← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 100

Sashe 35

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin taushin murya Nanni ta furta “ Didii kiyi hakuri mana ya tafi da matarsa tunda..” cikin sauri Didi ta furta “ Yi mun shiru , kema ai bayansa kike bi, toh bazai tafi da itan ba ,” wani d’an gefe Big Boss yayi wa Didi yana knodding kansa , yadda taga ya juya a tunanin ta mayar da ita  sai taga sa’banin hakan sabida waya Bobo da ya kar’ba, “ come in “ kawai Big Boss ya furta kafun ya kashe kiran, wani irin gurnani suka soma ji me ‘karfin gaske , Nani da Didi gabaki d’aya sun tsure suna Tuna’nın ta Inda suke jin gurnanin, kamar daga sama Simba ya shigo cikin tsalle yana bud’e bakinsa , Bobo na gefe babu abunda yake sai faman danne dariyar sa da yake , wani irin jijjiga Didi ta somayi sabida ganin Zaki ganin idanuwanta , babu abunda take fad’a sai wa innahu min sulaimanu,” Nanni ma gabaki d’aya burkicewa tayi ganin mutuwa a gabanta , yadda Simba ya nufo wajan Big boss yasa Daga Didi har Nanni suka shige wani d’akin a guje suka kulle ‘kofa , d’an ‘karamun ‘kafa Big Boss yayi tare da barin part d’in Simba na biye dashi, tsabar mugun sauban da Bobo har da zama Sabida gudun Diidii yadda ta dunga wuntsulo kafarta bayan ga sanda tana takawa dashi. 

Big boss kuwa tunda ya Fito gabaki d’aya mutanan wajan suka shiga taitayinsu, babu Wanda yake ‘kwa’k’kwaran motsi a cikin su yadda sukaga Simba na girgixa gashin jikinsa , babu Wanda be rikirkice ba , jikinsu har rawa yake yadda suka ‘kame ko motsin kirki babu Wanda yake yi sai bin hanyar da Simba yake bi suke da kallo, har Big Boss ya wuce part d’insa da Abla , Simba kuma ya zauna a harabar wajan , duk inda yaji motsi sai ya kalli wajan, idan hankalin su yayi dubu toh a tashe yake ganin yadda zaki yake kallansu , tsoransu karsuyi motsi ya cinyesu. 

Big Boss direct d’akin ta ya gaita, fuskarta tayi falau kamar wadda ta dad’e tana rashin lapiya , tunda ya kalleta sau d’aya bai sake kallanta ba sai ruwa da ya d’auka ya yayyafa mata, bakinta d’auke da salati ta ri’ke cikin da da ‘kafarta babu abunda take cewa sai “ Wayyo Cikina , Wayyo ‘kafana zai cire ,” ganin yadda take ‘ko’karin sauka daga bed d’in ya Mayar da ita tare da dora hannunsa d’aya kan mararta, a hankali ya soma matsa mata kamar me yi mata tausa a wajan, a hankali a hankali tun Abla tana ‘ko’karin kwacewa har ta soma ajiyar zuciya kad’an kad’an idanuwanta a lumshe ga ‘kafarta da ta ri’ke , ganin ta samo samun relief ne ya kwantar da ita tare da barin d’akin, cikin ‘yan mintunan da basu fi biyar ba ya dawo d’auke da allura a hannun sa, hannun ta d’aya ya kama Daidai lokacin da take ‘ko’karin bud’e idanuwanta , saukar allurar da tajine yasa ba shiri ta fashe da kuka Sabida arayuwa idan akwai abunda take tsoro cikin harda allura , bai ce mata komai ba fuskarsa har lokacin kuma a had’e take , Wajan da yayi mata allura ya d’an mulmula mata kafun ya kama ‘kafar da tun d’azu take ri’kewa, a hankali a hankali ya soma yi mata tausa a ‘kafar da take ciwo, tun tana ri’kewa har ta dena sai ajiyar zuciya da take saukewa , sai da ya tabbata ta dawo cikin hankalin ta tukunna ya bar d’akin. 

   Bud’e idanuwanta Abla tayi tana bun ‘kofar da kallo, sosai hawaye suke mata gudu a fuska , tun tuni ta dawo cikin hankalin ta amma ta kasa bud’e ido ta kallesa, wani iri take ji a cikin zuciyar ta , kamar ta tsayar dashi amma tasan bazata iya hakan ba , hawayenta ta goge tare da mi’kewa ta nufi toilet dan ta tsarkake jikinta. 

    ****Tana fitowa ta tarar da trolley d’inta da suke part d’in Didi a cikin d’akin, ko kallansu batayi ba ta koma ta kwanta , wasu hayawen na sakko mata a fuska, ita kad’ai sai sheshshe’kar kuka take abunta.

‘Karfe 2:40am wani irin haya’ki ya bad’e cikin d’akin Abla , wani irin halitta ne ya bayyana babu kyaun gani hannun sa d’auke da wata ‘kwarya ja yana kallan kan gadon da Abla take bacci a takure, wani irin dariya ya she’ke da ita tare da nufo kan gadon, yana ‘ko’karin ta’bata aka ta’ba handle d’in ‘kofar, lokaci d’aya aljanun ya ‘bace kamar be ta’ba wanzuwa ba , kallan yadda take bacci a takure yayi har ya shigo cikin d’akin, hannu yasa daniyar gyara mata kwanciya cikin magagin bacci ta ri’ke hannun nasa ,kallan face d’inta da tayi fiyau yayi tare da zame hannun nasa a hankali ya gyara mata kwanciyar, wayarta dake bedside ya d’auka ya kunna mata karatu cikin low volume kafun ya rage mata wutar su dumm duk da ya fahimci bata san duhu shiyasa bai bar mata Wanda zata ji tsoro ba ko ta farka sannan ya bar d’akın. 

**********
*************
Washe gari kiran sallahr asuba ne ya tayar da ita, a hankali ta soma bud’e idanuwanta , Side d’inta ta soma kalla kamar me tunanin wani abu , a jiyar zuciya ta sauke fuskarta gabaki d’aya a cun kushe babu walwala a tattare da ita , sai da tayi wanka sannan ta shirya cikin simple doguwar rigar ta mara hayaniya black colour sai mayafinta shima da ta d’aura , sosai take jin ‘karfin jikin ta Sabida gabaki d’aya ta dena jin ciwan maran da take, cikin sanyin jiki ta soma gyara d’akin, hatta d’akın dressing da toilet gabaki d’aya sai data gyara, tunani da wasi wasin abunda ya soma yi mata yawo cikin zuciya tayi , kamar bazata iya ba amma haka ta d’aure ta nufi cikin d’akin sa , ganin babu kowa a ciki ne yasa ta d’an saki a jiyar zuciya da kallo ta soma bin d’akin har zuwa kan allurar Da ta fashe , kamar zatayi kuka haka ta soma gyra d’akin, sai da ta gyara ko ina tas tas dashi kamar bashi ba sannan ta nufi dressing room d’insa shima ta gyara masa tass dashi, tana fitowa ta tarar dashi a tsaye wajan mirror yana cire button d’in rigar sa , kamar ta ruga a guje haka take jinta, cikin sand’a ta ‘karasa fitowa kanta a sunkuye tana wasa da hannun ta , a hankali bakinta na rawa ta furta “ina ….kwana ?” kamar wacce tayi da dutse dan ko kallan side d’in da take beyi ba har ya gama cire button d’in rigarsa, wani irin kuka ne taji yana san zuwan mata ta danne shi yanxu cikin yanayi kamar me shirin yin Kuka ta ‘kara gaishe sa, a maimakon ya amsa mata sai yayi wucewarsa zuwa bed d’insa kamar bai san da zaman wani halitta a wajan ba , a guje Abla ta bar d’akin sai a lokacin ya d’an d’ago da face d’insa ya kashe light d’in d’akin zuwa dum light. 

A d’aki Abla sosai tayi kuka harta godewa Allah a haka bacci ya d’auketa . Sai wajan around 11:04am ta farka shima yunwa ne ya farkar da ita , sai da tayi wanka sannan ta fito falourn fuskarta fayau, Jenny na ganinta ta ‘karaso Inda take “ weldone Mah, tun d’azu nake san dubaki amma na kasa Sabida karna takura miki kina bacci” d’an ‘karamun murmushi Abla ta saki , cikin Sauri kuma ta girgizawa Jenny kai jin abunda tace “ No ki barshi Youghurt kawai zansha shima mara sanyi sosai “ Madam shi kad’ai ? “ cewar Jenny, kanta Kawai Abla ta gyad’a mata batare da tace mata komai ba , tana kawo mata Youghurt d’in sosai ta shashi kuwa sabida yunwa da take ji amma duk da haka bazata iya cin abinci ba Sabida ta rasa appetite d’inta . Har wajan ‘karfe 1:30pm Abla tana zaune a falourn, kiran sallahr da ake ne yasa ya koma d’akin ta , sau d’aya ta kalli ‘kofar bedroom d’insa . 

     Tana idar da sallah ta kısa su Eshaal ko mood d’inta zai dawo amma gabaki d’aya sai ta ‘kara jinta so boring shiyasa sama sama tayi hira dasu kafun ta kashe kiran. Bata ‘kara fitowa falour ba tayi zaman ta a cikin d’akin yadda ta kwanta ta lafe cikin gado mutum sai yayi tunanin bacci take .

6:20pm Abla ta fito falourn cikin shigar wani material green colour me gan yayyaki a jikinsa , direct kitchen ta nufa , yanxun ma Youghurt ta d’auka dan tun safe ta kasa cin komai sai Youghurt ji take kamar intaci wani abincin zatayi Amansa , tana gama sha ta koma d’aki . 
     Gabaki d’aya tsawan lokacin nan bata kuma saka Big Boss a idanuwanta ba , tun safe da ta shiga cikin d’akin, yanzu ma da kuka bacci ya d’auke ta. 

Big Boss bai shigo cikin gidan ba sai around 2am , sai da ya canza shigarsa zuwa pjmas sannan ya nufi inda take, tunda ya shiga zauna ba sai duvet da ya gyara mata , yanxu ma karatun al’kur’ani ya saka mata kafun ya bar d’akin. 

******
THE NEXT DAY 

Haka Abla ta tashi su kuku da ita kamar wata mara lapiya , d’akin shi ta shiga ta gyara kafun ta fito ta dawo falourn, harta gama zamanta a falourn bata ga fitowar sa ba , jiki a sanya ye ta koma cikin d’akın ta . A takaice gabaki d’aya yinin ranar bata saka Big Boss a cikin idanuwanta ba , baya dawowa sai tayi bacci sannan kafun ta tashi yake ‘kara barin gidan, idan hankalin Abla yayi dubu to ya tashi kullum da kuka take kwana Sabida yadda ya fita har karta gabaki d’aya . 
Chapter 35 · 0% Book details