← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 100

Sashe 34

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jenny ce ta shigo cikin d’akin d’auke da ‘karamun tray sabida ihun Abla da taji, tana shiga yadda taga Abla akwance yasa tayi saurin ajje tray d’in tare da nufar ta “ Madam!Madam open your eyes “, tanayi tana jijjiga ta , ganin bata mutsine yasa tayi saurin nufar medium fridge d’in dake cikin d’akin, d’aya daga cikin ruwan mara sanyi sosai da d’Suka tare da bud’e button d’in , komai cikin Sauri take yinsa, sai da ta tuttula ruwan a hannun ta sannan ta wasa wa Abla da ko motsi bata yi ba , a karo na biyu ta ‘Kara wasa mata gabaki d’aya hankalinta ya tashi, ganin ta’ki motsawa ne ya ‘kara tayar mata da hankali bata san lokacin da ta tuttulawa Abla ruwa ba a fuska. Atshawar da ta soma ne yasa Jenny ajiyar zuciya tare da temaka mata ganin tana ‘ko’karin tashi zaune “ Sorry Madam , bari na fad’a musu condition d’in ki ko akwai wani temaka da zasu yi miki” ta ‘karasa tana ‘ko’karin mi’kewa , da sauri Abla ta ri’ko hannun ta , a wahalce ta furta “ No karki gayawa kowa please, just kije d’aki na daga bedside drawer akwai wasu magunguna ki kawo mun su yanxu and karki bari kowa ya shigo, duk Wanda ya ke nemana kice masa nayi bacci”, da sauri Jenny ta furta “ Amma Madam I have to tell Big Boss your condition “, cikin sauri Abla ta girgiza mata kai “ Nace karki fad’awa kowa , just do as I said please, am waiting for you”, kanta Jenny ta gyad’a mata tana barin d’akin cikin sauri , Abla kuma sai faman mur’kususu take a ‘kasa Sabida yadda takejin ciwon mararta, ga ‘kafar damanta da take mata mugun ciwo sosai, kusan haka take duk lokacin da take period sai tayi ciwan ‘kafarnan, ganin ya ‘ki dena mata yasa ta fashe da kuka har lokacin tana dafe da cikin ta .

Big Boss kuwa ranshi ba ‘karamun ‘baci yayi ba yau, yana kashe kiran ya buga wayar a jikin mirror, lokaci d’aya mirror ya tsaye ga wayansa da ta fashe itama hannunsa har ya soma Jini Sabida glass d’in da ya cake sa a hannun, jijiyoyin kansa ba ‘karamun fitowa sukai ba rud’u rud’u, cikin sauri ya janyo side drawer ya d’auki wasu allurai guda uku,d’aya yayi wa kansa ko bud’e idanuwansa da suka rine ba yayi , ya d’auko zai yi ta biyun kawai ya bugata da ‘kasa ransa  a’bace da duka hannayensa ya dafe kansa da yake sara masa kamar zai cire, babu abunda yake furtawa ‘kasan zuciyarsa sai “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un “ya d’au tsawan lokaci a hakan kafin ya Samu waje kan sofa ya lumshe idanuwansa.

****** Tunda ya shiga cikin bedroom d’insa Bobo da sauban suke jiran fitowarsa, kusan 1 hour suna zaune a falour kafun Sauban ya mi’ke tsaye “ yau fa izzar dude ta isheni, let me go and check “ da zafi Bobo shima ya mi’ke suka nufi bedroom d’insa , tun kafun su ‘karasa shigowa Bobo ya hango yadda Jini yake fita daga hannun Big Boss , cikin sauri ya ‘karasa shigowa “ Oh no” cewar Bobo lokacin da ya ‘karaso , shima sauban cikin sauri ya zauna kusa da Big Boss “Me ya sameka? Why are you bleeding ?” Shine tanbayar da sauban ke faman jera masa , Bobo kuwa gaban mudubin sa ya ‘karasa ganin alluran da Big Boss ya d’auko , cikin sauri ya sa ta a cikin aljihunsa kafun ya nufi fridge d’in d’aki, manyan faro guda biyu ya d’auka har ya fara bud’e murfinsu yana zuwa Kawai ya tuttulawa Big Boss akansa, da hannayensa biyu Big Boss ya dafe kansa har Bobo ya gama zuba masa ruwan, 
Sauban kuma ya d’auko First aid box yayi masa dressing a hannunsa,ko kuffan Big Boss bai ce masa ba sai da ya gama zai yi masa magana Big Boss ya nuna musu hanyar fita , Sauban zai sake magana Bobo ya girgiza masa kai tare da jansa suka fito waje “ Me yasa zaka hanani yi masa magana ? He’s angry , but I was surprise me ya ‘bata masa rai haka ?” Dan murmushi Bobo ya saki kad’an “ Don’t mind ! Time kawai yake so , let’s leave him for the night ,in ya sakko zuwa gobe sai muyi magana “ cike da damuwa Sauban ya furta “ baka Tuna’nın yaji wa kansa ciwo ? Ka duba yadda yayi hurting hannunsa , and does glasses dole a gyara a canzasu “, kansa Bobo ya girgiza masa “ in muka ce zamu sashi magana we will make the thing worse again , insha Allah babu abunda zaiyi tunda kaga ya tsaya a iya hannu bazai sake yin komai ba , let’s go”,  zasu bar wajan Jenny ta fito daga d’akin Abla hannunta da magunguna, gabaki d’aya batayi tsammanin ganin suba , suna had’a ido gabaki d’aya ta saki magungunan hannun ta suka zube a ‘kasa , kallan mamaki Bobo ya bita dashi kafun ya kalli magungunan da ta zubar “ Magungunan Menene wannan?” Cewar Bobo yana binta da kallan tuhuma, inda inda Jenny ta fara musu dan gabaki d’aya bata san ya zatayi ba gashi Abla ta hana ta sanar da kowa halin da take ciki , cikin d’an d’aga murya Bobo ya furta “ Baki da hankali ne ? Should I repeat my self?” Cikin Sauri jenny ta furta “ Sorry sir , magungunan Madam ne ?” Da mamaki Bobo ya furta “ magungunan Abla ? Me ya same ta ?” Sunkuyar da kanta Jenny tayi ganin bata da mafita dole ta fad’a musu “ Sir na shiga d’akin ta na sameta a süme da ta farfad’o kuma sai kuka take tana ri’ke da cikin ta , and ta bani umarni karna fad’awa kowa , my intention was to tell Big Boss amma ta hanani shine tace na d’ebo mata wad’an nan magungunan “, kansa Bobo ya ta’ba kad’an cikin Sauri ya sa ta kwashe maganin “ Don’t tell him! Banaso yasan komai , bari na kira  Dr ya duba….”, be ‘karasa zancan saba sabida bud’e ’kofar d’akin Big Boss da akai , shi d’inne a tsaye hannun sa d’aya a cikin aljihu d’ayan hannun sa me ciwo yana waje , wani irin kallo ya jefa musu gabaki d’ayan su , kafin ya wuce ya bar wajan babu Wanda ya kula ko kuma yake da shirin komawa “ Anya ba part d’in Didi zashi ba ?” Cike da rashin damuwa Bobo ya furta “ can zashi , let’s follow him dan yadda ya fita duk Wanda ya kuskura yashiga gonarsa sai ya sumar dashi,” da haka suka bar Jenny a tsaye jikinta har ya soma rawar tashin hankali, amma gudun kar Big Boss ya rigata zuwa part d’in yasa ta kwashe maganin ta fita da gudun gaske . 

Part d’in kuwa ya nufa Bobo da sauban suna bayansa Jenny kuma ta ‘karasa cikin part d’in da iya gudun ta , tana shiga ta tarar da Nanni da Diidii a zaune suna hira , da mamaki Didi ta furta “ ke lapiya kika shigo haka kamar wacce aka jefo ki?” Itama Nanni kallanta tayi “ Hope lapiya naga sai faman haki kike ?” Babu abunda Jenny take musu sai girgiza kai , Nanni zata kuma magana taji sallamar su Bobo, ga Big Boss da ya shigo cikin falourn fuskarsa a had’e ko kallan su Didi be yi ba sai kallan da ya jefawa Jenny da tayi saurin Nuna masa d’akın da Abla take ciki, gabaki d’aya tsakanin Diidii da Nanni an rasa me masa magana ganin yadda ya had’e rai ko kallansu baiyi ba , “ Me ya karo yaran nan shi kuma part d’innan?” Hannu Sauban ya d’aga mata “ Nima dai ban sanı ba Diidii amma ga Bobo nan ki tanbaye sa “ hararar sa Bobo yayi Nanni da ta damu gabaki d’aya ta furta “ kun samu a duhu ku fad’a mana abunda yake faruwa mana “ Da hannu shima Bobo ya nuna mata d’akin da Big Boss ya shiga “ I think kawai ku tanbayesa dan Nima ban sani ba “, kallan tuhuma Nanni ta jefa musu, zakuyi bayani idan na tarar da kun ‘barawa son d’ina , Diidii taho muje tunda bazasu fad’a mana ba “ da haka suka nufi haryar d’akin Ablan.

    Big Boss kuwa yana shiga ya tarar da ita a kwance hannunta gabaki d’aya dafe da cikinta gashi ko motsi bata yi , lips d’insa na ‘kasa ya tauna da ‘karfin gaske kafun ya ‘karasa inda take, gabaki d’ayanta ya d’aga sama tare da janyo wani brown towel da ya gani ninke a kan gadon ta d’ora mata , zai jiyo su Didii suka shigo d’akin, sallallami ta Somayi tana kallan Big Boşs “ Ina kuma zaka je da ita ? Maza maza ka ajjeta wallahi dan babu Inda zakaje da ita , kaji mun yaro da rashin kunya,” share su Big Boss yayi xai wuce Didi ta ‘kara hanasa , cikin sanyin murya Nanni ta furta “ Haba mana son bakaji abunda Didi ta fad’a bane ? Idan ka tafi da ita ina zaka kai ta kuma ? Gyaran jiki fa za’a yi mata kamar ko wacce amarya “ a fuske Big Boss ya furta , Banaso” ya ‘Karasa yana barin cikin d’akin , Didi da sauri ta biyo bayan sa tana shan gabansa “ babu Inda zaka je fa da yarinyar nan , na fad’a maka , idan ba haka ba yanxu ni sai na kira ubanka yayi mun iya ka da kai wallahi “ 
Chapter 34 · 0% Book details