← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 100

Sashe 56

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Tunda tayi wanka ta saka Bathrobe d’in tayi zaman ta a toilet abunta sabida batasan had’uwa dashi , kusan mintuna 10 tana zaune a toilet d’in har bacci ya soma d’aukar ta . Tura ‘kofar da akai ne yasa a firgice ta bud’e idanuwanta har tana ‘ko’karin zamewa yayi saurin ri’kota, zata kwace jikinta ya d’auke ta gabaki d’aya a jikinsa zuwan kan Bed d’in da ya gyara , hannun ya zo ta’bawa tayi saurin jan jikinta tana matsar kwalla “ Ni kamayar da, Allah bazan ‘kara zama da kai ba kashe ni kake san yi , ka Mayar dani , Allah bana san wajan nan “ lokaci d’aya Abla ta soma kuka zai ta’bata ta ‘kara saka masa kuka cikin saurin ya janye hannunsa “ shikenan , Don’t cry , Don’t okay ? Kinga dare yayi sosai yanzu , ki bani na duba ciwan ki yanzu kinji Sunshine ?” Kamar zatayi kuka ta furta “ Ni dai ka mayar dani , banasan nan wajan” sai kuma ta saka masa kuka, cikin sauri yayi ‘ko’karin rungumeta  ta ‘kara fashe masa da wani saban kukan tana girgiza kai “ Ni banaso karka ta’bani ai daman so kake na mutu”, idanuwansa ya d’an lumshe kad’an yana dafe goshin sa , yasan ko yace zai lallasheta yanzu bazata ta’ba sauraran sa ba , cikin cool voice cike da lallashi ya furta “ it’s okay bazan ta’ba kiba mai kikeso yanzu , kina jin yunwa ? Mai zaki ci ?” A hankali Abla ta fury “ Ni ka fita “, d’an kallanta yayi kad’an kafun ya furta “ Will you be happy if I go out ?” Cikin Sauri Abla ta jinjina masa kanta , “ it’s okay , I will go “ ya fad’a yana mi’kewa .  Yana fita Abla ta cigaba da shashshe’kar kukanta , tun tana yi har ga soma ajiyar zuciya bacci ya soma d’aukarta, motsi kad’an sai ta firgita ta bud’e idanuwanta , tun tana baccin tana farkawa har bacci ya d’auke ta sosai . 
   Duk abunda take akan idanuwansa , ganin yadda take firgita ne yafi komai damunsa , sosai yake kallan face d’inta a cikin wayar sa tsawan lokaci har sai da ya tabbatar Dagaske baccin ya d’auke ta sosai sannan ya koma d’akin bayan ya d’auki abubuwan da yake bu’kata. 
   A hankali yake takunsa yadda bazai tashe ba har ya ‘karasa inda take , fuskarta tayi fayau sosai Sabida kukan da ta sha , idanuwanta har sun d’an kunbura sosai ya tsurawa pink lips d’inta da ya d’an bushe ido kafun ya Janye idanuwansa gabaki d’aya zuwa abunda ya d’auko, baya so ta tashi daga baccin da take amma bazai barta ba sai ya duba mata ciwan ta .

***** Su Little suna barin part d’in His Excellency itama Nanni tayi saurin mi’kewa sabida tuna maganar Sindilu, gabaki d’aya kallanta sukai ganin ta mi’ke tsaye , Mamy ce ta furta “ ina kuma zaki je ana tattaunawa?”, Nanni ji tayi kamar ta sha’ke wuyan Mamy amma a fili sai ta d’an sakar mata lallausan murmushin da babu Wanda zai kawo akwai mugun abu a ‘kasan ranta , d’an ya mutsa fuska tayi kad’an kafun ta furta “ Ina so zan d’an sha maganin ulcer d’ina ne gani nake kamar yana ‘ko’karin taso mun”,kanta Mamy ta jinjina alamar gamsuwa “ Allah ya ‘kara Lapiya , ya kamata ma ki huta idan kinsha maganin “ itama Dada amsawa tayi da “ Gskiya Hauwa ta fad’a miki , ya kamata ki d’an huta dan Wannan ciwan idan ba ai masa yadda yake so ba shi zaiyi wa mutum aika aika “, kanta Nanni ta jinjina tana ‘kara ya mutsa fuskarta kafun tayi musu sai da safe , a hanyar barin falourn saitin inda flower base d’in da Abla ta fasa ta kalla ita kad’ai sai faman taunar ya tsa take “ in tasan wata ai bata san wata ba “ cewar Nani cikin zuciyarta. 

    Tana fita cikin Sauri ta wuce part d’in su bata tsaya a falour ba tayi saurin wucewa cikin d’akinta gudun karta had’u da kowa a falourn, tana sai da ta kulle ‘kofar d’akin ta saki wani ‘karamun ihun ta kaici kad’an “ Ni ? Ni waccen yarinyar take san tozartawa a cikin mutane ? Idan ta san wata ai bata san wata ba, yau yau d’innan zanyi maganin shegiya naga ta yadda zaku dinga had’uwa, cikin ‘kan’kanin lokaci ta sauya kayan jikinta zuwa Ja sai wani zunbullen Hijabi da ta d’aura a kanta yanda babu Wanda zai fuskanci wani abun. 

     Sai data tabbata babu Wanda zai ganta tukunna ta salalla’ba ta fita ta baya hannunta d’auke da ‘kullin maganin da Sindilu ya bata, cikin sauri ta nufi inda taga an ta’ba ajje sa amma baya wajan, ‘karamun tsaki Nani ta ja duk da fargabar da take ji cikin zuciyarta hakan bazai hana aikata abunda tayi niya ba tunda burin ta zai cika. Duk inda ta duba sai ta tarar da baya Wajan sosai zuciyarta ta hasala , cikin tsananin ‘bacin rai ta juya zata bar wajan, gurnaninsa da ta d’anjine yasa tayi ajiyar zuciya kad’an tana tun karar d’akin dukda fitulan wajen babu haske, yadda zuciyarta ta ‘kyan’kyashe da san cika burun ta haka take ‘kara kusa kai zuwa inda yake.

‘Dakin da tafi tunanin yana ciki ta kutsa batare da Tuna’nın wani abu ganin zoben tsafinta na hannunta , Hasken wajen ba wani sosai bane amma mutum yana iya ganin sa , daga nesa kad’an ta hango sa a kwance , Tuna’nın yadda zata fara samo fitsarin masa tayi , cikin ‘kan’kanin lokaci tunanin abunda zatayi ya fad’o mata cikin zuciyarta . Wani iriin maganganun siddabaru ta somayi tana tunkaro inda yake , idanuwanta a rufe sai faman surutu take tana murza zoban tsafin hannunta , yadda taga yana bacci ne yasa ta soma zagayeshi tana sul’kullanta har zuwa lokaci mai d’an tsaho, kamar magic sai gashi Simba ya mi’ke tsaye idanuwansa kuma a kulle , wani irin dariya ta she’ke da ita kafun ta fito da maganin da Sandilu ya bata , babu abunda idanuwanta suke hasasho mata sai ta inda zata d’ibi fitsarin، gabaki d’aya kamar wata mara hankali haka ta ‘karasa inda  yake batare da damuwa ko shakkar abunda take sanyi ba, ‘kasan Hijabinta ta tattare waje d’aya a daidai wajan ta kashinsa ta soma gogawa yadda zaiji ‘Kai’kayin wajan fitsari ya fito , kamar wata mahaukaci ta soma yi masa tafiyar tsutsa a wajan , Simba da idanuwansa suke a kulle sai motsa ‘kafar sa , cikin rashin saki ta saka hannun ta wajan Sabida gabaki d’aya hankali da tunaninta yana kan abunda take burin samu, wani harfi da Simba yayi da ‘kafarsa sai da ya tsoratar da Nani cikin sauri ta sunkuyar da kanta gudun karya ganta, d’ago da fuskarta da zatayi ne kawai taji feshin abu me wari , cikin tsananin rud’ewa ta bud’e baki zata kurma ihu taji wani abu ya cika mata bakı me shegen wari ga ruwa ruwan da taji a fuskarta , ba komai bane face kashi da fitsarin da Simba yayi mata , yana gama wa kuma yasaka ‘kafarsa duka biyu ya harbi baya yana jijjiga bayansa sabıda fitsarin da yayi sai kuma ya koma can gefe sosai yayi kwanciyarsa har lokacin idanuwansa a kulle . Nanni kuwa yadda Simba ya hankad’a ta baya sai da kanta ya bugu sosai a jikin bango, ga Nononta d’aya da Simba ya harba da ‘karfi , cikin wahala ta d’an tsaki ‘kamar tana Sumewa . 

***** Nanni bata dad’e da barin part d’insu wata mota ta danno kai cikin gidan a kuje , kai tsaye ‘bangaran His Excellency ya nufa , bai jira mai gadi ko security su bud’e masa motar ba ya bud’e cikin Sauri, a haka ya nufi part d’in da yasan zai same su. Alokacin da su His Excellency suke tsaka da magana kamar daga sama suka ji shigowar mutum, d’agowar da His Excellency zai yi idanuwansa ya sauka akan mutumin da bazai ta’ba mantawa ba arayuwar sa , cikin a zama ya mi’ke yana nuna mutumin da ya shigo da hannu ,” Kai ne ? Adam Dagaske kai nake gani ko kuma idanuwana ne ?” Gabaki d’aya mutanan falourn suma mi’kewa sukai tsaye , d’ago da fuskar sa da mutumin zai yi lokaci d’aya fuskar Dadyn su Baby ya bayyana , kansa kawai yake jinjina wa cikin rashin kuzari “ Ni ne , Tabbas nine , nayi matu’kar kewar ka aboki ban ta’ba tunanin zan sake sanya ka a cikin idanuwana ba “, cikin annashuwa His Excellency ya murmusa yana ‘karasowa Inda Alhaji Adam yake lokaci d’aya suka yi Hugging juna , Su Mamy da Suka shigo sai faman goge hawaye suke kad’an kad’an, mai da kallansa Dadyn su Baby kan Diidii, cikin sakin murya da Annashuwa ya furta “ Ranki ya dad’e Diidii na same ku lapiya ?” ‘Dage Kanta Diidii tayi “ Adamu ai ka rainani sai da kuka gama rungume rungumen ku sannan zaka tuna dani , toh banayinka “ ‘karamin dariya su Mamy suka saki Sabida abunda Didi tace , mai da kallan sa yayi kan Mamy shima “ Friend  ya naga ‘kanwar ka kamar wacce ake ragewa shekaru”, girgiza kansa His Excellency yayi yana nuna masa wajan zama “ Babu ruwana ai kun saba fad’an ba tun yanzu ba , ina ka tafi ? Kasa ina ta neman ka , kuma ya naganka kai d’aya , sai a lokacin Dadyn su Eshaal ya Tuna da Momy yazo , kallan Mamy yayi kafin ya furta “ Ina Tuna’nın bata san hanyar da zata shigo ba “, kanta Mamy ta Jinjina tana nufar hanyar barin falourn , sosai His Excellency yake kallansa “ Ka canza ba kad’an ba , bazamuyi magana ba sai ka huta tukunna zuwa gobe “ itama Diidii mi’kewa tsaye tayi “ ya kamata ku huta kuwa dukan ku duk kin ishi mutane da tsufa kafin wad’an can ifritan yaran su zo , kallan sa Dady yayi jin abinda Diidii tace , lallausan murmushi His Excellency ya sakar masa “ zan yi maka bayanın komai zuwa gobe “.

******** HARRY 
Chapter 56 · 0% Book details