← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 100

Sashe 13

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Gabaki d’aya cikin daran nan Big Boss bai runtsaba Sabida yadda Abla take masa kuka har wajan sallar Asuba tana rungume a cikinsa , sai a lokacin ta soma a jiyar zuciya alamar zatayi bacci ga kiran sallah da’ ake faman yi , kallan kyawawan eyes d’in ta da suka kunbura yayi , face d’in ta har ya soma yin ja , mayar da idanuwansa yayi kan phone d’insa da take ta haske tun d’azu yayi , batare da ya d’auka ba ya kwantar da Abla a hankali, kai tsaye toilet ya nufa cikin ‘kan’kanin lokaci yayi Wanka tare da d’auro Alwala , yana fitowa ya tarar da ta canza yanayin kwanciyar ta , gashi kamar bata jin dad’in kwanciyar da tayi . Cikin wasu white Gucci d’in kaya ya shirya , yana ‘ko’karin barin d’akin Abla ta bud’e idanuwanta a zabure kamar wacce aka tsikara , ganin yana ‘ko’karin fita ne ta kulle idanuwan ta da duka hannun ta tana kuka , d’an kallanta yayi kad’an tare da kawar da kansa Sabida kukan ta da yake ci har cikin zuciyar sa , a hankali ya tako zuwa inda take gabaki d’aya face d’in sa ta sauya , hannun sa d’aya ya mi’ka mata ,cikin sauri ta ri’ke nasan tana mi’kewa “ Me akai miki?”d’an turo masa lips Abla tayi, cikin sauri ya kawar da kansa daga lips d’inta “ karka tafi “, kamar Wanda aka sa dole ya furta “ Sallah! Ki zauna I will be back….” Bai ‘kara saba Abla ta ‘kara sakar masa kuka cikin Sauri tayi hugging d’insa , “ ina jin tsoro”, gabaki d’aya Abla ta’ki bari ya fita sabida yadda ta soma zabura , Da kanshi ya rakata toilet tayi alwala, dole sai a d’akin yayi sallah shima kansa har ya soma sara masa , tana idar da sallah ta soma hamma zata kwanta a kan dadduma, gabaki d’ayan ta ya d’auketa tare da kwantar da ita kan bed , yana ‘ko’karin tashi Abla ta ‘kara rungumeshi, d’an ’karamun murmushi da ko le’ben sa bai gama hawa ba yayi tare da kashe light d’in d’akin zuwa mara haske sosai, da hannu d’aya ya zame mata gabaki d’aya rigar jikinta yayi saura black bra d’in da ta saka sai pant din jikinta ,ganin rip d’in rigarsa na ‘ko’karin damun ta shima ya cire white shirt d’insa ya bar black singlets d’in sa , sosai yayi hugging d’inta a jikinsa , cikin Sauri ya runtse idanuwansa Sabida yadda yake jin tudun breast d’inta akan ‘kirjinta. Yafi tsawan 15 gabaki d’aya ya kasa runtsawa sabida body contact d’insu , face d’inta ya d’an kalla kad’an ganin yadda ta ‘kara turo lips d’inta waje , har shansa ya d’an tauna kad’an yana kawar da kansa gefe , saida ya d’auki wasu minutes d’in kafun bacci shima ya d’auke sa .

*****Mamaki ne ya kama Bobo ganin har yanzu Big Boss bai fito sallama , gashi yana kiran wayar sa amma har yanzu baiyi picking ba “ Something is wrong “ ya fad’a cikin zuciyarsa kafun ya kalli agogon hannunsa, ta’bashi da Little yayi ne ya dawo dashi daga tunanin da ya fad’a “ Yaya har yanzu yaya Big Boss bai fito bafa , ko naje d’akin sa ?” Cikin sauri Bobo ya furta “ No! Karka damu he’s alright,okay ?yanzu idan kaje kasan time d’in baccin sane and nasan yayi sallah tunda bai fito ba , just ka kwantar da hankalin ka “, Little sai sake magana Bobo ya furta “ No more questions, am going out now, dont be stubborn okay?” Kansa ya jinjina masa yana d’an kawar da kanshi gefe , Sauban ne ya d’an sakar masa murmushi tare da janyosa suka soma tafiya “ you also have me , lets go somewhere else okay ?” Cewar sauban lokacin da ya ja hannun Little , prince ma bin bayansu yayi. Wayar hannun sa Bobo ya kalla kafun ya kalli time “ Something is wrong”, zuwan Victor wajan ne yasa Bobo ya kallesa , d’an sara masa Victor yayi kafun ya matso daidai kunnan sa ya fad’a masa wata magana da babu wanda isa jin me yake cewa . ‘Dan ‘karamun murmushin gefen baki Bobo yayi kafun ya kalli victor “ Good job, let’s go “ da haka su Anthony suka fito da manyan black tinted cars guda uku , motar tsakiya da ta fita daban Anthony ya shiga bayan victor ya bud’e masa seat d’in baya, suma ragowar sojojin su motocin suka shiga ko wannan su sanye cikin black suit. Victor bai bisu ba sai sara musu da yayi har saida ya ga motocin su sun ‘bace kafun shima ya bar wajan.

***** Direct har falourn His Excellency ya nufi da su Little , yana kishingid’e akan kujera mai mazauni mutum biyu , sai Babbar 4 sitter da Uncle Adam yake zaune tare da wasu maza guda uku akanta , a one sitters ma , wasu mazane akan ta ko wannan su da shigar alfarma da alama tattaunawa suke. His Excellency yana kallan su Little ya lumshe idanuwan sa tare da bud’e su akan su, shima little tsaya kallan sa yayi har suka ‘karaso cikin falourn, kamar bazai yi magana ba sai kuma suka bud’e baki suka gaishe su sama sama , da hannu Sauban ya nuna His Excellency,” Sunan shi Abbu, you can all called him with that name “, cikin sauri prince ya furta “ Why ?”, kai tsaye sauban ya furta “ He’s like the father of the family, nima He’s a father to me , and he can be a father to you all”, cikin sauri prince ya girgiza masa kansa “ No ! He will be our uncle , We dont need a father , Yaya Big Boss is our father and mother right little ?” Wani irin sha’kuwane ya kama His excellency, lokaci d’aya ya dunga yin ta ba ‘ka’k’kau tawa , Little da prince basu san lokacin da suka ‘karasa wajan saba , cikin sauri Little ya soma tapping d’in bayansa “ Sorry” cewar prince , gabaki d’aya sai suka tsaya kallansu banda Sauban da yake sakin murmushi jin dad’i, a hankali His excellency ya d’ago da fuskarsa me cike da dattako ya kalli prince da little , “ Me yasa bakwasan Abbun ku?” Ba tare da wani damuwa ba prince ya furta “ sabida muma bayasan mu and we will never love him, he distanced his self from us ,” shiru Little yayi wa prince sai His excellency da yake kalla face d’in sa cike da murmushi ya furta “ kai ma baka murmushi kamar Yaya Big Boss , inka lumshe idanuwanka sai naga kamar  Yaya”, sai a lokacin His excellency ya saki wani murmushin manya “ Amma kuma shine kuka ce ni ba Abbun ku bane ? Ko sabida kunga yayan basa kulani?” A wannan karan little ne ya girgiza masa kai “ No! Yaya baya fushi without a reason, May be ka ‘bata masa rai ne amma if you apologize to him zai ha’kura musamman haka “ ya ‘karasa yana ‘kif’kiftawa His excellency ido. “ Tom shikenan , Na gode zanyi nima hakan amma tunda bazan zama Abbun kuba zan iya zama friend d’inku?” Yar ‘karamar dariya little yayi zai ce masa No shima His excellency yayi masa fiki fiki da ido kamar yadda yace , wani irin dariya prince da little suka sa lokaci d’aya , har yanzu Little bai dena dariya ba ya furta “ shikenan ka zama friend d’in mu “ Amma kunsan friends suna bacci tare , suna cin abinci tare , suyi hira tare , kunyi al’kawari anytime nake free zakuzo?”hannunsa Prince ya bud’e tare da furta “ we promised!” Hannayensa biyu His excellency ya bud’e musu kafun ya furta “ A hug for a friend please “, gabaki d’aya hugging d’insa sukai suna furta “ friends “, da hannu His excellency ya nuna musu su Uncle Adam da suke zaune sai kallansu suke cike da burgewa kowa face d’in sa murmushi ne akai , Uncle Adam ya fara nuna musu kafun ya furta “ His uncle Adam, yaya nane, sai kuma na kusa da shi Uncle Abbas shima yaya nane , na ‘karshen su kuma Anas sai kuma , Munnir da ‘kasim, and my other younger Brother Isma’il ya mutu long time ago” cike da pity face Little ya furta “ Allah ya ji ‘kansa “ gabaki d’aya suka amsa da Ameen. Ganin mood d’in kowa yana ‘ko’karin canzawa ne sauban ya nuna musu dinning, “ food is ready ya kamata yau friends suci abinci a tare , okay ?” Kamar yadda ya d’aga 3 fingers d’insa haka shima Little ya d’aga “ okay “  a haka suka nufi dinning d’in gabaki d’ayansu, masu aikin zasu fara aikin serving d’in su Little ya dakatar dasu “ No zanyi , ku barshi” d’aya daga cikin su zaiyi magana His excellency ya d’aga masa hannu, cikin girmamawa suka bar wajan. Warmer d’in wajan little ya soma bubbud’ewa kafun lokaci d’aya ta’be bakinsa ,”Yaya sauban mu canza abinci mana , ko friend?” Fuskar His excellency cike da annashuwa ya furta “ Anything you like “ Uncle Adam zai yi magana His excellency yayi saurin da katar dashi, “Bari a yi serving d’inku, we will eat another food “. A karo na biyu shima Uncle Abbas zaiyi magana His excellency ya furta “ My order ! Sauban akawo abunda sukeso” da haka ya mi’ke daga kan dinning d’in shima sauban ya bi bayansa sai prince da little ne suka tsaya suka fara serving d’insu kafun su dawo falourn suma. 

**********
Chapter 13 · 0% Book details