← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 100

Sashe 78

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

9:10pm gabaki d’aya mutanan gidan suka taru a babban falourn da ake cikin abinci, babu Wanda baiyi mamakin zuwan su Little ba musamman da sukaga har da Bobo dan sai da Little yayi mata al’kawarin zuwa , shima sai da ya kusa yi musu kuka tukunna suka zo amma babu Wanda suka kula, kowa tunanin sa zuwan Big Boss ne , Abla ma na kusa da su Eshaal haka kawai take san ganin sa , sai da suka ‘kara kusan 5 minutes kowa yana Tuna’nın zuwan sa , daman sun san bazai zoba shiysa gabaki d’aya kwiwar su ta sake musamman His Excellency da yake san saka shi a cikin idanuwansa, Harry ma sai zuba ido take tana jiran ganin Masoyinta “ It’s eat “ cewar His Excellency ya fad’a a sanyaye, sai da suka hau Dinning har su M.sarah na ‘ko’karin serving d’insu suka ji kamshin turaransa, da Sauri Abla ta d’ago da fuskarta ganin ita yake kallo ne yasa ta sunkuyar da tata fuskar, babu Wanda bai ji shock din zuwan saba , gabaki d’aya ya basu mamaki , tsuke musu fuska ya ‘karayi ba tare da yace komai ba ya ‘karasa Dinning din , James zai yi magana Big Boss ya bashi amsa da ido shiysa yayi shiru , babu Inda ya zauna sai kujerar da take facing ta Abla , duk yadda yaso su had’a ido ta’ki yarda da hakan, His Excellency kuwa duk da bai kallesa ba zuwan sa yayi matukar sashi farin ciki, a haka aka soma serving d’insu, za ayi na Big boss, Little yayi saurin mi’kewa “ it have being long , bari nayi serving dinka “ da haka Little yayi serving dinsa bai ce komai ba Sabida Kallan Abla da yake ta kasan ido ganin taki kallansa ne yasa ya cire takalmin ‘kafarsa d’ara tare da ta’bo tattan, dan ya mutsa fuska Abla tayi tare da d’auke fuskarta. 

IBTISSAM
      ( A heart touching story of love and destiny)

Story & written 
      By
Mss Lee   

                     09134652921

    TALLA!! TALLA!!! TALLAH !!!!!!!

SHIN KUNSAN WACECE HAJIYA NUSAIBA BR~B ZURU ?❤️

HAJIYA ~ NUSAIBA DR~B ZURU

MAMALAKIYAR ZIMH ISLAMIC AND MEDICINE DAKE RINGH ROAD A KANO NIGERIA
Tazo muku da ingantattu ko sahihan magungunan mata masu inganci, ba’anan kad’ai ta tsaya ba har da na cututtuka da Turarukan wuta , Humra masu shegen ‘kaushi . Abun Alfaharin kuma tana bada sarı cikin sau’ki, sannan kuma suna aikawa duk inda mutum yake afad’in duniyar nan. 

Duk wacce ta siya magungunan Hajiya Nusaiba Dr B zuru, taga be yi mata aiki ba tazo za’a dawo miki da kudin ki . 

KA’DAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKE SIYAR WA

1️⃣ Hadin amarya
2️⃣Hadin mai jego
3️⃣Hadin sabon budurchi
4️⃣Hadin Kaza Yar’Suddan
5️⃣zuma -Tsumi- Tabaje da sauransu
6️⃣Turaren Sandal ruuu& flastic Sandal
7️⃣ Hadin Hawwi domin inganta zafafiyar kauna
8️⃣Hadin bagadad,kahlij,kajiji,gafgaf dasauransu
9️⃣Hadin humra soyaya dole ta matan aure da normal humra

DON SAMUN ‘kARIN BAYANI KU NE META TA WANNAN NUMBER KAMAR HAKA : 
    08133647913 

   KANO NIGERIA 

LOCATION: RING ROAD BAYAN GİDAN MAN NAZARGO.

       SIYAN NAGARI MAIDA KU’DI GIDA

PAID BOOK

2 PAGES NA HA’DE KAMAR YADDA NAYI AL’KAWARI , PAGE ‘DIN JIYA DA NA YAU .

BOOK 2 
         S_____ 25

‘Kara kallan ta Big Boss yayi ko zata kallesa amma ta’ki kallan sa sai d’an tsuke fuska da tayi kad’an , ‘kafa yasa ka zai ta’ba ta tayi saurin janyewa , babu Wanda ya kula da yana yin su , “ Let’s  eat “, cewar Mamy , Nani da Momy ne kawai basa Wajan Dinning d’in sai James da M.Sarah sai Jenny da sukai serving d’insu. Kasa cin abincin Abla tayi Sabida yadda taji idanuwansa yana yawo a jikinta, ga mutanan gidan da suke zazzaune a wajan suma, ‘Yar ‘karamar ajiyar zuciya ta sauke tana ‘kara kallan abinci, “Daughter a dafa miki wani abincin ne? “ cewar His Excellency da ya d’ago da fuskar sa, cikin Sauri Abla ta girgiza sai kuma ta bud’e bakin ta “ Ah’ah zan…ci”, hannunta har rawa yake lokacin data d’auki spoon d’inta ya Big Boss da shima yake kallanta duk ya hanata sakewa. ‘Dan shiru His Excellency yayi yanaso yayi wa Big Boss magana amma yana tsoran halin nan nasa na zuciya sosai duk da kusan halinsa Big Boss ya d’auka shima . A ‘bangaran Eshaal ma gabaki d’aya kasa sakewa tayi kamar wacce take zaune akan ‘kaya , ga Bobo da yake facing d’inta akan kujera duk lokacin data d’ago face d’inta zata Tuba abunda ya faru , shiyasa ta kasa cin komai sai tsakura da take. Su Hajiya Falmata kuwa kamar su mutu dan haushi banda Harry da takeji kamar ta sha’ke Abla ganin ta zauna mata a waje, Hajiya Sa’adatu ma da yarta dau salma sai faman Harara suke mata ‘kasa ‘kasa, banda Hajiya karima da fuskarta take d’auke da murmushi, hatta su Amal abincin su suke ci hankali kwance, ga Hajiyar America da Didi da bakinsu ya kasa rufuwa sabida farin ciki , lokaci zuwa lokaci sai su d’ago su kalli kowa da kowa na cikin gidan.

    Gyaran murya His Excellency yayi kafin ya kalli Big Boss “ Baka soma cin abincin ba?”, gabaki d’aya sai mutanan falourn suka dakata da abunda suke kowa yana jiran ganin reaction d’in Big Boss , hatta Bobo da Sauban duk data tawa yayi, had’e face d’insa Big Boss yayi yana ‘ko’karin bud’e bakinsa Uncle dake gefensa yayi saurin ri’ke masa hannu, ita kanta Abla batasan lokacin da ta d’an ta’ba masa ‘kafa ba , Lips d’insa Big Boss ya d’an danne ba tare da yayi magana ba . 

    ‘Karan takun da suka soma jine yasa suka d’ago da kawunansu banda Big Boss da Abla , His Excellency hankalin sa gabaki d’aya yana kan Big Boss , lokaci zuwa lokaci kuma yana kallansu Little , Arwa ma data zauna can nesa da Abla lokaci zuwa lokaci tana satar kallanta daga inda take . Muryar Nanni ce ta karad’e ko ina na falourn bayanta kuma Momy ce dasu ka had’a Kai “Ah’ah yau kuma ahaline gabaki d’aya suka had’u?abun ya bani mamaki , Yaya har dasu Big Boss gaskiya wannan Dinner d’in babba ce “, ta fad’a tana sakin wani shegen murmushi musamman da taga Big Boss a wajan . “ zakuga abunda zan muku”, ta fad’a cikin zuciyarta , ganin babu Wanda ya kulata a cikin falourn ya ‘kara hassalata , waje ta samu a kusa da Momy data zauna yanxu tana kallan kowa da kowa na falourn , d’an ta’be baki Nanni tayi kafun ta furta “ Gaskiya naji dad’in ganin kowa da kowa na familyn nan sosai ciki kuma harda wad’anda ba’asan asalin su ba . Wani irin ‘kwarewa Abla tayi , Eshaal da taji kamar tayi kuka tayi saurin mi’kewa zata bata ruwa , Big Boss ya mi’ka mata ruwan gabanta , Hannunta har rawa yake lokacin da ta d’auki ruwan , d’an kad’an Abla tasha ta ajje cup d’in , a hankali ta mi’ke tsaye Mamy da barajı dad’in abunda Nani tayi ba ta furta “ Ina zakije kuma ?”, a sanyaye Abla ta furta “ Na ‘koshi ne “ zata kuma mata magana Dadyn Eshaal ya girgixa mata ta , Baby wani irin bakin ciki ne ya kamata kamar ta samu Nani tayi mata shegen duka , duk da wasu daga cikin yan gidan sun ji dad’in abunda tayi . Sai da Abla ta bar wajan gabaki d’aya kafun Big Boss ya d’ago da idanuwansa zuwa saitin Nani da take ‘ko’karin Kai lemo bakinta . Yadda taga yana kallanta ne yasa ta kasa shan leman tana d’auke idanuwansa , kallan second 5 yayi mata ya d’auke  fuskar sa kamar ba shi ba ya furta “ kinyi ‘ko’karin cutar da ‘kanina , yanzu kin ‘bata ran matata? Kinsan dalilin da yasa na bari ta bar Wajan ?huh “ sai ya d’an tsuke face d’insa kamar me wahalar yin magana “ wannan ya zama karo na farko kuma na ‘karshe da ko kallan banza wani yayi wa matata , ke kuma idan kika ‘kara yin gangancin ko da kallan banza ne , daga ranar bazaki ‘kara ganin kowa naki ba , dan sai na ‘batar dake , inda duk neman da za’ayi miki baza’a ta’ba samun kiba , zan ‘batar dake ta yadda yan yatsun ki bazaki ta’ba ganewa ba”, yana gama fad’ar hakan ya ajje spoon d’in abincin da ko ci baiyi ba ya bar wajan. Su Mamy kam sunji dadin abunda yayi hatta His Excellency da ya d’an kallesa duk da yadda ya ‘boye ‘bacin ransa amma shi yajisa a harsan sa , d’an ‘karamun murmushi Bobo yayi mai sauti ganin yadda Nani tabi ta soma diriricewa , “ Baki san wanene shiba ko ?huh yana miki magana ne a matsayin soja ba wai Wanda kika sanshi ba , in labarin sa kike ji yau zaki san wanene shi OUMAR FAROOQ MUHAMMED AL-TAUFEEQ , THE GENERAL OF THE ARMY, mutumin da ‘kasashe da yawa suke so ko ziyara ne ya kai musu , kiyi addua kar karnukan farauta suji muryar da yayi anfani da ita dan zasu farauto naman kine yana musu umarni da ido.” Sai kuma ya mi’ke tsaye zai bar Wajan “ Ina tayaki murya duk lokacin da kika shiga AMERICA ki ambaci sunan BIG BOSS , na tabbata har kyautar abinci sai sun baki “, yana gama fad’ar abunda zai fad’a ya d’an kalli side din Eshaal ganin yadda take murmushi, haka kawai murmushi ta shima ya saka shi murmushi, shiyasa ya murmusa tare da barin wajan. 

   ‘Yan falourn rasa abuncewa sukai sabida tsantsan mamaki, babu abunda ya fi basu mamaki kamar sani Big Boss , Wanda manya manyan labarai ake akansa duk da babu Wanda ya ta’ba ganin fuskarsa , lokaci d’aya suka sha jinin jikinsu gabaki d’aya musumman su Hajiya Harry da Falmata , Nani da tayi maganar wani irin fitsari ne taji yana ‘ko’karin zubo mata duk da taji alamun ta farashi a wandanta, tsoro ne ya kamata musamman kallan da Big Boss yayi mata dashi, tana ganin Hajiyar America tana ‘ko’karin yin magana tayi saurin barin Wajan ganin ranta ya ‘bacı fitsarin fara ke ‘boyewa yana ‘kara zubo mata.
Chapter 78 · 0% Book details