← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 100

Sashe 84

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

********
BOBO

Zaune yake gabansa System ne yana operating dinta saki Sauban da ya zuba masa idanuwa “ Dude Anya baka fad’a soyayya ba ?” Hararansa Bobo yayi yana d’auke fuskar sa , wani ‘karamin dariya Sauban ya saki yana ‘kara kallan Bobo “ who is she? “ nan ma shiru Bobo yayi masa “ ka rainani fa Bobo dakai da besty duk yan iska kuke san Mayar dani ? &/8 ma soyayyar ka fad’a ? Ni kuma ku barni a tuzuru?” Hannu Bobo ya d’aga masa alamar ba ruwan shi, lokaci d’aya kuma yadda Eshaal ta furta “ Na gode lokacin da ta ‘buya a bayansa , murmushi ne ya su’buce masa da har saida Sauban ya Kai masa duka “ Bana san wannan iskancin fa , ko da yake Nima zan baku mamaki sai dai kuji an d’aura kawai , “ ganin yana san damun sa da surutu ne yasa Bobo ya d’auki System d’insa “ idan tayi wari ai zamuji, ni kuma ba sace mun zuciya akai ba “, ya fad’a yana shigewa cikin bedroom d’insa . 

************
BLACK SPIDER

     A kulle hannunta suke cikin ankwa , gabaki d’aya a galabaice take Sabida tsananin azabar da take ji, nunfashin ta ma da ‘kyar yake fitowa Sabida wahala , ga d’akin da yake cike da matsananin duhu, lokaci d’aya kuma wani haske ya cika d’akin ga ‘karar tafiyar takalli da take ji cikin kunnuwanta amma babu damar ta motsa jikinta Sabida ta ko ina bata iya motsa ga’b’ban jikinta , Wanda ya shigo gabaki d’aya ba’a ina gane kamannin maca ne ko namiji ta ko ina an’boye wannan damar , har Inda take ya ‘karasa wajan tare da tsugunnawa ‘kasa , zai ta’ba mata fuska cikin Sauri ta bige hannunsa duk da yadda take jin ta a jiga ce , dariya ce ta karewa wajan kafun ya dam’ki gashin kanta “ kina da taurin kai , zuri’arki ma hakan , mijin ki ya mun abunda ya ‘kona mun rai Wanda Nima sai na wuce hakan akan ‘ya’yan ki , kisaka a ranki nan da d’an lokaci ‘kan’kanin ‘ya’yanki zasu zama gawarwaki, a gaban idanuwan ki kuma za’ayi layyar namansu mu bawa gumakan mu , da’kyar ta iya d’ago da idanuwanta muryarta har bata fita sosai ta furta “ Ya.. na.. ina ?” Jefar da ita yayi a ‘kasa da ‘kafarsa d’aya kuma ya daka mata ‘kafa har saida tayi ‘kara , wata waya ya ciro a aljihun sa tare da yin wasu danne danne a ciki yana ‘kara tsugunnawa ‘kasan , Daidai saitin fuskarta ya Hasko mata wayar , da Sauri ta d’ago idanuwanta , hannunta har karkarwa yake lokacin da kar’bi wayan , wani mutumine a d’aure cikin wani abu , da alama suma yayi dan ko nunfashi bayani ga jini ta ko ina da ya ‘bata masa fuska, Sabida yadda gashinsa yayi tsaho sosai ga Jinin da ya had’e dashi ne yasa ta fashe da kuka , ‘yan yatsun hannun su ta kalla da babu guda biyu da alama yanke wa akai dan har lokacin jini bai dena fita daga Wajan ba , Sosai take kuka tana kallan jikin wayar , ita kad’ai sai faman girgiza kanta take “ Allah bazai barku ba , wallahi kun kusa d’aukar hukuncin ku a tafin hannun ku , mugaye Wanda babu Allah a ransu “, bata ‘karasa ba aka d’auke fuskarta da mari “ Idan kika ‘kara anbato mana sunan abun bautanki sai mun kashe sa sannan mu kashe ‘ya’yan naki suma “, Ta san kad’an daga cikin mugancin süne shiyasa bata kuma cewa komai ba sai kukan da take yi mai fita tundaga ‘kasan zuciya , zuciyarta fall tsine musu take tana kai ‘karar su wajan Allah gagara misali, mutuminnan hannun sa kawai ya ‘kyasta , cikin ‘kan’kanin lokaci ya ‘bace , d’akin ya ‘kara duhu kamar d’azu.

 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨

8:25pm tsaye Abla take a gaban mirror tana ‘kara bin jikinta da kallo , sanye take cikin doguwar Abayar da M.Sarah ta kawo mata , sosai flowers din jikin abayar suka fito sosai kamar green , ga mayafin jikinta shima kalar Green , hatta hand pursed d’in hannun ta green ce , sai faman kallan kanta tare a jikin madubi, ga Tuna’nın yadda zasu fita duk ya cika mata zuciya , tana tsaye a gaban madubi ya shigo d’akin, sosai idanuwansu ya shiga cikin na juya , ko wannansu yana bin d’an uwansa da wani irin sahirtaccen kyau , kusan kayan su irin d’aya ne colour d’in, ga gyaran gashin kansa da ya Fito sosai , da hannu yayi mata alamar ta ‘karaso wajan sa , babu musu ta ‘karasa tare da hugging d’insa “ Kinyi kyau Sunshine “, murmushi  tayi kad’an kafun ta furta “ Ai ka fini kyau “, dogon hancinta da yake yawan ja ya ‘kara ja yanzu tare da kama hannunta guda d’aya “ let’s go “ sai a lokacin ta marairaice masa , da ido yayi mata alamar Menene , shiru Abla tayi kafun ta furta “ zasu gan mu    fa” kallan ta yayi shima kafun ya furta “ And ?” Hannunsa Abla ta ri’ko cıkin nata “ Ni banaso su ganmu Sunshine please “, yadda tayi magana dole ga sakashi lumshe idanuwansa , hannu nata ya ri’ke cikin nasa kafun ya furta “ it’s okay they won’t find out , let’s go”, bai bata damar kuma magana ba ya ja hannunta suka soma tafiya , Abla duk a tunaninta zasu sakko ‘kasa ne , amma da mamakinta sai taga ya nufi wani hanya da ita cikin part d’in , turn print d’insa ya saka lokaci d’aya wata ‘kofa ta fito ne kama da wajan karatu , Abla babu abunda take sai bun wajan da kallo ganin kamar under ground suka shiga, hannunta ya ri’ke sai da suka d’anyi tafi kad’an kafun ya ja hannunta zuwa left side , a nan ma sai da suka d’anyi tafiya zuwa wani  ‘kofa , kamar d’azu turn print d’insa ya saka ‘kafar ta bud’e , suna shiga Wajan falourn su ya bayyana “ sakin baki Abla tayi tana bun wajan da kallo , ido d’aya Big Boss ya kashe mata har lokacin hannunsa yana cikin nata , basu zauna a falourn ba suka fito inda motocin Big Boss suke , da kansa ya bud’e mata wata farar Lamborghini , kafin shima ya shiga , sosai cikin motar ya had’u musamman doguwar kujerar da take wajan har mutum zai iya kwanta wa ga abunsha da yake kan wani center ne ‘kyau. Ba a d’auki mintuna ba motocin suka soma tafiya , Big Boss da Abla kuwa suna cikin mota suna shan Love d’insu ga Abla da take faman zuba shagwa’barta san ranta . 
Chapter 84 · 0% Book details