← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 100

Sashe 43

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

    *****Hajiya falmata kuwa tana shigowa falour ta tarar da uncle Adam shima ya dawo duk da face d’inta babu fara’a sosai haka ta shanye komai cikin bariki da saka murmushi akan fuskarta , shima murmushin ya sakar mata yana zama “ uwar gıda sarautar mata “ wani irin murmushi Hajiya falmata tayi tana fari da ido “ kuma amarya ba ? Kwallin ‘kwall matar Adam “ girgiza kansa Uncle Adam yayi “ bazaki canza hali ba haryanxu ? Har agaban ‘ya’yanki bakya kunyar kiran sunana duk yadda kike so wai Yaushe zakiyi hankali?”d’an tsaki Hajiya falmata tayi “ mitar ka tayi yawa , kai komai sai kayi complain akai haba nifa banasan iriin wannan abun” d’an murmushi Uncel Adam yayi “ Toh maida wu’kar mana ai ba abun fad’a bane Hajiya Falmata na , yanzu wanka nakeso na fara tukunna kafin na zo miki da maganar da nake san yi . Cikin sauri Hajiya falmata ta tari nunfashin sa “ ah ah kasan banasan iriin haka , kawai ka fad’amun tun yanxu kafun kashiga wankan naka zai fi maka sau’ki ma,” koma da gaggawa Wallhi ki bari na fara wanka mana ?” Itama Hajiy falmata mi’kewa tsaye tayi “ babu Inda zakaje fa sai ka fara fad’amin”,d’an Jim kad’an uncle Adam yayi kafun ya furta “ Daga yau bakece Chief  leader d’in gidan nan ba Sabida His Excellency ya mi’kawa wannan mu’kamun zuwa Sirikarsa “ da Haka ya bar falourn yana mamakin reaction d’in face d’inta . Yana barin falourn Hajiya falmata ta same ‘kasa , ‘kafafuwanta gabaki d’aya ta ware su a ‘kasa ko motsi ta kasa shock ne ya kamata dan ko idanuwanta bata ‘kiftasu. 

*******A part d’insu Hajiya Sa’adatu gabaki d’aya ko wannan su yana cikin tashin hankali babu abunda yake musu yawo a cikin zuciya sai mu’kamun Abla , cikin ba’kin ciki Hajiya sa’adatu take furta “ Me his Excellency yake nufi da mu’kamun da ya bawa waccen shegiyar ? Me hakan ke nufi ? Nan gaba komai namu za’a kwace kenan ko kuma me ? Gaskiya da sake hakan ba me yiwuwa bane Anya bata lashe su ba kuwa ? Wallahi bazan ta’ba bari hakan ya faru ba dole na d’au mataki yau yau d’in nan ba sai gobe ba, wata number da tayi saving da ‘kaura tayi dialing kafun ta wuce bedroom din ta. 

✨✨✨✨✨✨✨

6:20pm Abla ce zaune kan sallaya , tun bayan idar da sallan da tayi bata tashi ba sai yanzu . Direct gaban mudubinta ta koma Sabida gashin kanta da ta ke san gyarawa , sai da ta tabbatar ta busar dashi da hand dryer tukunna ta soma gyarashi a hankali Sabida uban cikowar da yake dashi da ‘kyar take iya tajewa , dad’inta d’aya ma kwana biyu gashin kanta ya ‘kara laushi shiyasa baya mata wahalar da yake mata kamar da. Sai data d’auki almost 30 minutes tana gyaran gashin kanta sabida mugun cikowar da yake dashi, yana gamawa phone d’inta ta janyo Daidai lokacin da Fanan tayi musu group call,Abla na d’aga wa gabaki d’aya suka rufeta da fad’a babu abunda take sai faman dariya , a ‘kufule Fanan fa furta “ Allah Abla baki da mutunci duk lokacin da zamuyi waya sai dai Mudunga ganin ki update , ko message muka bar miki sai dai mu dawo mu tarar da reply wallahi ki canza halinki, ai na kusa zuwa nigeria wallahi duk Inda kika shiga ma sai nasaka BiiBii ya nemoki, had’uwata dake bazai yi kyau ba dan sai na ‘kwa’kwule wannan idanuwan naki masu kama da farin tattabara “, dariya suka kyal’kyale cikin tsokana Abla ta furta “ Shikenan tunda bakuyi murna da zuwana bari na dauka “ hararar ta Baby tayi “ da kin ganni a mafarkin ki kuwa yau “ cikin Sauri Abla ta furta “ Nikam ina Eshaal ne ? Ko bakwa tare ?” Dariya Baby da Fanan sukai lokaci d’aya “ Ni dai babu ruwana idan tazo sai ta fad’a miki da bakinta ko kuma ga Baby nan kınsan duk neman rigima baya mata wahala “ cikin Sauri Baby ta furta “ Wallahi babu ruwana , Eshaal ta koyi masifa yanzu, ah too gwanda kije ki tanbayeta da kanki ai kunfi kusa “ ‘karamin kwafa Abla tayi “ idan tayi wari ai zanji “ zuwan Eshaal Kenan ta furta “ baza ma tayi wari ba balantana kiji, nifa naga kin murmure , Anya ?” Hararar ta Abla tayi kafin ta furta “ Anya fresh d’innan da kike babu komai a cikin Kodai kin..” da sauri Abla ta kashe kiran tana furta “ Yar iska kawai “. 

Kallan time Abla tayi ganin 7 ta wuce d’an ta d’an ja ‘karamun tsaki har zata kwanta sai kuma ta Tuna da kwalbar da M.Sarah ta kawo mata , cikin Sauri ta d’auko ta dukda bata cireta daga cikin ledar ba , sunan kwalbar ta d’auka tare da mayar da ita inda ta d’auka , babu abunda ya fad’o mata cikin ranta , duk iya Tuna’nın da take sanyi ta kasa yau sabida yadda take jin kanta a cinkushe sosai , tsaki Abla taja tana ajje wayar cikin jin haushi . 

7:45pm Abla tashiga dressing room d’inta , tunanin kayan da zata sa ta soma , cikin sauri ta furta “ Babu abunda zan sa Menene ma had’i na dasu” ta ‘karasa tana kwa’be fuska tare da fitowa daga cikin dressing room d’in, tana zama kan gado jenny ta shigo cikin d’akin bayan knocking d’in da ta dad’e tanayi hannunta d’auke da wani designer box me shegen kyau ,” Madam it’s for you! “ kar’ba tayi tana bin box d’in da kallo har Jenny ta futa , cikin sauri ta bud’e box d’in wani irin farin gown ne a ciki duk da ba’a warwaresa ba zakaga yadda storn d’insa yake faman shinning da walwali, da sauri Abla ta d’aga gown d’in ita kanta ba ‘karamin kyau rigar tayi mata ba , cıkin sauri kuma ta ajjeta tana jan tsaki “ yanzu akan wata banza zan saka wannan rigar ? Babu Inda zani ma ,” ta ‘karasa tana türe jakar, vibrating d’in da wayar ta tayi ne yasa ta d’an kalleta kad’an , babu suna a jiki har zata ‘ki d’auka sai kuma ta saka a kunnenta bakinta d’auke da sallama , wani irin shirune ya karad’e kunnuwan su babu Wanda ya kuma magana a cikin su , “ Assalamu Alaikum ?” Abla ta kuma fad’a ganin babu alamar za’a amsa mata ta kashe kiran , tun kafun ta ajje wayan aka sake kiran ta , yanxu cikin d’an jin haushi ta d’aga kiran zatayi magana taji saukar muryarsa cikin dogon kunnanta “ ki saka kayan, zamu tafi in not less than 10 minutes if not zan zo na shirya ki da kai na “ Abla zata ce masa ta fasa zuwa yayi hanging call d’in.

Kallan time Abla tayi kafun ta ‘kara kallan rigar duk da yadda tayi mata kyau bata jin zata iya sata “ ko nazo na sa miki da kaina “ shine abunda ya dawo cikin kunnanta , cikin sauri ta mi’ke tsaye tana d’aukar rigar zuwa dressing room d’inta . 
Chapter 43 · 0% Book details