Sashe 26
Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Direct cikin bedroom d’insa ya tafi da ita , cikin lallausan gadan sa ya zaunar da ita, yana dure ta Abla tayi ‘ko’karin tashi ya kuma mayar da ita , ganin ta’ki nutsuwa ne Big Boss ya d’an daka mata tsawar da ta sa lokaci d’aya ta tsaya tare da rufe idanuwanta “ Nifa wajan Little nake san zuwa , Dan Allah zasu cutar dashi fa “, kusa da ita Big Boss ya zauna kafun ya janyo ta jikin sa yana tapping d’in bayanta a hankali “ it’s okay ! dena kukan , zan kaiki wajan Little”, cikin kuka Abla ta furta “ Basa san mu ko? Suna so su cutar da Little fa “, hannu yasa ya mata alamar tayi shuru, shirun kuwa tayi tare da lafewa a ‘kirjinsa tana sakin ajiyar zuciya a hankali, shima bai dena tapping d’in bayan taba tsawan lokaci ga addua da yake mata ‘kasa ‘kasa daidai saitin kunnuwanta , sai da ya tabbatar ta nutsu kafin ya furta “ Me ya faru?” ajiyar zuciya Abla ta saki a hankali cikin sanyi jiki ta furta “ Mafarki nayi”, shiru Big Boss yayi mata kamar bazai tankaba sai ya furta “ Wana iri?”, Abla kamar zatayi kuka ta soma bashi labarin mafarkin sai da ta zo ‘karshe kuma kukan da take ‘ko’karin ri’kewa ya kwace mata , Hugging d’inta yayi a jikin sa shima , shi kad’ai sai faman taune ‘kasan lips d’insa yake , cikin cool voice d’insa ya furta “ Mafarki ba gaskiya bane, and karki fad’awa kowa wannan mafarkin , ba kyau fad’an irin mafarkin nan, just calm down okay ?” ‘Dago da fuskarta Abla tayi ita kanta bata san ya akai ba ta shagwa’be fuska , “ Amma mai yasa nayi irin shi ban ta’ba yi ba”, hancin ta Big Boss ya ja kad’an “ a times kamar ana so a nuna maka wani abu da kai baka sanshi bane , karki sa mafarkin cikin ranki okay ?” Kanta ta d’aga masa yanxu ma , “ shine kike ta kiran sunan Little banda nawa ?”d’auke kanta Abla tayi daga fuskarsa , da hannu d’aya ya jiyo da face d’inta , “ d’azu i was a bit angry with you , in zakiyi fushi ki dena fad’an maganar da ta zo bakin ki any how okay?”,a hankali Abla ta furta “ kayi ha’kuri, ni ba haka nake nufi ba “, karan hancin ta Big Boss yaja har saida tayi ‘kara “ Am hungry , cooked something for me “, kanta Abla ta jinjina masa dan gabaki d’aya mafarkin da tayi ya sagar mata da jiki, sai da ta zo Daidai ‘kofar fita taji saukar muryan shi “ karkiyi shirme “ d’an murgud’a baki Abla tayi kad’an yadda bazai ganta ba , sai da ta fita sannan ta d’an harari ‘kofar “ wai karnayi shirme , yen yen yen”, ta ‘karasa tana barin wajan gabaki d’aya.
***************
A ‘bangaran Hajiya falmata kuwa , Harry ce Baje a ‘kasa gabaki d’aya ba’kin ciki da takaici ya hana ta kuka , ga kanta da sai faman ‘kyalli yake sabida man da su M.Sarah suka shafa musu, Hajiya falmata na tsaye ko zama ta kasa yi sai faman taunar yatsa take ita kad’ai, cikin tsananin ‘barin rai ta soma magana “ Lalle yaran nan ya zama la’anan ne tunda baya d’aukan kowa da gashi, toh wallahi bazata sa’buba kafin nazo karka sai na gama da shegiyar yarinyar nan mai kama da mayu sannan na lallata auran da ake tun’kawo dashi, Indai ina raye bazaku ta’ba zama cikin kwanciyar Hankali ba ko da kuwa zanyi yawo tsirara ne “, sai a lokacin Harry ta iya bud’e bakinta “ Momy wallahi idan ban kashe yarinyar nan ba zuciya ta bazata ta’ba dena tafarfasa ba , sai na kawar da ita gabaki d’aya daga Doran ‘kasar nan, sai na ‘kunsa mata ba’kin cikin da bai ta’ba goguwq a cikin ranta ba , na tsane ta , na tsane ta , wai har ni Harry zan bawa wata shegiya ha’kuri ? Yarinyar da baifi in kifata da bango ba, yauyau d’in nan ba sai gobe ba sai na cusa mata ba’kin cikin da sai taji zaman gidan nan ya isheta, yau yau d’innan ba sai gobe ba “ ta ‘karasa tana mi’kewa tsaye “ Harry me zakiyi ?” Cewar Hajiya falmata , tsaki Harry tayi kafin ta soma magana “ Babu abunda ya shafeki da abunda zanyi , abu d’aya zakiyi mun ki saka bokan ki ya bani kwallin mallaka, kwallin da duk nacin sa idan ya kalleni dole ya soni , dan sai na ci uban yarinyar can idan na aure sa .”ta ‘karasa tana barin falourn .itama Hajiya falmata d’akin ta tanufa bayan ta suri wayarta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Abla tana fitowa cikin falourn ta tarar da su M.Sarah a tsats tsaye , Sarah na ganinta ta furta “ Welcome Mah , akwai abunda kike bu’kata?”girgiza mata kawai Abla tayi tana ‘kara sowa cikin falourn “ M.sarah akwai abunda nake san tanbayar ki please “, kanta Sarah ta jinjina mata “ Okay “ Abla kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta furta “ Sarah su wanene suke fadawa su Little abinci?” Shiru Sarah tayi kamar mai tunani kafin ta furta “ kamar wad’an da suke sarawa His excellency ne “ d’an shiru Abla tayi kafun ta furta “ Daga yau ina so ki dunga kula da abubuwancin su , hatta abincin su inaso ke da James kun d’auki nauyin kula dashi” da d’an mamaki sarah ta furta “ Madam…” cikin sauri Abla ta dakatar da ita “ kiyi abunda nace karki damu, ayyuka bazasuyi yawa a nan ba tunda ga Jenny “ kanta Sarah ta jinjina mata kafun ta sara mata “ Döne “ d’an murmushi Abla ta sakar mata tare da yin hanyar kitchen , gabaki d’aya mafarkin da tayi ya saka mata ‘kin yarda da kowa , babu abunda ya soma yi mata yawo sai abincin da su little suke ci shiyasa take so James ya cigaba dayi musu abinci kamar lokacin da suke America.