Sashe 71
Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Su Little kai tsaye part d’in His Excellency suka nufa , yau kwata kwata bai fita ba Sabida wani dalili nashi, a falourn da suka saba zuwa da suka je amma babu kowa a falourn, cikin d’an tsuke fuska Little ya furta “ Yaya prince kawai ka ajje mu tafi in sun fito ai zasu gani “, hararar sa Prince yayi “ idan na ajje zaka dawo kayi masa bayanın Wanda yake a a kawo masa ?I think nasan inda yake , follow me “, biyo dan kuwa little yayi, Lifter Suka ‘kara hawa zuwa last falour , da kallo d’aya mutum zai gane ba ‘karamin kuka naira tayi ba lokaci da ake tsaya wajan, basu tsaya ba suka shiga ‘kofar farko da suka gani, gabaki d’aya mutanan falourn d’agowa sukai suma kallansu da basu ta ‘ba hawowa nan d’in ba musamman da ya zama kamar falourn da suke tattauna abu mai mahimmanci , sosai suke kallan su prince da suka shigo ‘kasa ‘kasa sukai sallama amma babu Wanda suka kalla a cikin d’akin. “ Easy work”, cewar Prince ganin su Didi suma a falourn , kai tsaye abincin hannun sa prince ya kai inda His Excellency yake ba tare da ya ce komai ba sai Wanda ya kai ‘bangaran su Diidii, d’ayan kuma Little ya sai wa Uncle , hannun sa Uncle ya ri’ke “ yau Little d’in nawa bazai mun magana bane ? Menene wannan abun da kuka kawo “ shima yau Little bai kalli Uncle ba “ Lil ce tace na kawo muku “, yana fad’an hakan His Excellency ya saki murmushi me d’au sauti, dan sosai yaji dad’in hakan , yana ‘ko’karin magana Little yayi Saurin futa da sauri , maida kallansa yayi kan prince da shima ya juya zai bar Wajan “ kuna fushi da Abbun ku amma kuka kawo mun abinci ?” Shiru Prince yayi kamar yana tunanin abunda zai ce “ Munyi wa Lil al’kawarin ko me take so zamuyi mata shiyasa mu ka kawo muku” shima yana gama fad’ar hakan ya bar falourn . Cikin sauri Mamy ta kalli His Excellency “ Yaya wacece Lil kuma ?”, a maimakon His Excellency ya bata amsa sai Uncle ya bata “ ‘kanwa ce kuma sirikar gidan nan da suke so sosai , duk Wanda yake neman tashi hankali ya ta’ba ta, a kanta har Auran dole suka had’a wasu Kawai dan sun saka tayi kuka “, ya ‘karasa yana sakin dariya tuno Auran su yar president da Big Boss ya d’aura musu aure , baban Baby ne ya furta “ Kamar ya bamu fahimta ba ? Wa haka d’au rawa aure? Sannan wacece yarinyar da har ta zama sirikar gidan nan bamu da labari ?. Ajje coffee d’in hannunsa uncle yayi yana kallan Dadyn Baby , “ wallahi Adam zan iya rantsuwa ta dalilinta yaran nan suke zaune a gidan nan , if not yadda Farooq ya d’au zuciyar sa babu mai iya tan’kwara shi , amma itama ‘kanwar tasa idan taso yar rigima ce kuma ko me zakayi mata sai ta fad’i gaskiya bata shakkar fad’ar ta a gaban ko wanene , kamar yadda suke santa itama hakan ce a wajan ta , bari na baku takaitaccen labarin ta .
Tun daga had’uwar ta dasu Little har zuwan su Nigeria Dalilin ta sai da Uncle ya basu labarin , yana gamawa His Excellency ya saki wani murmushi, Dan su Nani da Mama gabaki d’aya kasa magana sukai sai kwalla da suke sharewa , “ waya fad’a muku bata da uba ?” Cewar His Excellency, gabaki d’aya sai suka kallesa jin abunda yace “ Ni nan daga yanzu nine uban ta dan sosai nake jinta a raina kamar ‘yar da na haifa , ban damu da labarin ta ba amma tabbas zan nuna mata gatan da ko wana uba yake nunawa yar sa , “ kallan sa ya mayar kan Mamy da itama take sakin murmushi “ Na yadda dake Hauwau , ina so a fad’o mun duk abunda ake bu’kata na bikin yar gata , nan da sati uku za’ayi bikin Auran su da ba’ayi ba , da kud’ina ba da kud’in kowa ba , duk abunda ake bu’kata a Zara cikin black card d’in nan “ ya ‘karasa yana ajje wani Black card “, babu Wanda baiyi na’am da zan can nan ba shima Dadyn Baby duk da bai ganta ba sosai yaji farin cikin hakan “ Ai bazaka kashe kadan kai kad’an ba , komai da ya danganci furnitures ni zanyi wa yata bata san karere”, ko wa yasan da His Excellency yake shiyasa sukai dariya ,duk cikin falourn babu Wanda baiji ‘kaunar Abla ya shiga ransa musamman Mamy da ta ‘kudurta gyara yarta sosai dan tana barin Wajan nan zata kıra wacce zata fara yi wa ‘yarta gyara. Gabaki d’aya wannan tattaunawar da ake Nani bata cikin su shiyasa batasan abunda yake faruwa ba .
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
8:40pm