Sashe 82
Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
**************
‘Karfe 3:00 na yamma su Abla ne zazzaune akan kujera suna hira, sallamar Little da Prince da ta jine yasa ta d’an d’ago da kanta tana sakin murmushi “ Yaya Little” hararar ta Little yayi yana zama kan kujeran shima , kallan Prince Abla tayi kafun ta furta “ Yaya Prince mai kuma nayi ?” Hannun sa prince ya d’aga mata alamar ba ruwansa, ‘kara kallan Little , Abla tayi cikin marairaice fuska ta furta “ Haba Yaya Little me kuma nayi kake hararata”, shiru ya d’anyi kafun ya furta “ ki taso kawai ki koma part d’in ki , yanzu duk lokacin da mukesan zuwa wajan ki sai mun shigo nan? Kinsan ba masan zuwa nan wajan” cikin Sauri Fanan ta furta “ Haba mana, muma fa munaso ta zauna “ shima kallanta Little yayi kafun ya furta “ Shima can d’in ai zaku iya zuwa ku ganta”, Fanan zata yi magana Abla tayi saurin furta “ Shikenan ku tsaya please, Yaya Little Kayi ha’kuri kaji , kema Fanan kiyi hakuri “, kansa Little ya jinjina mata kafun ya mi’ke tsaye “ Wait a minutes ina zuwa “, bai jira amsar taba yayi wucewar sa zuwa hanyar fita , prince da ya fahimci abunda Little zai yi kawai zai ya ‘kyal’kyale da dariya ba tare da yace komai ba , gabaki d’aya su Eshaal basu fahimci dariyar da yake ba shiyasa suka share zancan little . Kusan mintuna 5 da faruwan hakan sukaji sallamar Little , Fanan ce ta fara d’ago da kanta zatayi magana idanuwanta suka sauka akan Simba da yake gefen Little , a rud’e ta furta “ Wa innahu min sulaimana wa innahu Bismillahir rahmanir rahim , me idanuwa na suke nuna mun ko na makance ne ?”, jin yadda Fanan take surutu ne yasa Baby da Eshaal suka d’ago kawu nan su , a rud’e Baby ta saka ‘kara tana dira daga kan kujera , Eshaal kuwa mutuwar tsaye tayi sabida rud’u, Abla tana ganin yadda suka tsorata ne yasa ta kalli Simba da Little , cikin marairaice wa ta furta “ Haba Yaya Little basu sanshi ba, Kasan dole su tsorata “, Little bai amsa mata ba sai shafa kan Simba da yayi , a kujera Simba yayi kansu, suma basu tsaya ba suka soma gudu a falourn suna tsalle,sabida rud’u Baby har ‘ko’karin hawa flower vez tayi , ganin bala’in ba me tsayawa bane ta fara haki “ Dan Allah kayi hakuri , kai Wana irin mugu ne wai ? Mai mukai maka da zaka sako mana wannan halittar ? To Wallhi kai da Allah dan zan ha’kura wahalar dani da kayi ba “ dariya Little ya saki kafin yayi ‘karamun fito, gadan gadan Simba ya soma nufo Baby itama tace ‘kafa mai naci ban baki ba ? Tunda ta saka gudu bata san inda take takawa ba har ta fice daga part d’in , sai a lokacin Simba ya juyo saitin su Eshaal , itama sai faman had’a zufa take , hannayenta biyu ta had’e masa alamar ro’ko “Dan Allah kayi hakuri mana , Maine ne abun d’aukar zafi da saka sako mana zaki ? Haba mana dan Allah”, Fanan kuwa sabida ‘kuluwa kasa magana tayi sai hararar da take bin Little dashi , ‘kugu Little ya ri’ke kafun ya furta “ an ina Lil zata zauna ?”, cikin Sauri Eshaal ta furta “ part d’inta “, mai da kallansa kan Fanan da ta sha’ki takaici yayi” A ina zata zauna ?” Wani irin harara Fanan ta jefa masa , a zuciye ta furta “ A nan zata zauna sai muga ta yadda zata koma part d’in”, Little najin haka kuwa ya ‘Kara tsokano musu Simba , a guje Eshaal tayi hanyar fita daga part d’in daidai lokacin da su Bobo zasu shigo suma , cikin saurin Eshaal ta ‘buya a bayan Bobo tana sakin ajiyar zuciya, Fanan kuwa tsabar haushi fad’uwa ’kasa tayi , hararar su Bobo yayi shi yayi shida prince kafun ya furta “ Follow me “ cikin Sauri Prince zai yi magana Bobo ya jefa masu wani kallo shid Little da ya d’an shafa gashin kansa “, Yaya..”. “ If you dare …”Bobo ya bashi amsa , shiru Little yayi shima yana kallan Simba da yake zagayesa, d’an le’kowa Baby tayi a bayan Sauban da ta ‘buya “ Wallhi Allah sai ya mana hisaba, duk gudu d’aya lada goma , mugu kawai, fuskar ka fara amma zuciyar ka ba’kace kamar Diddigar gawayi “, Fanan kuwa d’an hararar sa tayi tare da barin falour, d’an fito Bobo yayi cikin Sauri Simba ya bar falourn sai a lokacin Eshaal ya fito daga bayan Bobo da ta ‘buya tana sakin ajiyar zuciya , itama Baby sai da ta ‘kara le’kowa ta tabbatar babu Simba tukunna ta fito daga bayan Sauban, ko kallan Sauban batayi ba Sabida bala’I ga idanuwanta da take hararar Little dasu kamar zasu fad’o ’kasa , “ Na gode “ cewar Eshaal tana juyawa , prince da Little kuma bayan Bobo da juya suka bi , shima Sauban Fasa shiga ciki yayi ya bi bayan Bobo.
Baby bata huce ba ganin Yadda Abla take ‘kumshe dariyar ta “ Zakiyi dariya da kyau ai , tunda kinsan d’an uwan nan naki mugu ne , kinga tafiya ta dan saura kad’an fıtsari ya ‘kwace mun a wando”, tana gama fad’ar hakan tabi bayan Fanan , a kan kujera Eshaal ta zauna kana kallan Abla “ Fanan fa ta sha’ka abunda d’an uwan ki yayi mata muma imani ne kawai ya shiga zuciyar mu “, ‘karamun murmushi Abla ta saki “ Karki damu Eshaal Indai Yaya Little ne zaku saba da wannan halin nashi , yanxu idan nace zan je wajan Fanan ma Baby sai ta sauke mun kwandan bala’in da yake kanta “ ta ‘karasa tana sakin dariya , itama Eshaal dariya ta saki tana tuno yadda Little ya saka su tsere a falour.
Kiran sallar La’asar da akayi ne Abla ta koma d’akinta , itama Eshaal ta wuce nasu d’akin. Tana shiga kuwa ta tarar da Fanan a gaban mudubi dariya ta saki ta furta “ Amaryar Yaya Little , ku kuma soyayyar taku da tseran zaki ta soma zuwa “, Baby da ta fito daga toilet dariya tayi itama “ kuma wallahi sunyi matching “, tsaki Fanan ta saki tana hararar su , a ‘kufule ta furta “ Allah ya sawa’ke nayi soyayya da yaro, Mtsww ni kun bani haushi ma “, ri’ke ’kugu Baby tayi kafun ta furta “ Ah’ah fa wallahi kar kizo kina mana kukan idan bashi ba sai rijiya , kuma wallahi namiji baya kad’an, tsaf ya aureki zama zakiyi ko kuma ku dunga tsere da zakin ku, Ina dalili “, wani pillow Fanan ta d’auka ta wullawa Baby, cikin Sauri Baby ta kauce itama “ Oho dai Matar yaro “, cikin jin haushi Fanan ta d’akko pillow zata jefa mata Baby ta ‘kara gocewa a haka suka soma yar tsere a d’akin.
********
************
HAJIYA SA’ADATU.
Zaune take cikin d’akinta sai yarta Yasmeen da wata Mata chocolate colour da ta zo mata , itama da kallo d’aya zakasan ba a wahala take ba , gabaki d’aya kwal ne a jikinta tundaga kan şarka da d’an kunne har zuwa abun ‘kafa da ta saka duk ta kwal ne , bakinta kuwa wani shegen cingum ne take taunawa sai faman bada saurin ‘kas ‘kas yake , ‘kara kallanta Hajiya sa’adatu tayi “ Yaya baki ce komai ba “, yatsina fuska wacce aka kira da Yaya tayi tana ‘kara tauna cingum d’in bakinta , sai da ta gama sham’kamshinta tukunna ta kalli Hajiya Sa’adatu “ Ai ni Sa’a kece kika gama bani mamaki, yanxu duk wata kıssa da kişisina na ‘ya mace baki sani ba? Bakisan yadda zaki ‘kwato wa kanki ‘yancı ba ? Anya ke yar gidan muce kuwa ? Ina bin malam da kike ? Duk a banza ? Ki kalli Yasmeen itama da tabi sahun ki babu wani mashin shini da zai dunga bata kud’i tana watayawa duk yadda take so , abun kunya kike san kwaso mana Sa’a ?” ‘Dan ajiyar zuciya Hajiya ta saki tana kallan yayar ta “ Yaya abun duk ba yadda kike Tunani bane , akwai yaran da yake so Yasmeen ta Aura amma shima shu’umun kansa ne dan ya keta miki rashin mutumci ba wani abu bane a wajan sa , abun takaicin kuma wai har yayi Aure?” Ya tsina fuska Yayar tata tayi “ Wanene wannan? Dan tun da kika kwallafa rai a kansa ba ‘karamin kud’ine dashi ba “, karaf Yasmeen ta kar’ba zancan “ Aunty ‘Dan Abbu da nake jin labarin su ? Süne da suka dawo kinga yadda suke da kyau Aunty, ga uban kud’i da suke dashi , musamman shegiyar matar sa da yawanci akwai sar’kar Diamond a wuyanta “, dakatawa Yayar Sa’a tayi daga taunar cingum d’in da take tana kallan Sa’a “ me take nufi ban fahimta ba ? Su wanene suka Dawo ? “, hararar Yasmeen, Hajiya Sa’a tayi ta ‘kasan ido kafun ta furta “ Ya.. ya … Yaya dama.. dama “, katseta tayi “Dama me ? Baki da bakin magana ne ko kuwa ?” Ajiyar zuciya ta sauke kad’an kafun ta furta “ Yayan Safreena ne “, da ‘karfi matar nan ta dafe ‘kirjinta “ Safreena fa kika ce ? Tabd’ijan Tashin hankali yana tunkaro wasu kenan “ sai kuma ta ‘kyal’kyale da dariya , kallan rashin fahimta Hajiya Sa’a tayi mata musamman data ga tana ‘ko’karin mi’kewa tsaye “ Ina zaki je kuma Yaya ?” Ba tare da Yayar ta kalleta ba ta furta “ matsalar ki ‘karama ce akan hutar guguwar da nake hango wa nan gama , zamuyi waya “. Ta ‘karasa tana d’aukar wayarta , wata number tayi dialing kafun ta furta “ Hello Hajiya ?” Da haka ta bar d’akin ta bar su Hajiya da sakin baki.