← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 100

Sashe 57

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun abunda ya faru tsakanin ta da Simba take tsoran fita , Gabaki d’aya ta zare kamar mahaukaci yanzu ko attachment din bata sawa lokaci d’aya duk ta rame babu abunda ya ke ‘bata mata kamar  kamar Tuna’nın Big Boss na tare da Abla ba ita ba , wannan abu yafi komai tsaya mata arai gabaki d’aya Batasan Abla bata cikin gidan ba , Tuna’nın ta a kulle tana part d’inta a falourn kamar yadda ta saba zuwa ta tarar da ita. ga uban ladaftar da su da M. Sarah take musamman ita da take bata da kunya gwanda yanzu sauran ba kullum take kiran su ba banda Harry da take ladaftar wa ganin rashin kunyar ta , kullum sai ta saka kwallin boka a idanuwanta tana san zuwa inda Big Boss yake amma tsoron Simba ya hana rayuwar sakat gabaki d’aya . Ga Hajiya falmata da itama ta fita sabgarta tun lokacin da taji labarin mu’kamun da ya koma wajan Abla gabaki d’aya hankalinta yana kan hanyar da zata dawo da mu’kaman kan take gabaki d’aya gold d’inta da dukiyar ta bayar Sabida ayi mata aiki kwakkwara akan mutanan gidan yadda komai zai koma ikonta. Shiyasa yanzu ko damuwa da  fita batayi Sabida burin da take San fara cimmawa.

WASHE GARI

Kiran sallah a kunnan Big Boss akayi sa Sabida gabaki d’aya bai runtsaba yana gefen Abla ga System d’in da ke kusa da shi yana operating d’inta . ‘Dan d’ago da kansa yayi zuwa saitin fuskarta , bacci take abunda hankali kwance , ga kiran sallah da akeyi, ya lura kamar yanzu ne baccin ya fi mata dad’i. Tsoran tayar da ita yake daga baccin Sabida gudun rigimar da zata soma shiyasa bai tashe taba ya sauka akan Bed d’in a hankali , kai tsaye Toilet ya nufa bai wani jima can sosai ba ya fito har lokacin Abla bacci take musamman yadda ta ‘kara lumewa cikin duvet.
     Ba Tashe taba , sannan bai ‘karasa inda take ba yabar d’akin gabaki d’aya Sabida sallar da za’a fara. 

****** 6:50am ya shigo cikin d’akin ganin har lokacin bacci take yasa ya d’an bud’e idanuwansa kad’an , baisan da wata kalar rigimar zata tashi idan ta farka, amma ganin lokacin sallah na tafiya yasa ya ‘karasa inda yake , bacci take abunda hankali kwance , daga gefen gadon ya zauna yana ‘kurawa fuskarta ido, bai san ya akai ba , bai san a wani lokaci ba soyayyar ta shigesa, irin san da shi kansa bazai iya fad’an adadin saba , sosai soyayyar ta take ‘karuwa a cikin zuciyar sa ko wana da’ki’ka da lokaci musamman idan tana kusa da shi. Peck yayi mata a goshi kamar wacce take bacci da ido d’aya ta ware idanuwanta gabaki d’aya , ganin sa a kusa da itane yasa ta bud’e baki zata fara kuka yayi saurin had’e hannun shima waje d’aya kamar wani ‘karamun yaro ya ‘bata fuskar sa “ Dan Allah karkiyi kukan nan please Sunshine Am sorry, don’t hurt with your cry’s okay ?” Abla bata san lokacin da ta sakar masa manyan idanuwanta da sukai shining ba alamar a kowane lokaci zata iyayin kuka , d’auke fuskar ta tayi daga şaitin ‘barin sa tana ‘kara tsuke fuskarta, hannun ta yayi ‘ko’karin ta’bawa cikin tashin hankali ta furta “ Ni karka ta’bani”, kallanta yayi idanuwansa har su soma lumshe ga shi tana ‘ko’karin sa masa ciwan kai da rigimarta “ it’s okay kinga har anyi sallah bari na temaka miki kiyi wanka sai kiyi ko?” Cikin Sauri Abla ta ma’kale kafad’a “ Ni zanyi abuna “ ta ‘Karasa tana ‘ko’karin mi’kewa , a hankali ta soma d’aga ’kafarta, ko ta ku biyu batayi ba tayi saurin tsaya tana ‘ko’karin ja baya , a hankali ta furta “ Ouch” da sauri Big Boss ya ri’ke mata hannu ganin yadda take ya mutsa fuskarta yasa ya d’auketa gabaki d’aya zuwa toilet d’in. 

***** basu wani jima sosai ba ya ‘kara fito da ita hannunsa sanye da towel d’in da ya nannad’eta a ciki, a hankali ya zaunar da ita yana kalan yadda ta ‘bata rai , ‘karamin murmushi ya saki Daidai saitin kunnanta ya furta “ I Love you Sunshine and I’m so sorry , bari na kawo miki rigar da zaki saka kiyi sallah okay ? But try to forgive me please “ cikin Sauri Abla ta ‘kara kawar da kanta musamman yadda taji lokaci d’aya zuciyar ta taharba. 

Wani irin doguwar riga ya d’auko mata mai kauri tare da hijab da bazai ta kura mata ba , da kanshi ya temaka mata ta saka kayan, da zatayi sallar ma yana jin lokacin da take shash she’kar kuka , tana idar wa ta tafi zata kwanta yayi Sauri ri’ke mata hannunta yana jingina ta daga jikinsa “ I love you and am so sorry , Mai kike so?” ‘Bata fuska Abla tayi kafun ta furta “ kamar dani gida “, d’an murmusawa yayi kad’an ganin yadda ta yi maganar kamar Baby “ it’s Okay , tunda Baby na tanaso na mayar da ita but kinga safiya ne yanzu muyi bacci first ko?” Yadda yağa reaction dinta kamar me shirin yin kuka ya furta “ it’s okay na bari mai kikeso?” Cikin sanyin murya Abla ta furta “ Yunwa nake ji”, karan hancinta ya ta’ba kad’an “ Me Sunshine zataci?”, kai tsaye Abla ta furt “ d’an sililuf da Youghurt “ d’an bud’e idanuwansa Big Boss yayi dan bai gane abunda tace ba gwanda Youghurt ma.  “ Menene shi?” Ta’be baki Abla tayi kafun ta furta” ‘Dan sililuf  shi zanci” wayarsa ya d’auko “ okay bari na saka a nemo miki” ‘bata masa face Abla tayi “ Ni kai zakayi mun” shi kansa baisan lokacin da ya furta “ whatt “ ba.

IBTISSAM
      ( A heart touching story of love and destiny)

Story & written 
      By
Mss Lee   

                     09134652921

    TALLA!! TALLA!!! TALLAH !!!!!!!

SHIN KUNSAN WACECE HAJIYA NUSAIBA BR~B ZURU ?❤️

HAJIYA ~ NUSAIBA DR~B ZURU

MAMALAKIYAR ZIMH ISLAMIC AND MEDICINE DAKE RINGH ROAD A KANO NIGERIA
Tazo muku da ingantattu ko sahihan magungunan mata masu inganci, ba’anan kad’ai ta tsaya ba har da na cututtuka da Turarukan wuta , Humra masu shegen ‘kaushi . Abun Alfaharin kuma tana bada sarı cikin sau’ki, sannan kuma suna aikawa duk inda mutum yake afad’in duniyar nan. 

Duk wacce ta siya magungunan Hajiya Nusaiba Dr B zuru, taga be yi mata aiki ba tazo za’a dawo miki da kudin ki . 

KA’DAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKE SIYAR WA

1️⃣ Hadin amarya
2️⃣Hadin mai jego
3️⃣Hadin sabon budurchi
4️⃣Hadin Kaza Yar’Suddan
5️⃣zuma -Tsumi- Tabaje da sauransu
6️⃣Turaren Sandal ruuu& flastic Sandal
7️⃣ Hadin Hawwi domin inganta zafafiyar kauna
8️⃣Hadin bagadad,kahlij,kajiji,gafgaf dasauransu
9️⃣Hadin humra soyaya dole ta matan aure da normal humra

DON SAMUN ‘kARIN BAYANI KU NE META TA WANNAN NUMBER KAMAR HAKA : 
    08133647913 

   KANO NIGERIA 

LOCATION: RING ROAD BAYAN GİDAN MAN NAZARGO.

       SIYAN NAGARI MAIDA KU’DI GIDA

PAID BOOK

BOOK 2 
         S_____ 19

Fiki fiki Abla tayi masa da idanuwanta da ta d’an waro kad’an . Cikin cool voice ya furta “ what’s suluf suluf ?” Ita kanta batasan lokacin da dariya ya kwace mata ba , ganin Kallan da yake binta dashi ne yasa tayi saurin toshe bakinta . “ it’s funny ?” Ya tanbaya lokacin da yake d’aga girar sa guda d’aya , d’an kanta Abla ta girgiza masa a hankali “ ‘Dan sululuf nace fa , kuma abinci ne da ake ci da yaji..” kallan bakinta da take maganar yayi kamar ya mayar da idanuwansa kan fuskarta , cikin Sauri Abla ta janye nata idanuwan ganin kallan da ya je fa mata ,muryar sa data tsinkaya a cikin kunnan ta yasa ba shiri ta kalle sa “ pepper zaki ci da safe ? Why ? Banda abin yaji.” ‘Daga kanta Abla tayi daga kafad’un sa ganin tana ‘ko’karin mi’kewa ne yasa mata kaifafan idanuwan sa da ba shiri ta koma ta zauna “ Rigimar ki tayi yawa fa. Oya mai zaki ci?” Ya fad’a kamar ana fusgar maganar daga bakin sa . ‘Dan shiru Abla tayi kamar mai tunanin abu kafin ta kunshe dariyar da take sanyi “ Fine zansha kunu da ‘kosai “, girgixa kansa yayi kad’an yana kallanta “  what’s that again ?”, yanzu ma dariya ya Abla ta ri’ke kafin ta furta “ Bean cake”girar sa ya d’aga kad’an yana motsa la’b’ban sa , cikin sıgar tanbaya ya furta “ That’s what you want ?” Kanta Abla ta jinjina alamar Eh , batare da wani damuwa ba ya furta “ Okay bari na saka Didi tayi maki”, ya fad’a yana ‘ko’karin dialing wata number , cikin Sauri Abla ta kwace wayar tare da kashewa “please karki kirata “, cewar Abla

“Cake Bean d’in fa ?” Narai narai tayi masa da ido , “ Ni bacci zanyi “, bai kuma cewa komai ba sai ji tayi yayi sama da ita zuwa bed , cikin Sauri ta zaro idanuwanta waje cike da tsoro, fahimtar hakan ne yasa ya furta “ Don’t worry . Let’s sleep up”, cikin marairaice abu ta furta “ Amma …” da hannu yayi mata alamar tayi shiru kafun ya furta “ don’t amma anything. Bacci zamuyi”, yar ‘karamar ajiyar zuciya Abla ta saki duk da bata gama sakin jikinta ba , akan chest d’insa ya d’ora kanta yana lullu’besu da duvet, bayan ya rage musu haske kad’an. A fisge ya rad’a mata “ am with you , just sleep off”, har yanzu hannun sa na bayanta yana tapping a hankali , a haka bacci ya d’auke su rungume da juna. 

****** 
 Yau a part d’in su Bobo , Little ya kwana bayan ya gama complain d’in akira masa Yaya da Lil d’in su , har kusan kuka sai da yayi wannan ne dalilin da yasa ya kwana a d’akın Bobo.
Chapter 57 · 0% Book details