← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 100

Sashe 39

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ‘kar suka iya d’aukan kayan dan ba ‘karamin nauyi ne dasu ba , suna fitowa Victor da Anthony suka yi saurin kar’ban kayan , cikin tsananin mamaki Abla take bun simba da kallo duk da alama ya nuna bacci yake “ No wonder ! The Evil bata shigo ba , Aushe Simba ne ya ‘karaso, teacher d’in ku ya zo “, ta ‘karasa tanayin dariya ‘kasa ‘kasa cikin zuciyarta. Anthony bin bayan Jenny yayi , Victor kuma yabi bayan Abla kansa a sunkuye ko kallan direction d’in da take bayayi, kai tsaye part d’in His excellency Abla ta nufa , ba ‘karamun mamaki Abla tayi ba data ga ko ina shiru duk da tasan zuwan simba ne ya hana kowa na cikin gidan futowa . Falourn ‘kasa babu kowa sai Little da prince da Suke game , Abla na ganin su ta d’auke kanta da sauri little ya ‘karaso Inda take “ We’re sorry Lil , karkiyi fushi mana , we’re so so sorry dear “ kallansa Abla tayi “ gabaki d’aya kun dena soma bana ganin ku ko ? Fine thank god simba ya zo sai nasa yayi gunduwa gunduwa da namanku “ gabaki d’aya dariya sukayi little har da kama kunnansa “ We’re so sorry Aunty Little mun dena “, ya ‘karasa yana Kallan jakar hannun Victor “ and what’s this da naji yana ta ‘kamshi ? “ hannu Abla ta d’aga amsa alamar itama bata sani ba , da Sauri prince ya ‘karbi jakar , little kuma ya ‘kar’bi zo’ban “ yaya little nasan bamu ta kawo wa ba but baza’a ciki babu mu ba ko ? Let’s go Lil “, cikin Sauri Abla ta girgiza musu kai “ No basai na shiga ba “ hannun ta little ya kamata “ Allah sai kin shiga babu kowa a ciki sai su uncle fa , just let’s go” zata langwa’be musu little yayi saurin furta “ No more excuse Allah sai kinje “, babu yadda ta iha dole tabi bayansu, babu kowa a cikin ‘Kayataccen falourn da mutane guda uku, His excellency sai uncle da kuma uncle Adams , shigowar su little ne yasa gabaki d’aya suka d’ago suka kallesu, Abla ma cikin sunkuyar da kai ta shigo falourn , tashi zaune His excellency yayi daga kwancen da yake uncle da uncle Adam ma sai bunsu da fara’a Suke , cike da girmamawa Abla ta gaishesu hanta a ‘kasa , murmushin manya His excellency yayi yana kallan yadda take sun kuyar da kanta ‘kasa , jakar hannunsa prince ya nuna musu “ Friend , uncle just for you “ d’an waro ido his excellency yayi yana kallanta “ Dagaske ? Sun kuyar da kanta Abla ta ‘karayı shima uncle murmushi yayi “ finally yau Zamu kuma cin abincin queen chief amma ki tattara brothers d’inki kice musu bamasan ganin su “ Prince har da gyara zama “ Allah uncle babu Inda zani fa” daman yasan ko kowa bai tankaba prince sai ya tanka , cike da jindad’i his excellency yace prince yayi serving dinsa , tun kafun ya fara serving dinsa suke lumshe ido, gabaki d’aya miyar ta d’auki hankalin su , har ‘kasa kan rug His excellency ya zauna batare da nuna shi wani bane ya soma cin abincin sa hankali a kwance , kunya hakan ya bawa Abla tayi musu sallama zata tafi His Excellency yayi mata murmushi “ Naji dad’i sosai da sosai , thank you daughter, me kike so? Fad’i ko menene “ cikin Sauri Abla ta girgiza kanta “ Yaya Big Boss ne yace akawo”, babu Wanda bai kalleta ba jin abunda tace , His excellency har murmushi me sauti sai da yayi da ya bawa kowa mamaki, irin murmushin jin dad’in da ya dad’e beyi ba , har yanxu farin cikin fuskarsa ta kasa ‘boyuwa ya kalli uncle Adam “ from now on she’s the queen lady! Everything she wants ayi mata shi” shima uncle murmushi yayi “ gaskiya ta cancanci zama queen lady of the family “ bai kai ga ‘karasa maganar saba His Excellency ya furta “ from now on she’s the chief leader of the family , duk masu kula da abincin suna under her control  . “ Abla kasa magana tayi sabida tsantsan mamaki, ta rasa gabaki d’aya abun cewa , zatayi magana His Excellency ya girgiza mata kai “ you’re also my daughter, karkice komai, you make me happy to day , thank you so much”, Abla babu abunda take sai girgiza kanta sabida mamaki da Al’ajabi, uncle shima jinjina mata kai tayi  amma duk da hakan Abla sai da tayi masa Godiya Sabida yadda taji kuka na ‘ko’karin zuwar mata , Daidai flower base d’in ‘kofar da zata fita ta d’an şaka hannu ta türe ta ba tare da kowa ya kula da hakan ba sai jin ‘karewar fashewar ta , cikin Sauri Abla ta fad’a kan abun kamar wacce ta bige da gaske , farin abun da ta gani da aka tsire da allurai tayi saurin ri’kewa da hannunta , Daidai lokacin da Little da su prince suka yo kanta , Shima His excellency yana ‘ko’karin mi’kewa Sarawan da kansa yayi masa da azabar ‘karfine yasa ya dafe kan yana ambatan “ INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN” hannayen sa guda biyu duka dafe da kansa.

IBTISSAM
      ( A heart touching story of love and destiny)

Story & written 
      By
Mss Lee   

                     09134652921

    TALLA!! TALLA!!! TALLAH !!!!!!!

SHIN KUNSAN WACECE HAJIYA NUSAIBA BR~B ZURU ?❤️

HAJIYA ~ NUSAIBA DR~B ZURU

MAMALAKIYAR ZIMH ISLAMIC AND MEDICINE DAKE RINGH ROAD A KANO NIGERIA
Tazo muku da ingantattu ko sahihan magungunan mata masu inganci, ba’anan kad’ai ta tsaya ba har da na cututtuka da Turarukan wuta , Humra masu shegen ‘kaushi . Abun Alfaharin kuma tana bada sarı cikin sau’ki, sannan kuma suna aikawa duk inda mutum yake afad’in duniyar nan. 

Duk wacce ta siya magungunan Hajiya Nusaiba Dr B zuru, taga be yi mata aiki ba tazo za’a dawo miki da kudin ki . 

KA’DAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKE SIYAR WA

1️⃣ Hadin amarya
2️⃣Hadin mai jego
3️⃣Hadin sabon budurchi
4️⃣Hadin Kaza Yar’Suddan
5️⃣zuma -Tsumi- Tabaje da sauransu
6️⃣Turaren Sandal ruuu& flastic Sandal
7️⃣ Hadin Hawwi domin inganta zafafiyar kauna
8️⃣Hadin bagadad,kahlij,kajiji,gafgaf dasauransu
9️⃣Hadin humra soyaya dole ta matan aure da normal humra

DON SAMUN ‘kARIN BAYANI KU NE META TA WANNAN NUMBER KAMAR HAKA : 
    08133647913 

   KANO NIGERIA 

LOCATION: RING ROAD BAYAN GİDAN MAN NAZARGO.

       SIYAN NAGARI MAIDA KU’DI GIDA

PAID BOOK

BOOK 2 
         S_____ 13

Da sauri uncle dake gefen sa ya zaunar dashi har lokacin hannun sa dafe da kansa babu abunda yake iya nanatawa sai “Innalillahi wa ‘inna ilaihi raji’un”. Abla da ke du’ke a ‘kasa Prince da Little suka temaka mata ta mi’ke sai faman taune bakinta take da ‘karfin gaske ga fuskarta da take faman yin gumi ta ko inq , gabaki d’ayansu kallan His excellency sukai ganin yadda yake dafe kansa da yake mugun sara masa , Little da Prince da Sauri suka ‘karaso Inda yake , Abla kuwa mamaki da tsoro ne ya kamata ga hannunta da take ji kamar ana kona mata shi da garwashi babu abunda zuciya da gangar jikinta yake anbato sai sunan Allah . Kallan su Prince Uncle yayi da Sauri ganin yadda lokaci d’aya suka tayar da hankulansu “ ku kwantar da hankalin ku , okay ? Babu abunda zai same sa “, Da sauri Little ya furta “ But uncle me ya same sa? “ His excellency najin muryar Little ya d’ago da face d’insa cikin sauri , wani irin lallausan murmushine ya su’buce masa duk da har yanzu hannun sa d’aya na dafe da kansa, da hannu yayi musu alamar su zo , babu musu kuwa gabaki d’aya suka taho Wajan sa “ karku damu, ba wani abun bane, Hutu Kawai nake bu’kata okay ? It’s just a minor thing ,okay ?”cike da d’an damuwa Little ya furta “Every time friend kana aiki , just for today ka huta mana , atleast karka fita yau , kayi zaman ka a gida kayi bacci”, da murmushi akan face d’in His Excellency ya furta “ Wannan ne abunda friend yake so ? “ shima kansa little yayi knodding kafun ya furta “ yes.”hannun Little ya kama yana mi’kewa tsaye duk da yadda yake jin kansa na sara masa hakan be hana ya danne ba “ it’s okay tunda Hakane , let’s friend accompany me okay ?” Cikin gamsuwa prince ya furta Okay shima “ kafun ya koma d’aya side d’in His Excellency suka nufi wani d’an corridor . Tunda Suka bar wajan Uncle Adam da Uncle suke sakin murmushi , cikin jin dad’i Uncle Adam ya furta “ Allah ya hana kawunan su, Allah yasa komai ya zo cikin sau’ki “ Amin uncle yace shima har lokacin murmushin fuskarsa be d’auke ba , cike da girmamawa Abla ta juya zata ta’ba kayan flower base d’in da suka fashe uncle yayi saurin dakatar da ita “ No! No ! Daughter , karki damu za’a zo a kwashe ba sai kin wahalar da kanki ba , Allah yayi Albarka daughter “, d’an ‘karamun murmushi Abla ta saki cikin ‘kasan zuciyarta kuma ta amsa sa “ Amin”, komai cikin ‘karfin hali take yinsa , tana sakkowa ‘kasa Abla ta runtse idanuwanta sabida yadda suke mugun yi mata zafi, kallan hannun da ta ri’ke layar tayi gabaki d’aya yayi ja hannunta har ya fara kunbura kamar wacce tayi taruwar jini a hannu, ita kad’ai sai faman taushe lips  d’inta take sabida ‘karin zafin da take ji fiye da na d’azu , cikin sauri ta bar falourn ta fito daga cikin part d’in. A waje ta tarar da Jenny bata tsaya yi mata magana ba tayi gaba itama jenny tabi bayanta , duk yadda taso tayi magana da Abla sai ha’kura tayi ganin lokaci d’aya kamar mood d’inta ya canza zuwa na mara lapiya . Amma duk da hakan bata ce mata komai ba a tunaninta aikin da sukayi ne yasa ta gaji da wannan Tuna’nın ta kawar da komai na ranta.
Chapter 39 · 0% Book details