← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 100

Sashe 88

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******** Victor da Anthony kuwa basu bita part d’in ba ganin Big Boss da kanshi ya nufo part d’in sai suka taka masa baya , yana shiga part d’in ba Harry da ta nemo bala’in ba hatta su Fanan sai da suka shiga taitayinsu dan suna bala’in tsoran sa musamman da suka ga baya fara’a kwata kwata , yanzu ma babu fara’ar a fuskar sa , har su Didi
Sai da suka kallesa ganin yau babu M a tattare dashi , cikin Sauri Harry ta ‘boye a bayan Mamy , Daidai lokacin da M.Sarah take shigowa falourn bayanta kuma su Little ne . “ Belt “, ya fad’a da kakkausar murya , Victor ne ya cire belt d’insa na sojoji ya mi’ka masa , bai amsa ba sai ‘kara furta “ Belt “ da yayi , shima Anthony nashi belt d’in ya ciro ya had’e da na Victor , su Little suna ganin haka sukayi reverse a maimakon su shigo sukayi saurin komawar su . “ Sarah “, Big Boss ya fad’a cikin Husky voice d’insa , da Sauri Sarah ta amsa da “ Yes Boss “ tana kar’ban belt din “ beat her off “, ya fad’a har lokacin babu Wanda ya kalla , Su Mamy ne suka zaro ido “ Waza a doka ? Ban fahimta ba ?”, nufo inda Harry take M.Sarah tayi , itama da Sauri ta ja baya cike da tsoro, Babu Wanda Sarah ta kalla ta Julawa Harry belt din nan , cikin tsananin azaba ta gantsare itama tana sakin ihu , tun kafin Mamy suyi magana ma Sarah ta dunga lafta mata belt din nan , babu Wanda baiyi da Sarah ta daka tava amma takı tsayawa , hatta Big Boss tun Mamy na fad’a har ta dawo lallashin amma gabaki d’aya yayi buruş dasu , Uncle bai ce masa komai ba sai Bobo da Sauban da ya kira , suna zuwa ganin abunda yke faruwa suka soma lallashin sa amma gabaki d’aya ya mayar dasu yan iska , ganin yadda Sarah ta soma fasawa Harry jiki ne su His Excellency suka shigo part d’in , da ‘kyar Dadyn su Baby da Uncle suka lallashe sa , izuwa lokacin Harry ko hannunta bata d’aga wa sai kuka da take faman rerawa , cikin muryar sa ta izza yasa Sarah ta kulleta a d’aki me duhu, duk Wanda yayi magana muku yasa a ‘kara mata kwana biyu akan kwana ukun da yace zatayi , gabaki d’aya sai aka rasa mai bakin magana dan tsaf Big Boss zai aikata abunda yace d’in. Bai jira kowa ba yayi ficewarsa zuwa part d’in sa . Lokacin Abla ta farka daga baccin da take jikinta sanye da wani shirt d’insa da ya kusa kawo mata gwiwa , ido d’aya ya kashe mata kamar bashine ya gama tsare gıda ba , ita kuma ta turo ‘karamun bakinta tana furta “ Welcome Sunshine “, ta kowa yayi zuwa inda take kafun ya furta “ Mun shirya aiko ? No more fushi ko?” ‘Dan ya mutsa fuskarta Abla tayi tana girgixa masa kai “- ni ban shirya da kai ba , kuma ai na fad’a maka babu ruwana da kai bari ma na koka can part d’in na dena zuwa nan “, hannun ta Big Boss ya kama “ Babu Inda zaki ‘kara komawa ba , ina da mata ace za’a Mayar dani d’an iska , na gama magana babu Inda zaki koma “, sakin baki Abla tayi jin abunda yace , zatayi magana ya d’auke fuskar sa daga Side d’insa , cikin Sauri ta jiyo ‘bangaran da yake “ please! please ! Haba Sunshine d’in Abla , zan dawo fa “, kansa ya girgiza mata alamar a’ah , cikin marairaice fuska ta furta “ please Sunshine , I promise duk lokacin da kake nema na zanzo kaji please Sunshine , please “. Ta fad’a tana d’an yin d’age hannuwanta kuma ta zagaye wuyansa da shi har saida ya ran kafo da fuskarsa , goshinsa ta soma kısa kafin tayi kissing kumatunsa tana furta “ Please Sunshine “, da ‘kyar ya yadda zata koma shima kuma sai dai ta dunga kwana anan wajan , bata da za’bin da ya wuce ta amince masa , shiyasa kawai ta amince da hakan.  Bata güdü part d’in suba sai da ta tabbatar ya shiga wanka sannan ta güdü ta Inda ya nuna mata jiya , tana shiga d’aki kuwa ko zama batayi ba su Eshaal sukai knocking kofar ta , kallan jikinta tayi ganin shirt d’insa ne a jikinta , hijab din sallar ta tayi saurin zunbulawa ganin an ‘kara knocking, kamar me baccin gaske ta ‘bata fuskarta kafin ta bud’e musu ‘kofar. 

    Tana bud’ewa Baby tayi hugging d’inta tana dariya , d’an zaro ido Abla tayi tana binta da kallo , girgiza kanta Eshaal tayi “ wallahi Baby Allah ya shiryeki duk wani kan mugunta kin fi kyauri a Wajan “ wani dariyar Baby ta kusa sakawa tana kallan Abla da take binta da idanuwa itama “ Ni wallahi abunda yayi ba ‘karamun burgeni yayi ba , kina ganin ta kinga mai Zubin ba’kin hali wallahi “, Abla bata gane kan zan cansu ba har saida suka zauna “ Wai akan wa kuke magana ne ?” Kallanta sukai gabaki d’aya da mamaki ganin bata san abunda ya faru ba , Baby ce ta furta “ Wallahi bikin duka akayi a gidan nan , ni ban ta’ba ganin irin dukan nan ba wallahi , ni Wallhi na jinjina miki da kike tare da mijin ki bai fasa miki kai ba “, ‘karamin tsaki Abla tayi yana kallan su Fanan “ Mai ya faru ?” Gabaki d’aya abunda ya faru Fanan ta zayyane mata har d’akin duhun da ya saka a kulleta , ‘karamun ajiyar zuciya kawai ta saki cikin zuciyar ta kuwa babu abunda ta furta sai “ Weldone my Sunshine “.

      “Tunanin me kike ?” Cewar Eshaal , girgiza mata kai Abla tayi “ No babu komai bari na shirya sai mu sauka yau muyi girki ko ?”, kanta Eshaal ta jinjina mata “ Good idea “, ta shi Abla tayi ta d’auki abunda take bu’kata ta bar wajan , bata fi 5 minutes ba ta fito cikin doguwar material ba’ka plain da babu ko a do a jikinta . Gabaki d’aya sai suka sakko ‘kasa gwanin ban sha’awa suna tafiya suna hirar su , Arwa suka tarar a falourn ciki shigarta itama ga baki d’aya tsayawa sukai suna mata magana banda Abla da tayi kamar bata san taba itama tayi wucewar ta , d’an d’ago fuskarta Arwa tayi ta kalli hanyar da Abla tabi da kallo yanayin fuskarta na canzawa , Eshaal ce kawai ta fahimci hakan shiyasa fuskarta cike da murmushi ta furta “ Girki zamuyi ki taso kema muke tare kar ki zauna ke kad’ai anan wajan “, murmushi Arwa tayi mata tana furta “ Toh “, gabaki d’aya sai suka nufi kitchen din har da harwa , sai da kowa ya fad’i ra’ayinsa akan food din da za’ayi kafun su tsayar da magana d’aya , har lokacin kuma Abla bata kalli ko inda Arwa take ba . 

      Fanan ce ta kallesu “ I’m coming bari na d’auko wayana “, tana fad’an hakan ta fito daga kitchen zuwa falourn su , zata nufi d’aki taga Little a tsaye da alama yanzu ya shigo dan ko zama bai yi ba , ganin Fanan da yayi ne yasa ya saki murmushi sosai , ita kuma Fanan hararar sa tayi zata wuce yayi saurin ‘karasowa inda take “ Wai har yanzu haushina kike ji ? Nace fa am sorry bansan zakuji haushi ba , kuma matata zaki zama fa , Baby ta bani ke fa” wani irin harara Fanan ta jefa masa kamar idanuwanta zasu fad’o ’kasa “ Allah ya kiyaye ya auri yaro “ kallanta Little yayi kafun ya furta “ Nine yaro ? Ban girme kiba ? Ki aure toh sai muga wanene yaro ai , a ranar da aka kai kina ranar zan baki ajiyan ‘Ya’ya na “, yanzu ma wani mugun kallo Fanan ta je fa masa jin abinda yace , zata wuce ya saka hannu ya tare hanyar “ idan baki ha’kura ba wallahi yanzu wajan Yaya Big Boss zanje na fad’a masa , kuma nace yayi mana Aure , kin ha’kura ko baki ha’kura ba ?” Shiru Fanan tayi masa tana hararar sa ganin yadda ta’ki ha’kuran ne yasa shima ya juya “ Okay fine bari na je wajan Yayan “, hararan bayansa Fanan tayi a zuciye ta furta “ Yaushe nace ina gaba da kai ? Ba na ha’kura ba ?” Da Sauri Little ya jiyo yana murmushi “ Dagaske kin ha’kura ?” Kanta Fanan ta jinjina masa alamar eh , Little kamar mai tunani ya furta “ idan kin ha’kura kice ina sona kinji ?” Jin abunda yace ne yasa Fanan ta ‘kara Hararar sa , wayar aljihun sa ya d’auka tare da dialing number Big Boss zai kira tayi saurin dakatar Dashi , “ ka ta’ba ji mace ta furtawa na miji so bayan shi bai fad’a mata ba ?” Dakatawa Little yayi tare da mayar da wayar aljihunsa “ yeah you’re right , toh muma mu fara soyayya sai muyi aure abun mu ko?” Shiru Fanan tayi batare da tace komai ba , kallan abun hannunsa Little yyi kafun ya d’auki guda d’aya sai faman ‘kyalli yake yasa mata a hannunta guda d’aya “ Yau zamu fara soyayyar mu Kinji ? Duk lokacin da kika zauna ki dunga kallan abun hannu na , Ina sanki Amarya to be “, yana fad’a ya juya yana sakin dariya abunshi , kasa motsi Fanan tayi daga ‘kamewar da taji sabida mamakin Little , da ‘kyar ta iya jan nunfashi mai ‘karfi tana kallan abin hannun da ya saka mata , sai kuma ta  harari hanyar da ya bi , Karafff idanuwansu ya had’u , wani irin blow kiss Little yayi mata daga inda yake da ya saka Fanan ba shi ta gudu zuwa d’aki a guje.
Chapter 88 · 0% Book details