Sashe 21
Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
‘Karfe 2:15pm Abla na zaune a cikin d’akin ta ,yau gabaki d’aya bata cikin mood hatta face d’in ta sai da ya nuna hakan duk da ba’a d’aure take ba kuma ba a sake take ba ga abincin ta da yake kan table ko ta’bawa batayi ba , tun tana game a cikin wayar har ta gaji ta ajje ta , hakanan take jin ranta a ‘bace shiyasa ta fasa zama akan gadon ta kwanta a kan lallausan carfet d’in d’akin, jikin ta sanye cikin wani light brown d’in wando da ya yazo mata Daidai gwiwar‘kafarta sai santala santala ‘kafafunta da suka futo fess da su , rigar jikin ta fara ce me kama da armless sosai ta kama jikinta sai d’an ado adon flowers brown da yake cikin rigar , yau ko d’an kwali bata saka ba musamman yadda tsawan gashin ta ya dawo na ban mamaki dan har ya wuce Wanda Big Boss ya yanke mata , yadda ta takure waje d’aya sai kace me jin sanyi ‘karar bud’e ’kofar da akai ne ta d’an bud’e idanuwanta da ta kulle , sanye yake cikin wani black d’in wandon Bottega veneta sai rigar jikinsa da ta kasance milk colour , sosai kayan suka yi masa kyau kamar dan shi aka yi , gyaran gashin kansa ba’karamun kyau yayi masa ba musamman yadda aka ‘kawata gyaran gashin nasa da ya ji mayına da turare kala kala na gyaran kai , ‘kafarsa kuwa sanye yake cikin ‘bakin takalmin Yeezy da ake hango dogayen fararan ‘yan yatsunsa da suka sha gyara sosai , hannayensa gabaki d’aya suna cikin aljihun sa , a hankali yake binta da fararan sexy eyes d’insa , gabaki d’aya yau bai sanyata a cikin idanuwan saba sai yanzu, yadda yaga ta kulle idanuwan ta ne yasa ya d’an murmushi kad’an da gefen kumatun sa dan idan ba kula kayi sosai ba bazaka ta’ba cewa murmushin yayi ba , gabaki d’aya idanuwansa suna kanta musamman shigar da tayi ba ‘Karamun yi masa kyau tayi ba , lumshe idanuwansa yayi kad’an kafun ya tako zuwa cikin d’akin har yanzu Kuma ta’ki bud’e idanuwan nata , Hannun sa biyu ya saka ya d’auke kamar wata Baby, cikin Sauri Abla ta bud’e idanuwanta batare da ta kalle saba ta furta “ Ni kasauke ni”, yadda ta fad’a a shagwa’be ne yasa ya kalli lips d’in ta da sukai pink sosai , har ya zauna kan d’aga cikin sofa d’in d’akin har lokacin kuma tana jikin sa bai sake taba kamar yadda take kiciniyar ‘kwace kanta , kallan face d’in ta yayi sosai ganin yadda ta had’e face d’in ga jaa da ta soma kamar me shirin yin kuka . Cikin wani irin murya mai dad’in sauraro ya furta “ Are you angry ?” Shiru Abla tayi masa sai ma face d’in ta data ‘kara d’aure wa tana kawar ta kanta gefe,hannun sa d’aya ya saka ya talla’bo kwankwasan ta , cikin Sauri Abla ta ri’ke masa hannun tana ‘kara d’aure face d’in ta “ Ni bana so , ka sake ni”, ‘kara ri’ko kwankwasan nata yayi sosai a jikin sa kafun ya ‘kara furta “ Are you angry?”a maimakon Abla ta bashi amsa sai kawai ta fashe masa da kuka tana ‘boye face d’in ta a cikin ‘kirjinsa “ Ya Allah “ shine kad’an abunda Big Boss ya iya fad’a kasan zuciyarsa sai idanuwansa da ya lumshe yana sauraran yadda take kukan , shi kad’an yasan me yake ji cikin zuciyar sa kamar Wanda ake zubawa narkakken dalma haka yake jin zuciyarsa , ganin ta’ki dena kukan ne yasa ya d’ago da face d’in yana kallan yadda hawaye suke zubo mata sosai , “ Bana san kuka ,Okay ?” A maimakon ta amsa masa sai lips d’inta data turo kad’an tana ‘kara Kawai da face d’in ta , a karo na biyu ya ‘kara juyo da face d’in ta zata kuma kawar wa ya furta “ Don’t you dare “, d’an shagwa’be face Abla tayi zata kuma kukan yayi kissing Lips d’in ta , cikin Sauri ta Mayar da lips d’in da ta turo,bai tsaya a iya lips d’in ba kafun ya sumbaci forehead d’in ta Shima ,Zai sumbaci kumatun ta tayi sauri ‘boye face d’in ta “ Ni ka ‘kyaleni “, shiru Big Boss yayi mata sai hannun sa da ya d’ora akan Baby tummy d’inta , “ Me yasa baki ci abinci ba ?” Shiru tayi masa kamar me shirin masifa ta furta “ Na ‘koshe “, bai ce mata komai ba ya zaunar da ita a gefen sa , zata tashi ya jefa mata wani irin kallo da sai da hantar cikin ta takad’a dan gabaki d’aya babu fara’akan face d’insa , cikin Sauri Abla ta koma ta zauna tana fiki fiki da idanuwan ta , da hannun ya nuna mata alamar ta zuba abinci,a tunanin ta shi zaici shiyasa ta sha’ko masa plate d’in da abinci, tana mi’ka masa ya ri’ke hannun ta da plate d’in, “ oya eat them all “, cikin Sauri Abla ta zaro idanuwan ta jin abunda yace , cikin Sauri Abla ta marairaice masa “ Ni bana jin yunwa fa “, Lumshe mata idanuwa yayi kafin ya furta “ kinji abun da nace ?”, banza Abla tayi masa sai kallan abinci da tayi , cikin d’an ‘baci ‘bacin rai ta soma cin abincin kamar zatayi kuka , ko spoon 5 batayi ba ta kallesa ko zai ce ta bari amma ko kallan ta bai yi ba , sai da yaga at any moment idan ta ‘Karaci zatayi amai ya rabu da ita , zata ajje abun ya kalleta face d’insa babu fara’a , “ am hungry too “, d’an kallansa tayi ganin yadda ya had’e face tashiga taitayin ta , abincin ta mi’ko masa amma ya ki kar’ba , kalmar “ feed me “ da taji ya ambata yasa tayi saurin kawar da kanta ganin yana ‘ko’karin d’ago da face d’in sane tayi saurin d’aukar spoon ya dakatar da ita “ with your hands “ Now !” Ya fad’a da d’an ’karfi da Sauri ta d’ibi lafiyayyiyar fried rice d’in ciki ta kai masa baki , kamar bazai ciba sai kuma ya bud’e bakin sa kad’an tasaka masa zata janye hannun ya ri’ke mata shi ahankali yake tauna abincin sai da ya cinye sannan ya saka fingers d’in ta a baki yana sid’e ’yan yatsun hannun nata , yadda taji wani yarr har cikin kwakwalwarta ne yasa tayi ‘ko’karin janyewa amma ya’ki bata damar hakan, a karo na biyu da ta kai masa abincin still abinda yayi mata Kenan kamar zatayi kuka Sabida yadda take jin ta , zatayi na uku ya kauda kansa tare da ajje abincin gabaki d’ayan ta ya d’aga zuwa toilet da kanshi ya wanke mata hannun ta sannan ya ‘kara d’aukar kamar Baby, suna fitowa ya kuma zaunar da ita kan Laps d’insa , cikin husky voice d’insa ya furta “ when ever I’m around akan laps d’ina kawai zaki zauna and don’t be stubborn “Ya ‘karasa yana hugging d’inta sosai a jikin sa , shiru Abla tayi masa har tsawan mintuna 7 yadda yaga kanta yayi gefene ya bashi tabbacin bacci tayi a jikinsa shiyasa ya gyara mata kwanciya tsawan 10 minutes kafun ya kwantar da ita akan gadon yaya lullu’beta da duvet, forehead d’inta yayi wa kiss kafin ya sumbaci lips d’inta shima kad’an “ rigimammiya “ ya furta kad’an kamar me rad’a har zai juya ya bar d’akin sai ya zaro wata Babbar waya iPhone 15 a aljihun sa , karatun sudais ya kunna mata kafun ya ajje mata Daidai saitin kunnan ta bayan ya rage mata volume , yana barin d’akin gabaki d’aya.