← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 100

Sashe 41

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

‘Karfe 3:10pm Abla ta farka daga baccin da ya d’auke ta , mamakine ya kamata sosai ganin ta kwance tana bacci , d’ayan side d’in ta takalla ganin baya wajan . Cikin Sauri ta kalli hannayenta ganin wanda ya washe cikin ‘kan’kanin lokaci . “ Su wanene suke san cutar damu? Me yasa mafarkin da nayi ya zama gaskiya ? Laifin me mukai musu ?” Shine abunda Abla take maimaita wa cikin zuciyar ta , ganin tana ‘ko’karin sawa kanta ciwan kai yasa ta ajje gabaki d’aya tunanin komai a gefe . Bata bar d’akin ba sai da ta gyara ko ina na cikin bedroom d’in. 

   Tana shiga cikin d’akin nata wani saban Tuna’nın ta somayi game da abunda ya faru d’Asu , gabaki d’aya ta rasa wata hanya zata bi, babu abunda yake mata yawa cikin zuciya sai mafarkinta , “ Anya zan iya kuwa ?” Cewar Abla ta fad’a a fili , da Sauri kuma ta furta “ No! No! Bazan iya ba “ ta ‘karasa tana kulle idanuwanta.” Please ki kula mun da yaya na !” Maganar Little da ya fad’a mata a cikin mafarki yana faman kai kawo cikin zuciyarta, gani take kamar abunda take sa’kawa cikin zuciyarta ba mai yiwuwa bane amma duk da hakan bata da wani za’bin idan tana san sanin abunda take ‘ko’karin binciko wa kamar yadda ta gani a cikin mafarkinta . 

‘Dan turo bakinta tayi ganin komai yana ‘ko’karin ca’kud’e mata , Zo’ban ta da ta saka a fridge ta d’auko Allah ya temaketa bai yi sanyi sosai ba har wani kulle ido take lokacin da taji ‘kamshin sa , tray d’in da ta shigo da shi d’azu ta d’auko tare da serving d’in kanta kad’ai , a hankali take cin abincin ta hankali a kwance , sallamar sa da taji ne ta d’an d’ago da kanta tana amsawa a hankali , kasa cigaba da cin abincin tayi sabida idanuwansa da take ji yana yawo a jikinta . Amaimakon ya zauna akan sofa sai shima ya zauna a kan rug tare da tankwashe ‘kafansa kamar yadda tayi , cikin d’an rawar murya ta furt “ Sannu da zuwa .” shiru Big Boss yayi mata batare da ya amsa ba , d’an d’ago da kanta tayi sai karaf ya sauka a cikin nasa, da sauri ta janye nata idan idan tanajin wani iri a jikinta. “ So kike Wifey ta koya miki yadda ake sannu da zuwa ?” Cewar Big Boss , yadda yayi magana mutum zai iya rantsewa ba shi bane , d’an tsuke fuskarta Abla tayi batare da ta tanka masa ba . Cikin d’an jin haushi ta saka hannunta zata d’auki zo’banta ya d’an ri’ke hannun “ kina so na kira miki wifey ta koya miki?” A zuciye Abla ta janye hannunta , cikin ido da ido ta kallesa cikin d’an masifa masifa ta furta “ Ba wifey ko sholy sho ce babu abunda ya dame , ni ina ruwa , wifey , wifey , wifey saura waifilo ma “ gabaki d’aya ta manta Wanda yake gabanta sabida haushin da taji,kwalla har ta soma tarar mata a idanuwa Sabida ta kaici, tana ‘ko’karin mi’kewa yayi saurin Hugging d’inta “ I Love you my Baby Doll”. 

IBTISSAM
      ( A heart touching story of love and destiny)

Story & written 
      By
Mss Lee   

                     09134652921

    TALLA!! TALLA!!! TALLAH !!!!!!!

SHIN KUNSAN WACECE HAJIYA NUSAIBA BR~B ZURU ?❤️

HAJIYA ~ NUSAIBA DR~B ZURU

MAMALAKIYAR ZIMH ISLAMIC AND MEDICINE DAKE RINGH ROAD A KANO NIGERIA
Tazo muku da ingantattu ko sahihan magungunan mata masu inganci, ba’anan kad’ai ta tsaya ba har da na cututtuka da Turarukan wuta , Humra masu shegen ‘kaushi . Abun Alfaharin kuma tana bada sarı cikin sau’ki, sannan kuma suna aikawa duk inda mutum yake afad’in duniyar nan. 

Duk wacce ta siya magungunan Hajiya Nusaiba Dr B zuru, taga be yi mata aiki ba tazo za’a dawo miki da kudin ki . 

KA’DAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKE SIYAR WA

1️⃣ Hadin amarya
2️⃣Hadin mai jego
3️⃣Hadin sabon budurchi
4️⃣Hadin Kaza Yar’Suddan
5️⃣zuma -Tsumi- Tabaje da sauransu
6️⃣Turaren Sandal ruuu& flastic Sandal
7️⃣ Hadin Hawwi domin inganta zafafiyar kauna
8️⃣Hadin bagadad,kahlij,kajiji,gafgaf dasauransu
9️⃣Hadin humra soyaya dole ta matan aure da normal humra

DON SAMUN ‘kARIN BAYANI KU NE META TA WANNAN NUMBER KAMAR HAKA : 
    08133647913 

   KANO NIGERIA 

LOCATION: RING ROAD BAYAN GİDAN MAN NAZARGO.

       SIYAN NAGARI MAIDA KU’DI GIDA

PAID BOOK

BOOK 2 
         S_____ 14

NOT EDITED 

Tuna’nın me kike?”cewar Big Boss ganin da alama ta manta da shigowarsa, nan ma shiru Abla tayi masa sabida duniyar Tuna’nın da ta fad’a , finger d’insa d’aya ya sa ya d’an doki goshinta, a firgice Abla ta kallesa , sai kuma tayi saurin kallan jikinta da abincin gabanta ganin har lokacin tana zaune a in da take “  Tunanin me nakeyi haka ? ya Allah “, cewar Abla da gabaki d’aya ta d’an rud’e ganin yadda yake kallanta , hannunta d’aya ya ri’ke cikin nasa kafun ya ‘kara furta “ What’s wrong with you huh? Tunanin me kike ?” Cikin Sauri Abla ta girgiza masa kai “ No babu komai ba tunanin komai nake ba .” ‘Dan tsuke fuska Big Boss yayi kad’an “ what’s on your mind ?” Ya furta yana tsare ta da idanuwansa , ‘kwarewa Abla ta kusan yi cikin Sauri ta d’auki zo’bon gabanta ta sha “ Dagaske babu komai fa “ ta fad’a a sanyaye. “  Zaki rakani wajan wifey anjima ?” Wani irin d’ago da fararan idanuwanta Abla tayi ta d’ora masa sai kuma tayi saurin d’aukewa tana kallan abincin gabanta da gabaki d’aya ya fita a ranta , “ Are you afraid ?” Ya ‘kara furtawa yana binta da narkakkun idanuwansa , tsuke bakinta Abla tayi tana ‘ko’karin tattara abincin gabanta “ Ni ina ruwana da matar ka” tana ‘ko’karin mi’kewa ya ri’ke hannunta guda d’aya “ Are you jealous?” Fusge hannunta Abla tayi cikin jin haushinsa , ko kallan inda yake bata yi ba ta fice daga cikin d‘akın zuwa dining. Tana ajje tray d’in ta dafe kanta “ Ya Allah ! Tuna’nın ne nakeyi haka ?” Yana gama tanbayar kanta taji kamar kalmar na ‘kara shigar mata cikin kunne “ I love you!!!! “, da duka hannayenta Biyu Abla ta toshe kunnuwanta tana furta “ A’uzubillahi minash shaid’anir rajeem”, sai kuma ta d’aga fuskarta cike da jin haushin kalaman sa “ Wifey ! Wifey! Wifey ! Ni ina ruwana da wata wifey d’inka da zaka takura mun , duk lokacin da naga yar iskar yarinyar nan sai na fasa mata baki, Mtsww “ ta ‘karasa tana kuma jan wani tsaki , kamar zatayi shiru sai kuma ta ‘kara maimaita “ wai nice ma zan rakashi wajan ta ? Fine zanga ko wace yar iskace ai ,huh “ ta ‘karasa tana zama akan dinning d’in kitchen d’in batare da ta koma d’akin taba, sai Youghurt d’inta da ta d’auka tana sha.

***** Tunda ta fita daga cikin d’akin yake bin hanyar da ta fita da kallo , shi kad’ai wani irin murmushi me d’au sauti da ya’kawata fuskar sa ya saki ,irin murmushin da Zai ce be san ranar da yayi saba “ She looks more gorgeous when she’s jealous “, ya fad’a wani murmushi me d’au sauti na ‘kara sakko masa, almost 10 minutes yana zaune a cikin d’akin amma babu Abla babu alamar ta. Diamond watched d’in shi ya kalla ganin lokacin sallah ya kusa ya sa ya d’an motsa gefen bakinsa kafun ya bar d’akin gabaki d’aya zuwa nasa . 

ABLA 

Tana cikin kitchen d’in nan har after 4 , sai data gaji dan kanta tukunna ta koma bedroom d’inta , tana shiga ta tarar da baya ciki,da fararan idanuwanta ta d’an harari inda ya zauna kamar Ance mata yana wajan. Hasken da wayar ta tayi ne yasa ta ‘karasa gaban mirror d’in , tana d’auka taga alamar shigowar message shiyasa tayi Saurin shiga WhatsApp d’inta . Message d’in su Eshaal ne ya soma shigo wa cikin wayar , ga missed called d’in group called data gani, sai data bi gabaki d’aya tayi musu reply tana ‘ko’karin sauka taga message d’insa , kamar zata share sai kuma ta shiga cikin message d’in duk da batayi saving number ba tasan shine “ 8:25pm I will introduce you to my wifey.” Takaici ne ya kama Abla bata san lokacin da ta d’an saki tsaki ba tana kashe datar ta gabaki d’aya “ Wifey? Huhhh”. 
Chapter 41 · 0% Book details