← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 100

Sashe 70

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

    “ zan fad’a muku amma sai kun mun al’kawarin abu d’aya , kun yadda ?” Kallan ta sukai sosai prince ya furta “al’kawarin Menene kike so ?tell us “ kanta Abla girgiza masa “ No Nidai sai kun fara mun al’kawari zakuyi mun tukunna zan fad’a muku . “ Fine  munyi al’kawari “ cewar Little , ajiyar zuciya Abla ta d’an sauke tana kallan yadda suka zuba mata idanu suna jiran jin amsarta “ a sanyaye Abla ta furta na Abbun kune “ karo na farko da ta ta’ba ganin ‘bacin rai Little , bai ce mata komai ya mi’ke zai tafi
 Prince ya mi’ke zaibi bayansu, cikin Sauri Abla ta furta “ Yaya Little ! Yaya prince kun manta kunyi mun al’kawari? Kallan jakar Little yyi kafin ya furta “ yes munyi muku da bamusan akan Menene ba , but Lil don’t talk about him again please “ cikin Sauri Abla ta furta “ Amma mai yasa Yaya Little ? Abbun kune fa “ yau cikin d’an ‘bacin rai Little ya daka wa Abla tsawar da ta sata saurin ja da baya har tana ‘ko’karin fad’uwa , Yana mata tsawan kuma sai ya dawo Little d’inşa “am so sorry Lil raina ne ya d’an ‘baci”, kanta Abla ta d’an jinjina masa a sanyaye “Am sorry too “, ta fad’a tana zama kan kujera , yadda suka ga yanayin ta ya canza gabaki d’aya ne yasa suma suka dawo suka zauna “ Lil are you angry with us ?” Cewar prince , kanta Abla ta girgiza masa “ ah’ah kawai inaso kukai masa abincin nan ne  da su Dada ,” ‘kara kallanta prince yayi kafun ya furta “ Lil”, itama cikin Sauri ta furta “ Dan Allah , kun manta kunyi mun al’kawari duk abunda nace inaso zamu yi mun ?just this once dan Allah yaya ba dan ni ba”, kallan Little da shima yayi shiru prince yayi kafin ya furta “ okay !just for you only “, kanta Abla ta jinjina musu “ Na gode sosai bari na d’auko muku sauran “ Sabida farin ciki bata tsaya jin amsar suba tana barin Wajan little ya furta “Yaya prince mai yasa ka yadda ? Kasan I hate to see him amma shine kuke so muje wajan sa?”, kafad’un sa prince ya dafa kad’an “ you don’t have to worry , abincin kawai zamu kai fa ba wai zama zamuyi ko muyi masa magana ba ko so kuke Lil  ta zauna cikin ‘kunci ? Kamanta we promised our self duk abunda Lil take so zamuyi mata shi ko mu bama so ? Ka manta ?” Kansa Little ya girgiza masa “ No yaya prince ban manta ba , just inna tuno he’s our father i so much feel annoyed, inda na san hakan ne da tun lokacin da yaya yace zamu bar gidan zan bishi”. Fitowar Abla ce yasa yayi shiru yana kallan yadda ta fito da bags d’in, ta farko ta nuna masa “ Na Abbu” sai kuma ta nuna ta biyun data ‘karshe “ the middle one na Uncle ne sai na ‘karshen nasu Nani”, kallan yadda take murna Little yayi kafin ya furta “ are you that happy ?” Kanta Abla ta jinjina masa alamar eh , bai ce mata komai ba ya d’auki bag d’in shima prince ya d’auka har sun juya zasu soma tafiya Little ya d’an jiyo “ I have a surprised for you, just be ready “, bai jiya jin tanbayar da zatayi masa ba suka bar part d’in, Suna fita Abla ta saki murmushi kad’an “ Insha Allah, you will be the most happiest family , i will love to see you all together “, sai kuma ta d’an yi murmushi kad’an mai ciwo Sabida tuno itama batasan nata iyayan ba , balantana tayi fushi da su. 

**********
       *************
 Momyn Baby ce a tsaye cikin d’akin da akai mata masauki dashi , tun d’azu wayar da take hannun ta take kare a kunnanta da alama waya take me mahimmacin ko zama ta kasa yi sai zagaye d’akin da take , a kallan farko mutum zai gane yadda tashin hankali ya fito mata sosai a fuska . Banji mai aka ce mata ba sai amsar da naji tana bayar wa “ Adam ya shammace ni , irin shammatan da ban ta’ba tsammanin cikin karo dashi haka da wuri ba , ni zai muna furta ?Ni d’innan zai muna furta ? Menene akai Adam ? Dole ya canza salo , hakan bamai yiwuwa bane , “ shiru Momyn Baby tayi tana sauraran maganganun da ake fad’a mata, “ shikenan zanyi yadda kukace amma wannan karan tabbas aiki babba za’ayi wa Adam ya fi aikin farkon dan naga shegen mutumin nan zuwan shi gidan nan ko tanı bayayi, duk yadda na rabashi da shegiyar yarinyar nan amma kamar yanzu komai lalace wa yake tunda naga har kiran sunan ta yake , idan kuma naga tana ‘ko’karin ’bata mun shiri kamar mahaifiyar ta to itama zan kawar da Ita ne kowa ma ya huta”. Motsin da taji kamar alamar takune tayi saurin furta “ bari zan kira , naji kamar ana takowa ne “, cikin Sauri ta kashe wayar tare da ajjeta akan table . 

     Turo ‘kofar d’akin akai ba kowa bane face da take tsaye sai faman ya tsina fuska take ga wani irin shegen murmushi da take yi lokaci zuwa lokaci. Kallan Momyn Baby tayi daga sama har ‘kasa kafun ta shigo d’akin tana saka key ta ciki , lokaci d’aya ta kyalkyale da dariya “ Menene ya baki mamaki? Gani na a wannan lokacin ko kuma mamakin gani na a cikin d’akin ki wanne daga ciki ?” Itama Momyn kallanta tayi daga sama har ‘kasa tana shanye komai a zuciyarta , “ Lapiya nagan ki anan ?”, ‘karasa shigowa Nani tayi kafin ta furta “ Lapiyar Kenan, kisha ku ruminka, duk tafiyar mu d’aya dan haka kar kiji komai a ranki dan gabaki d’aya naji maganganun ki “, zuciyar momy ta buga da ‘karfi amma duk da hakan bata nuna a fili ba “ Kamar ya nan fahimce ki ba “, ‘kara kallanta Nani tayi tana sakin wani dariyar “ Nasan ‘kudurin ki akan mijin ki da kuma ‘ya’yan da suke wajan ki , ko so kike na fad’a miki wanene uban d’aya daga cikin ‘ya’yan ?” Cikin Sauri Momy ta kallate yanzu tsoro ya soma bayyana akan fuskarta . Wani magani Nani ta d’auko ta ajje mata a gaban mudubin d’akin sannan ta nuna mata shi da hannu “ Poison ne kamar yadda kika gansa , a ko wana lokaci zan iya saki aikin kısa , idan ki kayi kamar kin çıka burin da suke san cikawa ne , idan kuma kikace zakiyi gaban kanki to tabbas zaki fad’a Rami, na baki daga yau zuwa gobe idan kin yanke shawara zaki iya jina a ko wana lokaci . Tana gama fad’ar hakan ta bar d’akin , bin bayanta da kallo Momy tayi “ Me hakan ke nufi ? Ta san Shiri na ko me ? No hakan bazai ta’ba faruwa ba “, cikin Sauri ta d’auke kwalbar batare da ta duba ko ta mecece ba ta saka ta a cikin wata drawer tare da ‘kara dialing wata number da Sauri tana karawa a kunnanta. 

*********HARRY

Gabaki d’aya Harry ji take rayuwar ta kamar a ‘kaya tun lokacin da ta saka kwallin nan, kullum cikin mafarkan Simba take yana san kashe ta , shiyasa gabaki d’aya ko fita bata sanyi Sabida shi , yanxu ma a zaune take ta saka kwalaban shaye shayenta a gaba tana sha, gabaki d’aya kamar ba a cikin hayyacin ta take ba , babu abunda take fad’a sai “ Masoyi Big Boss , Masoyi Big Boss karka tafi kamar ba , kazo muyi soyayya , masoyi na , karabu da ita ka taho waje na kaji masoyi? Kaji masoyi ?” Shine abunda take iya fad’a cikin shaye shaye tana surutunta da ba’a ganewa sosai tana ‘kara kurbar maganin gabanta da. 
     A wajan mahaifiyarta ma abun duniya ya isheta , duk ‘yan kud’ad’en da take dasu da kusan rabin kwala kwalanta ta siyar dasu sabida cikar burin ta na Wajan boka na kan dutse, amma komai kamar a banza take yi sai asaran kud’ad’en ta da take ga aiki da gabaki d’aya baya  gaba baya,  baya sai uwar kud’in ta da ake ci , tayi tayi  uncle Adam ya bata kud’i ya haka , sau tari tayi attempting zuwa kar’ba a wajan Abla amma sai taga kamar za’a raina ta a gidan shiyasa kwata kwata bata je ba , amma har yanxu abun na cikin ranta shiyasa gabaki d’aya adan da take da kwala kwalai yanzu ta rage sa ba kamar daba da kullum cikin shigar gwal take . 

*******
*************
Chapter 70 · 0% Book details