika kwanaki bakwai a saudiya boss ya fara samun kira daga wajen aiki, dan mun wuce ƙa'idar kwanakin da aka bamu na hutu, duk yanda yake da son aiki da ƙwazo saina fahimci bayason komawa yanzun, nima dai bason komawar nakeba sam, amma yaya zamuyi hakan tilasne a garemu kodan ɗunbin ayyukan da muka baro.
A ranar yayma Umm-Anum magana akan binmu, sai dai abin mamaki da al'ajabi a take ta nuna ɓacin ranta akan bazataje ba, shiru mukai kawai duk muna kallonta, yayinda fuskar Boss da Anuwar ta nuna tsantsar ɓacin rai akan hakan. Kafin suce wani abu akan hakan Abbu yaja hannunsu suka fice daga gidanma gaba ɗaya.
Wannan al'amari ya tsaya min a zuciya, dan yinin ranar gaba ɗaya wuni Umm-Anum tai cikin ɓacin rai, yayinda na yini nikuma cikin nazarin komai da fashin baƙi a kai.
★•°•★°•°★•°•★°•°★•°•★
A ɓangare su Jawaad suna fita daga nan wucewa Abbu yay dasu masaukin takawa, tattaunawa suka shigayi game da abubuwa masu dama, Abbu yace, “kuyi haƙuri kubar ɓacin rai kunji, itama ba laifinta bane, babu yanda za'ai taƙi son zuwa ƙasarta kodan shekarun data ɗauka bata cikinta, al'amarin bai baku mamakiba yanda har yanzu bata iya tambayar kowa daga ahalin nata ba, tunfa washe garin zuwanku har yanzu bamu sake zaman tattauna komaiba, tama ƙi ƙara nuna tana buƙatar jin komai, hatta da yanda ka rayuwu bayan barinta gida bata tambayeka ba Jawaad. Wannan babban al'amarine daya dace ace an zauna anyi dogon nazari a kansa. Shi sihiri a jikin ɗan adam abune mai wahalar yakicewa, musamman irin nata da ba'asan dalilinsa ba ma da sarƙaƙiyar sa, shifa mai sihiri baya gajiyawa da ƙoƙarin ɗaura wani akan wani, dan ya riga yayi imani da yin wannan shirkar itace ƙarfin ikonsa, har yanzu akwai sihiri tattare da mahaifiyarku, wanda inaji a raina akwai wani abu da aka binne wanda saimun tonosane komai dake jikinta zai iya warwarewa harmu fuskanci matsalar gaba ɗaya, bakuma wai dan addu'oin da muke basa ƙarɓuwa bane, ita rahamar UBANGIJI da kariyarsa bata taɓa gushewa ga wanda ya dogara da shi kuma yayi imani ya riƙe gaskiya, gaskiyar ɗan adam bata taɓa ƙarewa sai dai ace ƙaryar wane ta ƙare, dan haka mucigaba da bin komai mataki-mataki insha ALLAHU komai zai zama labari ne, Jawaad idan babu damuwa ka bamu haske dangane da family ɗinku ko zamu samu wani haske”.
Duk sun gamsu da maganar Abbu, dan haka Jay ya shiga basu tarihin rayuwar mahaifinsa da Umm-Anum kamar yanda kakarsa mama maryam ta shaida masa komai bata ɓoye masa ba. Ya cigaba da faɗin, “Ban taɓa zargin kowa a zuri'ata game da iyayena ba, dan babu wani alamun cutarwa dana taɓaji ya shiga tsakaninsu da mahaifina harya bar duniya, sai dai maganar gaskiya lalurar hauka da Ummuna ta gamu da shi a ranar rasuwarsa abin tambaya ce, ada ban taɓa ɗaukar hakan komaiba sai kwanannan da matata tai wata magana data kasa barin raina, na cewar a al'amarin Ummuna akwai alamomin sihiri, dan mutuwar Abba bai kai ace ta kasa jure ƙaddara ba har ta kaita da ciwon hauka, ciwo ma irin wanda mutum baison zaman gida, bayan duk musulmi yasan mutuwa wajibine ga mai rai. Abinda kuma naji daga gareku a yau da wanda ya faru ranar ya tabbatar min akwai abinda bamu saniba dake a ɓoye tabbas”.
Abbu ne ya sauke ajiyar zuciya yana gyara zamansa, yace, “Tabbas kamar yanda ka faɗa Muhammad akwai ababen tambaya masu yawan gaske akan al'amarin, ko sunanta sai a jiya na taɓaji, kai tsaye bamu da damar zarigin kowa akan wannan al'amarin, musamman idan mukai dubu da marigayi yayi shugabanci na ƙasa, ƙasarma babba irin taku, bazai yuwu ace baida maƙiyaba koda kuwa suna a kusa da shine. Sihiri gaskiyane, hakama addu'a waraka ce, sai dai wani lokacin sai kaga kamar ka ɗauki lokaci kana addu'ar babu biyan buƙata, ba haka bane, UBANGIJI maijin kukanmune a koda yaushe, mai kuma magance mana damuwarmu ne a koda yaushe, wani lokacin ita addu'a idan kayita takan jinkirta da ga abinda ka roƙo a kansa, saita zama kariyane ga wani al'amarinka ɓoyayye da kai kanka baka san da shi ba, mahaifiyarku ta jima cikin wani hali na jarabawa, mun kuma ɗauki lokaci muna gayama UBANGIJI, bamu taɓajin mun ƙosa ba, domin mun tabbatar shi kaɗaine mai badawa, yana jinmu, kuma yana ganinmu, yana kuma sane damu, jinkirtawar warwarewar komai ba yana nufin bai karɓi kukanmu ba. a yanda kuma nakeji a raina addu'armu ta kasance da kai, kai kanka, dan duk waɗanda suka iya tauyeta kaima abune mai sauƙi su ɓaddaka, inaga damuwa akan saita biku ba shine ya kamata ba, bincike akan ainahin miya faru shine ya dace domin mu samu bakin zaren, dan ko Anuwar bai kamata ya biku ba”.
Kallon Abbu Anuwar yayi cikin tsagwaron tashin hankali, kafin yace wani abu Takawa yace, “Wannan tunanin shine a raina nima Abu-Sufyan, Anuwar kayi haƙuri kaji, indai ƙasarmu ce zakaje ka rayu har saika gaji ma, amma ba a irin wannan lokacin ya dace ba, dan abubuwa da yawan gaske na zuwarmin a zuciya game da al'amarin nan, sai dai banason furta komai nafison matsayin Jawaad na jami'in tsaro shi yay wannan tunani, zuwan Umm-Anum da Anuwar ba shine abu mai muhimmanci ba a yanzu ƙwarai da gaske, dan komai ma zai iya faruwa inhar azzaluman da suka ƙulla al'amarin suna tare dasu ne, kai koma nesa da su suke suna bibiyar al'amarin komai dan nima nayi makamancin wannan rayuwar nasan sarƙaƙiyar cikinta, amma kai Jawaad minene a ranka?”.
Zama Jawaad ya gyara cike da kaifin basirar da ALLAH ya azurtashi da ita shima yace, “Na gamsu da duk abinda kuka faɗa, dan nima a kwanakin nan sune suka zama abin nazarina, rashin tambaya ta komai da Ummuna batai ba yafi komai tsayawa a raina sosai, ni a yanzu shirina na farko shine lallaɓata naji waɗanda sukai rayuwa dasu kamar ma'aikatan gidan da sauransu”.
“Tunani mai ƙyau” cewar Takawa da Abu-Siddiq. Jawaad ya cigaba da faɗin, “Sai abokai makusanta da Abbah ya rayu da su kafin shigarsa siyasa da hawansa mulki, abu na uku ne bamu da dama a kansa, dan a wajen Ummuna ne kawai zamu iya jin wasu sirrika game da rayuwar Abba da ƴan uwansa a lokacin da yake mulki, dan haka wannan na ajiyesa gefe zanyi anfani da waɗancan damar guda biyu mugani ko za'a dace, amma nima na gamsu da basai sun bimu ɗinba kam yanzun”.
“ALLAH yay maka albarka” cewar Abbu yana dafa kafaɗar Jawaad dake a kusa da shi. A tare suka amsa da amin. Abbu ya cigaba da faɗin, “Nima nanda sati guda zan biyo bayanku dan inason ganawa da Abba (Alhaji Babba). Kai Jawaad ya jinjina masa yana ɗan murmushi da faɗin, “ALLAH ya tabbatar Abbu”. Da Amin duk suka amsa..
Akan wannan shawarar taron ya tsashi, shi dai Anuwar badan yasoba ya haƙura akan binsu Jawaad, dan yay masifar ƙwallafa ransa da zumuɗin son ganin ahalinsu.
★★★★★★★★
Cikin hikima Abbu ya samo sunayen ma'aikatan da su Umm-Anum sukai rayuwa dasu a gidan gwamnati da kafin hakan, harma da sunayen abokan Abban Jawaad ɗin data iya tunawa da ƙyar.
Sai kuma ta nema tada hankalinta akan komawar su Jawaad ɗin, ta kafe akan ita bazata barsu su koma ko inaba sunzo kenan. Duk yanda Jawaad dake cikin damuwa shima yake ƙoƙarin mata bayani akan aikinsu da buƙatarsu da akeyi taƙi fahimta, tamaƙi sauraren komai, saima ta saka masa kuka daga ƙarshe. Wannan abu ya sake tada hankalin Jawaad sosai, dama dauriya kawai yakeyi. Da ƙyar aka shawo kanta da lallashi akan Jawaad da Bilkisu zasuje su ajiye aikinsu ne su dawo nan da zama gaba ɗaya wajenta.
Wannan batu ya sakata yarda, amma sunsha gargaɗi akan karsu daɗe basu dawo ba, dan da farko ma catai Jawaad yaje shi kaɗai yabar bilkisu ita anan, sai da Abbu ya sake wata sabuwar dabarar ya lallaɓata sannan tadai barsu suje ɗin, sukuma dawo akan lokaci kamar yanda ta faɗa, inba hakaba zata aika a ɗakkosu koda basu gama shiryawaba.
Da wannan yarjejeniya daba tabbatacciya ba muka baro ƙasar saudia cike da kewa ni da boss. su Ummu kam can muka barosu dansu sati biyu zasuyi.
Saukar yamma mukayi ƙasarmu ta haihuwa, inda muka iske Sadiq yazo tarbarmu, dan shikaɗai yasan da dawowar tamu, dama tunda muka tafi boss bai yarda munyi waya da kowaba bayan su oga Aliyu, su Ummah duk yaƙi yarda yay waya da su, dan baiso suji komai da wuri harsu kasa daurewa su sanarma Alhaji babba, a yanzunma da muka dawo bazai faɗa musu komaiba gudun matsala.............✍

Asha sauran weekend lafiya🤒😣🚶🏻🚴🏼
Chapter 121 · 0% Book details