← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 100

Sashe 31

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Tunda ya d’ora kansa akan Lap’s d’inta Abla ta kasa motsawa , shima kuma be janye kansa ba , idanuwansa still kuma a kulle suke , d’an satar kallan sa tayi kad’an ganin be d’aga mata cinyar ba , tana dubawa sai taga idanuwansa a kulle kamar me bacci, d’an ’karamin bakinta Abla ta turo kad’an tana ‘kara bin face d’insa da kallo duk da rabun dogon gashin kansa ya rufe masa face d’insa , maida kallanta tayi kan dogon gashinn shima ma tana zuba masa idanuwa musamman yadda ta ganshi ba’ki sai shining yake sabida yadda yasha mayuka sosai ga wani irin ‘kamshi da yake tashi daga kansa, hannun ta d’aya ta d’ora akan kamar ne tsoran wani ya kamata , yadda taji gashin kansa da shegen laushi da sanshi yasa ta zura hannun tana ya mutsa gashin a hankali , gabaki d’aya yanayin gashin ya d’auke mata hankali shiyasa gabaki d’aya ta gashin wanene. 

   Big Boss kuwa tunda ta saka hannun ta cikin gashin kansa ya bud’e idanuwansa dukda babu me kula da hakan Sabida yadda gashin sa ya rufe kusan rabin fuskar tasa , sosai yake jin dad’in abunda takeyin shiyasa bai motsa ba har lokacin, a hankali ya soma lumshe eyes d’insa yana bud’ewa , kusan sau 3 yana abu d’aya kafun ya kulle eyes d’insa gabaki d’aya. 

Ta d’au kusan mintuna 10 tana abu d’aya kafun ta soma tattara gashin kan nasa waje d’aya kyakkyawar Side face d’insa ta fito sosai da ita , kasa janye idanuwanta Abla tayi daga kansa , sosai take kallansa kamar Yaushe ta soma ganin sa , red lips d’insa da yafi komai d’aukan hankalinta ta kai hannu wajan kamar me shirin ta’bawa sai kuma tayi saurin janye hannunta sabida yadda taji zuciyarta tana har bawa da Sauri Sauri , babu abunda ya fad’o mata arai sai abunda ya faru jiya a tsakanin su, kamar Ance yana kallanta ta saka hannunta gabaki d’aya ta kulle idanuwanta. 

11:20am wayarsa ta soma haske alamar kira ya shigo, har lokacin Big Boss bai bud’e idanuwan sa ba wayar kuma na jikin sa , a karo na biyu da ta ‘kara haske ne yasa ya soma bud’e idanuwansa a hankali cikin nutsuwarsa , gabaki ya bud’e su gabaki d’aya a cikin d’akin da take, d’an juyowa yayi kad’an daniyar kallan inda take yaganta har lokacin a zaune ga wuyanta da ya karkace sai faman ya tsina fuska take da alama batajin dad’in kwanciyar ,” silly girl “ ya fad’a cikin ‘kasan zuciyarsa lokaci d’aya ya mi’ke zaune ita kuma Abla tayi baya zata fad’i ya tare ta , yanzu kam sosai ta ya mutsa fuskarta tare da d’ora hannunta a kan wuyanta , cikin yanayi na bacci ta furta “ ouch” da alama wuyanta ri’ke wa yayi shiyasa ta ri’ke hannun ta sosai a Wajan. Hannun sa d’aya Big Boss ya saka a Wajan yana murza mata shi a hankali a hankali, kusan 2 minutes yana mata hakan kafun yayi ‘ko’karin mi’kewa , cikin bacci Abla ta janyo hannunsa sosai , by mistake hannunsa ya bigi boobs d’inta , yadda Abla tayi da face d’inta sai ya so baka dariya dan sosai ta shagwa’be ta da alama taji zafi, d’an murmushin gefen baki kad’an Big Boss yayi kafun ya gyara mata kwanciyarta yana lullu’beta da white duvet me laushin gaske , phone d’insa kawai ya d’auka yabar d’akin.

****** 12 Saura ya shigo cikin d’akin da take , sanye yake cikin milk colour d’in kayan kanfanin Kate Rowland da yayi bala’in yi masa kyau sosai kyawun Big Boss ya ‘kara fitowa , irin had’uwa da kyau da yayi bata ‘baki ne wajan fusaltashi , a hankali ya soma cikin d’akin ’kafarsa sanye cikin brown half shoe d’in Thank God I’m Vip, daga bayan ‘kafarsa sosai farar fatar ‘kafarsa ta fito fari tass dasu , hannayensa gabaki d’aya suna cikin aljihu hakan ne ya bawa brown watches d’insa fitowa sosai tare da sar’kar da kullum ba ya rabuwa da ita a cikin wuyansa , sai faman walwalin zallan pure diamond take. Har kan gadon ya ‘karasa ya zaune gudun karya tashe ta , baccin ta take so peaceful a bunta shiyasa cute face d’inta ya fito sosai , watche d’in hannun sa ya kalla tare da lumshe idanuwansa , a hankali ya kai bakin sa Daidai saitin forehead d’inta ya sumbata, yadda ta kwa’be face kamar tana ganinsa yasa ya firgiza kansa, cikin wani irin sauri ya rad’a mata “Baby Doll “ a kunne kafin ya mi’ke ya bar d’akin gabaki d’aya .

♾️♾️♾️♾️
♾️♾️♾️♾️♾️♾️♾️
Chapter 31 · 0% Book details