← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 100

Sashe 98

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Hannunta ya kama suka shiga cikin building d’in , gabaki d’aya an ‘kawata falourn sama da harsashen mai har sashen , dan sosai falourn yayi bala’in yin kyau fiye da yadda suka barshi, dan fad’ar irin ‘kawatuwansa ma ‘bata lokaci ne , basu zauna a falourn ba ya jata zuwa part d’insa , nan ma sosai part d’in Big Boss ya canza kamar ba shi ba , ganin yadda take tafiya a hankali ne yasa ya d’auketa gabaki d’aya zuwa bedroom d’insa , yana zaunar da Ita akan sofa ta zame zata kwanta ya hanata “ Kin gaji ko?” Kanta Abla ta jinjina kawai tana jin gida da sofan “ Bari kiyi wanka kici abinci , sai ki huta kinji”, kanta Abla ta girgiza masa “ zanyi anjima”, shima kansa ya girgixa yana shafa gefen face d’inta “ No Dear , just wait for me , am coming “, ya fad’a yana nufar d’akin dressing room d’insa .

    Bai d’auki dogon lokaci ba ya fito , cikin ‘kan’kanin lokaci sukayi wanka, tare da cin abinci duk da Abla da ‘kyar ta yadda ta ci abincin , sallolin da yake kansu suka soma ramawa , ana idar wa Abla ta zame zata kwanta ya ‘dauketa zuwa kan bed , “ Am sorry Momyn Unborn , yanzu zamuyi bacci , shima unborn yayi ha’kuri yanzu zamuyi bacci , okay ?”, idanuwan Abla a lumshe ta jin jina masa kai , ko da suka kwanta bata d’auki mintuna biyu ba bacci ya d’auketa.

***********
      NIGERIA***

Su Baby suna zaune a d’akin wayar Eshaal ta soma ringing , kallan wayar dake hannunta tayi duk da batayi saving number ba ta gane me kiran, gabaki d’aya sai ta kasa d’auka “ Dallah ki d’auka “, cewar Baby dake hararan ta , ajiyar zuciya Eshaal ta d’auka , “ ki bari kawai bazan iya ba “, cikin Sauri Baby ta katseta “ bazaki iya me ba ? Kiran ? Wallahi tun wuri bazaku bayar dani ba , kina mace kice bazaki  iya d’auka ba ?” Ta fad’a tana fusge wayar hannun Eshaal, tun kafun tayi wani yun’kuri  Baby tayi answering called d’in da ya sake shigowa tare da mi’ka mata wayar , harararta Eshaal tayi tare da runtse idanuwa tana kare wayar akunnanta , bansan mai aka ce mata ba , sai “ Tohm” kawai tace tana kashe kiran . “ Baby mai yasa zakiyi picking called d’in ?” Hararar ta Baby tayi “ ke kika sani wallahi babu kyau dai wula’kanci, Allah ya baki daga sama gasash she kina wani jin kunya , ki bari duk lokacin da wata tayi wufff dashi zakiyi bayani musamman yadda naga yan matan gidan nan kullum cikin kallan su suke , barin wannan mai şiffar ‘kanjaman ( Harry)”, yanxu me yace miki?” Ajiyar zuciya Eshaal tayi “ kirana yake “, cikin Sauri Baby ta furta “ ki sauri ki kije karki barsa ya dunga jiranki, kin manta yau zamu fara plan A?”, Fanan da ke gefen ta da tun d’azu batayi magana ba ta furta “ Yes ya kamata muyi komai cikin lokacin da muka samu kafun lokaci ya ‘küre mana ,” da haka suka samu suka lalla’ba Eshaal har ta ‘kimtsa.  

       Ko da ta fito falourn batayi Tuna’nın zata same sa anan ba shiyasa tayi saurin dakatawa daga tafiyar da take tana sunkuyar da kanta, Bobo da yake sanye cikin wasu top din ‘kananan kayane yayi murmushi kad’an “ ki ‘karaso mana “ ya fad’a yana ‘Kara binta da kallo , Eshaal bata kuma d’ago fuskarta ba ta ‘karaso cikin falourn , akan 2 sitter ta zauna ba tare da ta kallesa ba ta gaishe sa , shiru Bobo yayi mata , hakan ne yasa ta d’ago idanuwanta , karaf ya shiga cikin nasa , da Sauri Eshaal ta saka hannu tana ‘boye fuskarta sabida wani irin kunya da ya kamata , Bobo kuwa tashi yayi daga kan kujerar da take ya zauna a tata “ Amincin Allah su tabbata ga Mrs Bobo,” yanxu ma murmushi Eshaal tayi ba tare da ta bari sun sake had’a ido ba , cikin siririyar muryarta ta furta “ Kai ma haka “, d’an rankafowa Bobo yayi kamar bai fahimci me take nufi ba yace” Nima me ? “ ganin yadda take ‘boye face d’inta yasa Bobo ya furta “ please duk lokacin da suke tare ki dena ‘boyen fuskar ki , kinji? Or you don’t like chatting with me ?” A hankali Eshaal ta girgiza masa kanta alamar “ ah’ah “ then removed your hand “, ba musu kuwa Eshaal ta zame hannun nata , “ I understand, baki saba magana da ni ba , but from now on you will get used to it, Dan matar soja , soja ce , am going somewhere, but I wanted to see your face  first , shiyasa nazo, yanzu an bani izini na tafi ?” Kanta Eshaal ta Jinjina masa alamar eh , “ ba kyasan zama na kenan ? Korata kike ?”, kanta Eshaal ta girgixa masa “ No kace zakaje wani waje ne that’s why “, hmmm kawai Bobo yace yana ‘ko’karin mi’kewa “ it’s okay tunda Mrs Bobo bata bu’kata ta , am going “, kwalla ta ce taji tana ‘ko’karin taran mata a ido a rayuwa babu abunda ta tsana kamar a wula’kanta wani shiyasa taji kamar shima hakan tayi masa “Kayi hakuri “ cewar Eshaal tana kulle idanuwanta sabida hawayen da taji yana san sakko mata , cikin Sauri Bobo ya zauna a gefen ta “ Subhanallahi, Love why zakiyi kuka ? Stop it please Nima in ba so kike nayi miki kukan ba “, göğe hawayenta Eshaal tayi da handkerchief d’in da ya mi’ka mata “ Now tell me , Ni na ‘bata miki rai ko ?” Kanta Eshaal ta jinjina masa , cikin Sauri ya zaro eyes d’in , “ Bakaine kace zaka tafi ba ?” Ta fad’a tana sunkuyar da kanta ‘kasa , murmushin da Bobo yayi me sauti ne yasa ta sauke ajiyar zuciya , that’s why kikeso kiyi mun asarar precious hawayen tun kafun lokacin fitar su yayi ?” Eshaal bata gane me yake nufi ba sai kanta da ta jinjina masa , Bobo kamar wani yaro ya kama kunnensa guda biyu “ shikenan Am sorry Love , ko sai an samo bulala kin mun ?” Murmushi Eshaal tayi jin abun da yace , bai fitan ba sai janta da ya somayi da hira , tun tana nonno’kewa har ta soma sakin jikinta tana basa amsa , daman shima hakan yake so shiyasa ya zage yana mata hıra, bashi ya bar falourn ba sai da ya tabbatar ta sake dashi sosai , duk da hakan kuma bai ‘kyaletan ba acewar sa zasuyi waya anjima . 

       Eshaal tana komawa d’aki taga gabaki d’aya sun canza kayansu zuwa ba’ka’ke , kallan su tayi cikin Sauri Baby ta furta “ Mrs Love bamu da lokaci ki sauri kishirya. Cikin Sauri Eshaal ta shirya cikin ba’ka’ken kayansu , ko wannen su da face mask a hannunsu duk da basu saka ba , gudun kar sojojin su d’auka wasu ne daban su jibgesu shiyasa suka ri’ke a hannu, ko wannan su da waya a hannun sa , sai wasu jaka da suka d’auka yar ‘karama ki wannansu da ‘karamar wu’ka a ciki. Fanan ce ta soma duba falour ta tabbatar da babu wanda zai fito tukunna suka fito kamar wasu munafukai. Allah ya taimakesu ma sojojine kawai a falourn , daman fargabarsu karsu had’u dasu Bobo ko su Little , cikin ikon Allah kuwa basu tarar da ko d’aya a ciki ba . Su kansu basu san me zasu farayi ba duk da binciken da suke so suyi ga kowa na gidan shine plan A d’insu . Part d’in da yake d’an nesa da nasu Suka nufa musamman da suka ga anrage hasken wajan ba kamar na part d’insu ba . 

       Kallan sojojin wajan sukayi tsafff kamar masu shirin shiga part d’in, gudun kar Sojojin su zargesu kawai suka shiga part d’in , suna shiga kuwa suka soma jin taku kamar ana shirin shigowa falourn , kamar wasu tsuntsaye sukai realle zuwa bayan kujerar wajan , Baby da tafi kowa neman rigima sai da ta le’ka dan ganin ko wanene ya fito , Yasmeen ce ta fito cikin shigar kayan baccinta da alama ruwa ta zo d’auka, shi d’in kuwa ta d’auka har ta soma tafiya taji kamar motsi, a tsorace ta furta “ wanene a nan wajan ?” Waro idanuwansu su Baby sukai ganin tana ‘ko’karin tona musu asiri, cikin Sauri Baby ta bud’e bağ  d’inta tare da ciro farar powder din da suka d’auka , gabaki d’aya ta zazzaga a fuskarta , “ Nace wane ne a wajan nan “ cewar Yasmeen da ta ‘kara magana , cikin Sauri Baby ta shash shafa kwalli a fuskarta tare da cire d’an kwarin kanta , dogon gashin kanta black colour ya fito duk da yadda ta gyara kanta sai da ta batashi tare da zubo shi har göshinta, bansan mai ta rad’a musu ba sai gani nayi tana suna jinjinq mata kai , matso Wanjan da Yasmeen take ne yasa Baby yin tsalle tare da tura a gabanta , cikin matsananciyar tsorata kuwa Yasmeen ta ‘kwalla ‘kara itama Baby bakinta ta bud’e mata lokaci d’aya hakwaranta da ta sakawa ba’ki suka fito , idanuwanta Baby ta soma warowa Yasmeen tana wani jijjiga kamar me aljanu, babu shiri Yasmeen ta fad’i ’kasa sumammiya gabaki d’ayan su dariya ce ta kamasu sai a lokacin suka fahimci part d’in Hajiya Sa’adatu suka shigo. 
Chapter 98 · 0% Book details