← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 100

Sashe 96

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

   Ya dad’e yana operating System d’in gabanta , time ya kalla yaga har past 9, kallan ‘bangaran da take bacci hankali kwance yayi kafin ya kashe system d’in gabaki d’aya yana barin d’akin. Fitar sa ba dad’ewa Abla ta farka daga baccin da ya d’auke wa , mi’ka tayi sosai dan ba’karamun Jin dad’in baccin tayi ba . Wanka ta somayi tare da shiryawa cikin wani material me shegen kyau riga da wando maroon colour sai mayafinsa da ta d’aura akanta , tana cikin fesa turare ya shigo d’akin shima cikin shigar fararan ‘kananan kaya da alama favorite colour d’insa ne sabida yadda komai nashi yake da white , ajje turaran tayi tana sakar masa murmushi “ Good Morning Sunshine “, har kin tashi daga baccin ? Ya katse ta lokacin da yake ‘karasowa inda take , kanta Abla ta jinjina masa tare da juyowa tana kallanta “ Sorry Sunshine bari ma fara kawo mata coffee kafun nayi mana breakfast”, hannunta ya kama “ You’re not allow to do anything , ko bana nan ban amince ki d’auko koda Youghurt bane a fridge sai dai a d’akko miki, understood ?” Cikin marairaice fuska Abla ta furta “ Sunshine” shima kallanta yayi in a serious turn ya furta “ And I mean it , okay ?” Ganin da gaske yake yasa Abla ta furta “ Okay” sakin face d’insa yayi tare da kama hannun ta , “ let’s go and eat, kafun mu tafi “, Abla har tana murna da yaji yace zasu tafi dan gabaki d’aya Tuna’nınta ta d’auka gida zasu tafi . Suna sakkowa ‘kasa basu tarar da kowa ba sai tashin ‘kamshi da ko ina yake , kai tsaye dinning suka nufa da kansa yayi serving d’inta , shi da kansa kuma ya soma bata a baki sai da ya tabbatar ta ‘koşhi tukunna ya ‘kyaleta. Itama spoon ta d’auka zatayi serving d’insa ya girgiza mata kai “ Am fasting “, Abla kamar zatayi kuka ta furta “ Shine nima baka fad’a mun nayi ba?” Shiru Big Boss yayi mata ba tare da ya amsa matan ba , yau ta fahimci da izzarshi ya tashi, bata kuma cewa komai ba ta mi’ke zata d’auki plate d’in yayi saurin dakatar da ita , sai hannunta da ya kama suka koma d’aki. 

    Sai da suka d’auki good 2 hours ya tabbatar abincin cikinta ya lafa tukunna ya d’auko wasu coat masu kyau black colour ya saka mata d’aya tare da saka d’aya shima , da mamaki Abla ta furta “ Bana jin sanyi fa “, shima Big Boss kai tsaye ya bata amsa “ zamuji sanyin ne , no more questions,just do everything I asked you to okay ?” Kamar wata Baby Abla tayi knodding kanta tana furta “ Okay” , bed side d’in gadon ya bud’e sai ga wayanta nan, Abla har da d’an sakin ajiyar zuciya Sabida kwana d’ayan nan da tayi bata ga su Eshaal ba har tayi kewar su , dad’inta d’aya da tasan yanzu zasu je gidan.

    Suna fitowa gabaki d’aya sojojin sukai musu combo daidai motar tsaki Victor yazo zai bud’e Big Boss yayi masa signal ya barshi, hakan ne kuma ya faru dan dakanshi Big Boss ya bud’e Sunshine d’insa mota , suna shiga Victor ya shiga cikin motar shima , cikin ‘kan’kanin lokaci motocin suka tafiya cikin street din waje da yake sha’ke da sojojin kafin su hau kan babban titi. Allah sosai ta matsu su koma gida dan gani take kamar motocin basa Sauri , tsafff kuma Big Boss ya Lura da Ita amma bai ce mata ko uffan ba , tun tana Tuna’nın isowa gida har ta soma hamma , basu ‘kara tafiyar mintuna goma ba suka iso Murtala Muhammed international Airport, Abla bata ankara da inda suka zoba sai da suka fito daga cikin motocin , kamar zatayi kuka ta kallesa amma ganin yadda ya d’aure face d’insa sosai ne yasa tayi shiru sai fiki fiki da eyes da ta soma kamar zatayi kuka , kasancewar ta wani hanyar suka bi daban yasa suka wuce babu mutane, Daidai inda plane d’insa suke sojojine birjik a Wajan , hannunta ya kama suka shiga wani part a cikin jirgin daban yayinda , inda Suka shiga kamar falourn ne da d’aki a ciki, akan gadon ya kwantar da ita, har yanzu bai saki face d’insa ba gashi itama tayi masa fiki fiki da ido , a hankali Abla ta furta “ Sunshine” sai a lokacin ya kalleta , zatayi magana ya saka mata hannu akan lips d’insa “ Don’t say anything, am your husband, you know I won’t hurt you ko ?” Cikin Sauri Abla ta jinjina masa kai “ Fine bari na cire miki coat din ki sai ki kwanta kinji “, yanzu ma da kai ta amsa masa kafun ta furta “ Ina zamuje ?” Kai tsaye Big Boss ya bata amsa da “ America” ita kanta tayi mamakin American da yace , ji tayi kamar zatayi kuka gashi babu wanda ta gani a cikin yan gidan tun jiya , ya kula da sudden change d’inta amma bai kulata ba , ya cire mata coat d’in, kamar kuwa yasan baccin take ji, cikin ‘kan’kanin lokaci tayi baccin ta bayan ta gama kunbure kunburenta. Saida ya tabbatar tayi bacci tukunna ya saki face d’insa “ Stubborn kawai”, Big Boss bai bari jirgin ya tashi ba sai da ya tabbatar da baccinta yayi nisa sosai tukunna ya bada umarni , har jirginsu ya tashi zuwa America Abla bata sani ba Sabida yadda baccinta yayi nauyi.

******************
    Tun safe su Baby suka kwada kiran Abla awaya amma basa samunta, tun sunayi har suka ha’kura , Fanan ce ta furta “ nasan duk lokacin da ta d’auki wayar zata kira mu , or may be ma muganta sun dawo” gabaki d’aya sun yadda sa magan ganunta shiyasa suka share zancan, Baby duvet ta ja tana ‘ko’karin komawa bacci , itama Fanan still abunda tayi kema , mi’kewa tsaye Eshaal tayi zata fita Baby ta furta “ Ina zakije ?” Kallanta Eshaal tayi kafun ta furta “ Yunwa nake ji, zan ci wani abun ne kafun na kwanta ,” kanta Baby ta jinjina mata tana shigewa duvet bayan sun ‘kore ‘karfin Acn, Eshaal tana fita kitchen ta wuce direct dan tun d’azu take jin yunwa yau , tea kawai ta had’a sai bread da d’auka shima slice biyu, akan dinning ta zauna tasha tea d’in ta sai da ta gama ta wanke cup din da ta ‘bata tukunna ta fito daga kitchen d’in, Eshaal ba ‘karamun tsorata tayi ba ganin Bobo a tsaye kamar daman jiran fitowar tata yake , cikin rawar murya ta furta “ Ina kwana ?” Bai amsa mata ba şai
binnta da kallo da yayi “ Nazo kar’ban amsata “cewar Bobo yana tsare ta da idanuwa, da Sauri zuciyarta ta soma gudu, kanta ta sunkuyar ‘kasa tana wasa da fingers din hannunta , shima bai ce mata komai ba sai binta da kallo da yayi yana jiran amsar ta. “ Fine tunda bazakiyi magana ba let’s all sit here idan Uncle ya fito sai na tanbayi auranki gabaki d’aya “, cikin Sauri Eshaal ta d’ago ta kallesa , ganin yadda ta soma diriricewa ne ya furta “okay , bazan ba sai da amincewarki, kinsha mun sweet kin’ki bani amsa ko sai nq fad’a da baki na ?it’s okay, bari na sake , ganin kamar zaiyi kneeling Eshaal ta furta “ No please “,kallanta Bobo yayi kafin ya furta “ No me ? Ba kyaso na fita yau kenan ? And da alama kema bacci kike ji, duk da hakan babu Wanda zai tafi sai kin bani amsa , Eshaal “ ya kira sunanta , a hankali ta amsa da “Na’am”, shiru Bobo yayi sai kuma ya furta”Zaki iya soyayya da Abdul_Maleek? Zaki iya zama abokiyar yaruwata ? Zaki kasance tare da nayi as your life partner ?”, yanzu kam sosai jikin Eshaal ya soma rawa jin abunda maganganunsa “ karkiyi shiru please say something,  Will you ?” da ‘kar Eshaal ta iya furta “ Yes a hankali tana sunkuyar da kanta ‘kasa , sosai Bobo yayi murmushi kafun ya furta “ Please Mrs Abdul_Maleek Bobo d’ago da kyakkyawa face d’in ko saurayin ki zai kalla yaji dad’i , cikin Sauri Eshaal ta güdü zuwa d’aki tana rufe face d’inta , shima murmushin yake yi bai fita daga cikin falourn ba sai zama da yayi , Eshaal kuma tana shiga d’akin fad’awa kan gado tayi har Fanan tana farkawa daga barci kamar wata zautacciya ita kad’ai sai sakin murmushi take tana ‘boye face d’inta , wayarta ta kalla ganin message ya shigo “ You look so beautiful when you’re shy Mrs Bobo”. Aka ‘karasa message d’in tare da wasu red heart,kamar yana ganinta ta saka hannu ta kulle fuskarta , baccin da bata koma ba kenan, Bobo ma ya dad’e a falourn da ‘kyar ya iya ha’kura Sabida wajan da yake san zuwa mai muhimmanci. 
Chapter 96 · 0% Book details