← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 100

Sashe 38

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da ta kuma ‘karewa kanta kallo sosai kafun ta d’auki mayafin kayanta daniyar yafawa , dai dai lokacin da shima yake shigo d’akin, tun daga nesa yake bunta da narkakkun idanuwansa , cikin Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa sabida yadda take jin idanuwan sa akanta , batasan lokacin da ya ‘karaso wajan ba sai ‘kamshin turaransa da ke tukan mata hanci gabaki d’aya sai kamshin jikinsu ya had’e ya ‘kara bada wani ‘kamshin ne sanyi da saka nutsuwa a cikin zuciya . Da hannu d’aya ya d’ago da ha’barta, cikin Sauri Abla ta runtse idanuwanta tana sauraran yadda bugun zuciyarta yake fitowa da Sauri da Sauri,tunda ya ‘kurawa fuskarta ido ya kasa janyewa kamar Wanda aka sawa magnet a jiki ta ko ina kallan fuskarta yake , sai da ya matso da fuskarshi Daidai saitin tata har suna sha’kar nunfashin juna kafin bakinsa da yayi masa nauyi ya iya furta “ öpen your eyes please “، kamar Wanda ya ‘kara zugata ta kuma runtse idanuwanta , cikin cool voice voice ya furta “ karki bari na maimaita! Okay “, fiki fiki Abla ta somayi da idanuwa kamar mara gaskiya da ‘kyar ta iya bud’e idanuwanta , ganin fuskarta daf da tasa yasa tayi saurin yin ‘kasa da fuskarta amma ya Hanata damar hakan. “ Baki iya gaisuwa ba ?” Rawa bakinta ya somayi sabida kusancin su, da ‘kyar bakinta ya iya bud’ewa zata gaishesu ya had’e lips d’insu, d’ayan hannunsa kuma ya tallafo ‘kugunta sai da ya shanye lipgloss din bakinta duka sannan ya sake ta yana runtse idanuwansa da suka soma canza ‘kala , d’an ’bata fuska Abla tayi ganin yadda ya göğe mata lip gloss d’inta , ta juya zata d’auko wani yayi saurin girgiza mata kai “ Bazai yi mana kyau ba!” Ya fad’a yana taune lips d’insa na ‘kasa , bata fahimci abunda yake nufi ba shiyasa ta bud’e zata kuma sawa ya kar’ba yana kuma girgiza mata kai “ ki bari duk lokacin da naga kinsa , you’re ready sai mu saka tare okay ?” Har yanzu Abla bata gane abunda yake nufi ba , kawai sai ta jinjina masa kai alamar toh, sarai ya fuskanci bata gane me yake nufi ba shiyasa ya ‘kara taune lips d’insa . Hannunsa d’aya ya saka ya ri’ke nata zuwa bedroom d’insa , sai da ya zauna tukun na ya saki hannunta “ am hungry” ya ‘kara shima yana langwabar da kansa kamar little , cikin sauri Abla ta d’auke fuskarta . Tuna’nın yadda zata yi serving d’insa sosai take shiyasa ta sakko da Kayan kan rug. Da mamaki ya ke kallan abunda take ‘ko’karin yi cikin Sauri ya furta “ Rug ? Me ? Naci abinci?”, da mamaki Abla take kallansa jin abunda yace “ baka so?” Kansa ya d’aga mata a sanyaye ta mi’ke zata kwashe kayan ya kalleta “ anan kike san cin abincin?” Yanxu ma kanta Kawai tayi knodding bata dena ‘ko’karin d’auke tray dinba . Sakkowa yayi shima cikin Sauri Abla ta kallesa da mamaki “ zan akai mata kan dinning ne “ Nop nan ma yayi “ cewar sa , d’an ‘karamun murmushi Abla tayi , cikin nutsuwa ta soma serving d’insa, bai ce mata uffan ba har ta gama , zata mi’ke ya nuna mata laps d’inta alamar ta zauna , cikin zaro ido Abla ta soma kallanta , “ na zuba maka abincin fa “ da katar da ita yayi ta hanyar furta “ I know ! Just do as I said kafun bride tazo “, yana ambatar bride Abla ta kawar da kanta ‘kasa , bata zauna a cinyar saba sai tayi zaman ta a ‘kasa “ ka bari duk lokacin da tazo sai ta zauna na yafe “, da Sauri Big Boss ya kalleta jin abunda tace gashi ko kusa ta’ki yarda ta d’ago face d’inta balantana ta kalli fuskarsa, duk yadda ya so su had’a ido ta’ki barin hakan. “ Am hungry” ya fad’a har yanxu yana so ta d’ago face d’inta , abincin ta kalla , kafin ta saka hannayenta biyu ta matso masa Dashi gabansa , zata d’auke hannun ta ya ri’ko hannun, kallan da Abla tayi masa ne yasa ya lumshe idanuwansa yana ‘kara bud’ewa “Are you jealous?” Kanta Abla ta girgiza masa “ No “ kansa ya Jinjina “ I will see ! Lokacin da Wifey tazo…” d’an kallansa tayi da fararan idanuwanta a karo na biyu kafun ta mi’ke tana d’aukan tray d’in da ta shigo dashi, “ we’re are you going ?” Tray d’in hannunta ta nuna masa kafun ta furta “ Naga ka damu da wifey d’in taka shiyasa na baku space “bata bashi space d’insa da zaiyi magana ba ta bar d’akin , a hankali ya furt “ She looks more beautiful when she’s jealous!”. 

Abla tana koma wa kitchen ta tarar da Jenny ta ‘kara tsaftace komai ga uban alayyahun da ta gyara “ Weldone jenny na barki kina ta jira ko ?” No madam kawai banaso kizo ki tarar da aiki da yawa shiyasa ,  “ Thank you jenny but zanyi ero riro ne first, help me with a hot water please “ cewar Abla da Sauri jenny ta kunna heather d’in ruwan zafi , gabaki d’aya sai da ta fito da kayan cikin da take bu’kata, Ganda , nama, bushash shen kifi da normal kifi babu Wanda bata fito dashi ba , jenny babu abunda take sai bin komai take da kallo tun kafun tasan ne za’a dafa sai faman had’i yar sliver take. Sai data kuma wanke hannunta da soup don hannu tukunna ta soma temakawa Abla duk da ba wani abun tayi ba sai mi’kowa Abla kaya da take, komai Abla ce takeyin kayanta, cikin ‘kan’kanin lokaci ko ina ya çıka da ‘kamshin miyar Efo d’insa Abla , dan baza’a kira ta da Efo kai tsaye ba sai an had’a da rich Sabida yadda komai yaji , ko kallanta mutum yayi sai ya wunka ya tsotse . A ‘katuwar pot d’in da tafi ko wacce girma Abla tayi . White rich d’inta data ji’ka ta d’ora shima cikin pot me d’an girma, sai da ta tabbatar da komai yana tafiya normal kafin ta d’auko kayan had’in zo’banta da already ta ji’ka ga kayan ‘kamshi da ta saka a ciki, tun kafun kad’an d’ana zo’ban zai burgeka sabida yadda ‘kamshin ginger da na’a na’a ya cika ko ina , a tsaftace ta gama had’a zo’banta me d’an karan dad’i , cikin dogon jugs ta zuba guda uku, sai bottles d’in da ta d’auka guda goma sha biyar ta d’ura a ciki ragowar kuma ta zubawa Jenny da M.Sarah suma nasu, Jenny sai faman washe baki take tana yiwa Abla Godiya . Tuwan Abla nayi ta. Mulmulasu ta saka cikin manyan warmers suma guda uku, the same thing ta ajje wa su M.Sarah nasu, “ Madam You’re super awesome Mah, ina jin dad’in zama dake sosai like my elder sister “ d’an hararar ta Abla tayi , sai da kika girme ni tukunna zaki ce mun elder ? Cut it off santi kike “ dariya Jenny tayi , she don’t know why but tana san Abla sosai musamman yadda take kyauta ta mata shiyasa tayi wa kanta Al’kawari ko me Abla take so zatayi mata and she will protect her with all she have . Raba warmers d’in tayi gida uku, ko wanne da set d’insa da zobansa, na farkon cikin sa akan dinning ta ajje bayan ta d’auki wani a cikin medium warmers ta kai bedroom d’inta , hatta zoban bottles d’inta gabaki d’aya ta jerasu cikin fridge yadda zaiyi sanyi sosai, sauran warmers d’in a cikin jakar zuba abinci ta ajjesu sai zo’bo da suka ajje daban, kallan jenny Abla tayi “ jenny we have to divide our self , Wannan na kusa da ke kikai part d’in Diidii, when she asked you kice Yaya Big Boss ne yace akawo mata okay?’Ni kuma zanje part d’insu Little okay ?” But Mah basuyi nauyi ba kuma ?” Don’t worry Wannan ba me wahala bane ! “ but am coming “ ta ‘karasa tana barin Wajan , d’akin sa ta shiga yadda taga light so dum tasan bacci yake shiysa tayi saurin komawa bayan ta rufe masa door a hankali . 
Chapter 38 · 0% Book details