← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 100

Sashe 99

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        “ Yasmeen ? Ihun me naji kınayı ?” Gabaki d’ayansu zaro ido sukai ganin wata matsalar tana ‘ko’karin afkuwa tun basu shirya ba , a guje Baby tayi wata hanyar , suma ba shiri su Eshaal suka bita duk da basusan hanyar da suka biba dan sun tabbata idan suka fita a haka za’a ganesu. Hajiya Sa’adatu ce ta shigo falourn itama sanye da kanyan bacci , mama kine ya kamata ganin Yasmeen a kwance duk a tunaninta bacci ne ya d’auki Yasmeen , shiyasa ta ja ‘karamun tsaki tana miki “ ke dai kam Yasmeen ban san lokacin da zaki girma ba , kamar wata ‘karamar yarınya ki kwanta a ‘kasa ? Ynzu Ina tashinki zaki katsemun jin dad’i na gwara na barki kawai, danni yunwa nake ji “ zaro idanuwa su Fanan sukai dan suma cikin kitchen d’in suka shigo kamar zasu shige dinning ai Fanan ta ga ‘kofar fita daga kitchen d’in , cikin Sauri ta bud’e ’kofar suka fita , suna rufeta ita kuma Hajiya Sa’adatu ma shigowa kitchen d’in. Kazar da ta zo d’auka ta d’auka a öpen zata juya taga kamar haske ya d’an haske kitchen din , kallan saitin inda hasken ya fito tayi , mamaki ne ya kamata ganin kamar ‘kofar kitchen d’in nasu a bud’e “ Wanene ya bud’e ’kofar nan?” Cewar Hajiya Sa’adatu , nan ma ganin kamar za’a Ina kamasu Baby ta ja hannunsu suka zagaya ta baya duk da ba wani haskene da yawa a Wajan , suna zagayawa Hajiya Sa’adatu ta bud’e ‘kofar , ganin babu kowa a Wajan yasa ta kulle ‘kofar tare da shashantar da zancan. 
        Ajiyar zuciya Eshaal ta sauke “ Wana bala’in ne ya kawo mun nan part d’in ? Kinga dare yayi , for now mu ha’kura kar by mistake Mamy ta le’ka d’akin mu taga bama Wajan ko kuma wani yashiga by mistake kunga zamu iya shiga matsala dan dole zasu bincike mu, gabaki d’aya sun yadda da maganar ta shiyasa babu Wanda yayi musu a cikin su, suka soma bi ta Wajan , Allah ya temakesu basu ga kowa ba , har zasu wuce wata shuka Baby tayi saurin dakatawa tana kallan shukar sosai , ganin ta dakata da tafiyar da take ne Fanan ta furta “ Me kike kalla haka ?” Baby bata kula taba sai jakar hannunta da ta bud’e , wu’kar da suka zo da ita ta d’auka cikin Sauri ta nufi shukar, Eshaal ce tayi saurin ri’ke mata hannu “ Me kike ‘ko’karin yi?” Fusge hannunta Baby tayi tana ‘kara kusantar flower “ Tabbas ita nake gani “ ta fad’a a hankali , bata tsaya ‘bata lokaci ba ta hankad’a flower ta fad’i ta fashe , cikin Sauri Baby ta soma dudduba cikin ‘kasar flower , bakinta d’auke da Bismilla ta saka hannunta a ciki tare da janyo abunta batasan komene ne ba , wani irin taji a hannunta kamar wacce aka caka amma duk da hakan ai da ta janyo abunda ta d’am’ka da mugun ‘karfi , wanda yayi sanadin girgiza zukatan mutanene da dama , a guje Baby ta furta “ mu güdü nayi motsi “ bashiri sukace ‘kafa mai naci banbaki ba , a guje suka saka güdü tare da barin Wajan. Suna tafiya wannan flower ta ‘bace gabaki d’ayanta . Ta kitchen suka shiga part d’insu Allah ya taimakesu babu wanda suka gani a part d’in, cikin sand’a sukayi saurin shigewa d’aki suna sakin ajiyar zuciya . Baby bata zauna a d’akın ba ta Shiga toilet abun da ta d’auka ta kalla tare da wanke wa , abun mamaki mukulli ne sai ‘karamar bishiyar da ta nanna d’eta , Baby batayi Tuna’nın komai ba ta wanke ‘kasar wajan tare da fitowa daga toilets d’in, tana fitowa Eshaal ta shiga toilet d’in lokacin Fanan ta fita kitchen samo musu wani abun, kallan abun hannunta Baby tayi bakinta d’auke da Bismillah ta dunga tsitstsige abun bushiyar da ta gani duk da bata da tabbacin ko mai nene, sai da ta cire ta tsaf haka kawai taji tana san bud’e mullin, tana murd’awa kamar wacce aka ja sai ji tayi ta fad’i ’kasa , a tsorace ta bud’e kwad’an jin kamar jikinta yana karkarwa tayi saurin bud’e bedside drawer d’insu ta saka kwad’an a ciki,lokaci d’aya taji jikinta ya dena yi mata rawa ga wani irin bacci da ta soma ji, addua kawar tayi Batare da ta jira su Fanan ba tayi wanciyarta cikin mıntunan da basu wuce d’aya ba bacci ya d’auketa. Fanan tana shigowa ta tarar da Baby tayi bacci , har zata tasheta sai kuma ta ‘kyaleta, Eshaal da ta fitoma sosai tayi mamakin baccin Baby da wari, basu yi wani hira sosai ba , suka ci abunda Fanan ta d’auko musu kafun su kwanta . Gabaki d’aya su bacci na d’aukarsu wani irin jijjiga d’akin ya somayi kamar ginin d’akin zai fad’a , abun mamakin kuma ko juyi su Baby basuyi ba baccinsu suke hankali kwance , wata irin halitta ce ta bayyana a cikin d’akin mai girgitarwar gaske jikinta kamar bushiya ga alamar ciwo gabaki d’aya a jikin ta , kansu Baby tayi gadan gadan, amma data nufesu sai taji kamar ana ‘kona mata jiki, wani irin girgiza ta sakeyi kamar zata ta’ba su , azabban zafin da tajine yasa ta d’an saki ‘kara tare da janbaya, maida kallanta kan bedside d’in da Baby ta saka mukullun nan tayi, tana ta’bawa hannunta ya ‘kone , cikin Sauri ta baya tare da ‘kara ta’ba a wannan karan gefen fuskarta ne ya ‘kone a haukace Sabida a zaban zafin da taji yasa ta bangaji bed side , lokaci d’aya cikinta ya soma karkarwa , wani irin huta ta soma ci a jikinta , yadda wutar nan take ci mutum sai yayi tunanin gabaki d’aya d’akin ne zai ‘kone amma ko kusa babu abunda wutar nan ta ta’ba sai wannan halittar da take ‘konewa duk irin kururuwan da take babu wanda zai iya jinta . Abunda bata sani ba mukullin da Baby ta ajje a gefen alqur’ani ta ajjesa shiysa duk lokacin da halittar nan taso ta’ba abun take ji zafi, dalilin da yasa ta soma ci da wuta kuwa hankad’a bed side din da tayi ne yasa mukullun ya ta’ba alkurani , wanda hakan ba ‘karamun buga zuciya yayi ba , tun abun na ci da wuta har ya cinye gabaki d’ayansa , wani irin Sautin taşs ya cika d’akin kafin abun ya ‘kone baki’kine wani irin wari na fita cikin seconds din da basu wuce 50 komai ya ‘bace hatta mukullin da Baby ta d’auko Wanda sautin ‘karar konewar nan saida Abbu da yake sallah ya dafe saitin zuciyarsa a Daidai lokacin da wani ba’ki haya’ki yake fitowa daga cikin part d’in , cikin tsananin rud’u da juyewar tunani komai yake tafiya musamman da akace rashin sani yafi dare duhu, amma wani rashin sanin Al’kairi ne kamar yadda yazo wa ahalin nan , kamar yadda Baby ta bud’e mukullinta bayan ta tsige bishiyar jiki hakan ne ya zama mahad’i ga ‘boyayyan ahalin ta yadda tsarkakekken jini ya had’u waje d’aya , a halin da ba’kin jini yake ‘ko’karin tarwatsawa, shine ya sake had’u, kamar yadda suka gojewa had’uwar taurari biyar, cikin rashin sani taurarin nan suka haska ko ina , jini da jini yana ‘ko’karin bayyana alokacin da aka samar da wani tsarkakekken jini mai ‘Kona ba’kin jini da girgiza zuciyoyin wasu.

*************
PRISON

A lokacin da Nani take wani irin ‘baccin wahala a lokacin ta soma jin kamar ana mata d’an kira a kunne , ‘kara kiran sunanta da akai ne yasa ta farka a firgice amaimakon sunanta ya ambaci tsarkakakke abun tsarkakewa sai bakinta ya buge da anbatan shed’anin bokanta sindilu. Shid’inne ya bayayyana a gabanta , sabida razani Nani sai da ta ja baya gabanta na dukan uku uku, shima Sindilu ita ya soma bi da idanuwansa da suka rine zuwa ja , kamar wanda aka sha’kewa ma’kogaro ya furta “ kinyin şaken da guguwa ta tashi alokacin da ba’a mu’katarta , jinin da nake gudun had’uwa suna dafff da had’uwa kamar yadda nayi hasashen bayyanar jini, cikin rashin sani taurarin da nake san dakushewa süne suka karya duk wani abun jin dad’i na , cikin ‘kan’kanin lokacin an karyamun ko wana ikona a cikin ‘yan da’ki ‘ka zan koma asalin halitta da aka Mayar dani, kamar yadda ‘karshena yazo ba tare da sani ba kema
‘Karshen ki yana kusu ba tare da kin fargaba, lokaci na ya ‘kare , ta bud’e kwad’an da ya kulle jinin su , bud’ewarsu kuma shine rugujewar tamu rayuwar, “ Sindilu ya ‘karasa yana wani irin abu, itama Nani tsumar zaune tayi kamar wacce zuciyarta take ‘ko’karin bugawa , wani irin ba’kin jinine ya soma fitowa Sindilu, kamar wani zautaccen mahaukaci haka ya dunga wasu irin abubuwa mai firgitarwa da buga zuciyar mai imani, gabaki d’aya abun sai ya koma na Al’ajabi, yadda Sindilu yake abu sai ya girgixa zuciyar me imani ya ‘kara sakawa zuciyarsa tsoran Allah, cikin mintuna kad’an Jikin Sindilu ya soma d’ayewa kamar wanda ake watsawa tafashash shen ruwan zafi, kamannunsa suka ji gaba da rikid’a zuwa suffar gizo gizo ,Ba a ‘kara minti biyu ba ya fashe tare da ko mawa wani irin bakin haya’ki , yana komawa kuma wannan ba’kin haya’kin ya shige idanuwan Nani da ya zamo babban nakasu a rayuwarta ta har abada , kifewa Nani tayi a wajan kamar wacce zuciyarta ta buga dan ko nunfashi batayi. 

       Ko wana azzalumi akwai ranar sakayya kamar yadda Sindilu duk ‘karfin tsafin tsafin sa ya koma ‘karamar halitta cikin ‘kudurar ubangiji, irin halittar da yaro ‘karamı xai take ta . Duk zalincin sa da tsafin sa ya kasa ku’butar da kansa daga kalar azababbiyar azabar da yasha , kafun yace wajen mai hisabi. Wanda ko wannan sassa zai fad’i abunda ya aikata bayan ka tafi da littafinka a tafin hannunka. 

ALLAH KATSAREMU DA MASUSAN GANİN BAYAN MU
    ALLAH KARKA BARMU DA IYAWARMU KA NESANTAMU DAGA AZZALUMAN BAYINKA , KA KARE MU DA FA’DAWA HALAKA

  ✨✨✨✨✨✨✨✨

UNITED STATE 
Chapter 99 · 0% Book details