← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 100

Sashe 69

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

****Big Boss na fitowa sukai clashing dasu Sauban da suma suke ‘ko’karin shiga part d’in, ajiyar zuciyar Sauban ya sauke “ We’re are you going Dude ? Don’t tell me you guys are leaving me here ?” Banza Big Boss yayi masa zai wuce Sauban yayi saurin shan gaban sa “ please say something Dude , shi wannan d’an rainin hankalin na masa magana amma ya mayar dani d’an iska please say something , please “, agogon hannun sa Big Boss ya kalla kafun ya furta “ I need to go somewhere “,cikin za’kuwa Sauban ya furta “ that’s means Dude you guys are not leaving for sure ?”,shima kallan sa Bobo dake tsaye a wajan yayi “Yau nace zamu tafi?while zamu tafi after that old lady ( Didi)left , “, wani farin cikine ya kama Sauban amma duk da hakan sai da ya ‘kara kallan Big Boss “ Dude , you change at all yadda naga mood d’inka jiya definitely you guys are leaving, please what make you change your mind ? Please Dude tell me dan gaskiya yau sai na bada kyautar gift , d’an dakatawa Big Boss yayi daga tafiyar da yake sanyi kafun ya kalli Sauban cikin idanu “She wanted to stay here and I respect her decision, any problem ?”, shi kansa Sauban baisan lokacin da ya furta “ Kutmar Uba , Man? Daman soyayya zata saka ka canza ? You ? I have to give her a gift wallahi “, ta’be baki Big Boss yayi yana kallan Bobo da yayi mutuwar tsaye, cikin sauri Bobo da sauban kamar wasu yara sukayi hugging juya “ Finally, my dream came true ,” cewar Bobo yana kallan Big Boss da ya had’e musu rai ,  cikin za’kuwa Bobo ya furta “ Big Boss tell me you love Sister , please?”, a maimakon ya amsa masa sai yayi wucewar sa zuwa inda Victor ya bud’e masa mota, a gaban idanuwansu Big Boss ya shiga mota , Victor ya rufe masa kafin su bar gidan gabaki d’aya . A fili Sauban ya furta “ Oh my God , am I dreaming ?wallahi he change , do you think if not now Big Boss zai zauna a cikin gidan nan for another minutes ?I will surely give her a surprise , let’s go “, cewar Sauban yana jan hannun Bobo kamar wani ‘karamin ‘kaninsa zuwa part d’insu. Shima sai faman murmushi yake , haka kawai wani irin farin ciki ya kamasa Sabida canzawar Big Boss d’in.

       ABLA 

 Tana shiga d’aki wayar ta dake kan bedside ta d’auka tare da sata a charge ganin babu charge gabaki d’aya a cikin ta . Tana sawa kuma bata zauna ba , tunanin abunda take sanyi ne yake mata yawo a zuciya , d’an ‘karamun murmushi Abla ta saki tana komawa kitchen , Doyarta ta yanka da yawa ta d’ora a huta, kafin ta soma d’auko kayan had’in miyar Egusi d’inta da take so , cikin ‘kan’kanin lokaci ta soma aikinta ganin akwai duk abubuwan da take bu’kata a çıkı. 
   Pounded yam Abla ta soma yi , a cikin turmi abunta ta daka ta sosai kafun ta saka suna warmers d’in da take bu’kata , Miyar Egusi d’in da tayi gabaki d’aya ’kamshin sa ya cika ko ina na cikin kitchen d’in duk da abun zu’ke kamshin da ta kunna , tana gamawa shima cikin warmers ta zuba lafiyayyiyar equsi d’inta da taji ganda da kifi da nama da ta saka sosai a ciki.  

   Jakar abincin ta da ta fara had’awa  ta d’auka tare da fitowa falourn , a maimakon ta kaishi kan Dinning sai ta ajje akan center , zata juya Kenan taji sallamar Little , da Sauri Abla ta furta “ Yaya Little “, murmushi Little yayi mata duk da fuskar sa ta d’an fad’a kad’an “ I missed you Lil , you just Disappeared from no where “,  wasa ta farayi da fingers d’inta “ am so sorry Yaya Little bayana ba charge shi baka jini ba , how are you feeling now ?ya jiki ?” Wani murmushin Little yayi mata “ am fine Lil daman ba wani serous matsala bane “, prince da tun d’azu baiyi magana ba ya furta “ Kamshin me nake ji ? Am start feeling hungry now “ d’an ’bata fusku Abla tayi “ Yaya prince baka yi missing d’ina ba kenan ?” ‘Dan zaro mata ido prince yayi “ Ni na isa nace miki haka ? Kema kin san nayi missing d’inki , ‘kamshin Abincin ne ya d’au hankali na , kamar hanci komai ba haka nake jira “, Kallansa Little yayi “ Allah Yaya prince kai a cici ne duk lokacin da baka ci abinci ba akwai matsala , “ d’an hararar sa Prince yayi yana furta “ Eh naji d’in Nidai koma Menene aka dafa a zubo mun dan I most taste it.” Dariya Abla tayi kad’an kafun ta furta “- Am coming yaya prince give me a minutes “ tana juyawa prince ya furta “ Yawwa Lil d’ita, a haka Abla ta ‘karasa kitchen su kuma suka zauna akan kujeran falourn , ba a d’auki dogon lokaci ba Abla ta fito hannunta da tray cikin Sauri prince ya kar’ba yana ajjewa bai tsaya ‘bata lokaci ba ya bud’e warmers d’in. Cikin Sauri ya furta “ Wow”, mi’kewa Abla tayi tsaye “ Yaya prince bari nayi serving d’inku “, kansa prince ya girgiza mata “ No! No kiyi zaman ki kawai , kar na gajiyar dake “ da haka ya d’auki plate d’insa guda d’aya yayi serving pounded yam d’insa da Egusi d’insa , yau ko tayi bai yiwa Little ba ya soma cin abincin sa “, gabaki d’aya tsayawa kallan sa sukai cikin tsokana Little ya furta “ wallahi kai dai Yaya prince matar ka ta shiga uku Sabida cin abincin ka , ina ji kullum kwana d’au za’a dunga dafa muku abinci, Sabida rowa Yaya ko Bismillah babu?”, hararar sa prince yayi yana ci gaba da cin abincin sa ko magana ya kasa , itama Abla Little ta zubawa nashi abincin, sosai kuwa ya ci abincin sa ,  daga shi har prince sun kasa magana Sabida santin da suke yi su kad’an , suna gamawa Prince ya furta “ Alhamdulillah “, Abla d’auke tray d’in ba sai da Suka gama ci sannan ta kawo musu ‘karamun bowl me cike da ruwa , hannun su kawai suka wanke a ciki, sai a lokacin Abla ta dawo ta zauna “ Lil so you know how to cook such kind food amma shine bakya kira na ko? Anytime kikayi just give me a called zan zo naci kinji ?because the food was so very excellent, i so much enjoyed it “, shima Little sosai ya fara santin abincin nata , sun d’au dogon lokaci suna maganar kafun idanuwan Little ya sauka akan jakar abincin da Abla ta ajje “ Lil what’s this ? Menene a ciki ?” Kallan Abincin Abla tayi kafun ta kyalli Little da yayi mata tanbayar “. 
Chapter 69 · 0% Book details