← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 100

Sashe 10

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****Abla tana fitowa daga d’akin Big Boss a falour ta tarar da su Little , murmushi ya sakar mata shima lokacin da ya ganta . “ Lil tun d’azu fa nake neman ki , hope yaya be miki fad’a ba ? Kuma ya yadda mu zauna ko ?” Cikin sauri ta girgiza masa kai tana matsowa inda suke a zaune “Na gyara masa d’akı ne fa , shiyasa baka ganni ba “, da kansa ya jinjina mata batare da ya sake cewa komai ba , itama mayar da kallan ta side d’in prince tayi tare da ambatan sunan sa “ Yaya Prince ?” ,shiru prince bai amsa mata ba , ga phone da take hannun sa gabaki d’aya ya mayar da hankalin sa kanta . Sai a karo na biyu da ta ‘kara kiransa ya d’ago da eyes d’insa “ Sorry Lil banji ki ba sai yanzu “, wata tanbayar Abla ta jefa amsa “ Amma Yaya prince Tuna’nın me kake haka ?”, d’an iska prince ya fesar daga bakin sa kad’an “ ba wani abu bane mai muhammanci, just I’m feeling everything here strange , ban ta’ba zama a wani waje ba kuma nayi feeling like am home kamar nan, sai kuma gida idan muna tare duka , and ko lokacin da nake school I didn’t feel so very comfortable like this ba , the people and everything here , mai yasa suke san zaman mu a tare dasu bayan bamu had’a any connection dasu ba or that means” yan ‘karasa yana kallan Little , shima little cikin Sauri ya mi’ke tsaye , “ No yaya prince , please don’t think something else okay ? Bana so “ ganin yadda lokaci d’aya ya soma had’a zufa ne Abla ta furta “ ka kwantar da hankalin ka yaya Little kaga kana bani tsoro “ ta ‘karasa tana marairaice Fırst kamar me shirin yin kuka , cike da wasa little ya kashe mata ido d’aya “ Dont worry Lil, I won’t scare you, babu abunda ya same ni , kunga yanzu time d’in sallah yana ‘ko’karin wuce wa , let’s pray first , but Lil zaki mun fresh fruit salad kafin na dawo ?” ‘Dan dukar kafad’an sa Prince yayi “ tayi maka ko tayi mana ? Little Yaushe ka koya rowa ?” ‘Dan karamin gwalo little yayi masa “ Nidai bazaka wahalar mun da sister ba , Lil byee ! See you “ itama waving hannun ta tayi musu kad’an tana murmushi. Suna barin falourn itama ta nufi d’akin da ta kwana jiya , bata tsaya ‘bata lokaci ba ta wuce toilet dan tayi alwala . 

      Ko cikakkiyar mintuna 2 batayi a cikin toilet d’in ba , wata irin ba’kar halitta me kama da tsaka ta bayyana a cikin d’akin, ga idanuwan halittar da suka kasance ba’ka’ke sosai , sai faman bud’e dogon harshen ta take tana fesar da wani abu me kamar ruwa a cikin d’akin, ta ko ina sai yawo take da ta tunkari hanyar shiga toilet sai ta juya ta koma wani wajan , ta dad’e tana ‘ko’karin tunkarar toilet d’in da Abla take ciki amma sai ta fasa ta nufi wani side d’in. ‘Ko’karin bud’e toilet d’in da akai ne ba’kar halittan nan ta ‘bace gabaki d’aya kamar bata ta’ba wanzuwa ba , Abla tana fitowa daga toilet d’in bakin ta d’auke da addua har ta d’auko daddumar da zatayi sallah akanta bayan ta nad’a dogon veil d’in ta .      

     Tun a cikin sallah Abla take jin ‘kafarta kamar tana mata zafi , amma gabaki d’aya bata mayar da hankali kai ba , Har ta idar da sallar ‘kafarta ba ta dena zafi ba , gaban mudu’bin d’aki ta ‘karasa ko zata samu man zafi, cikin sa’a kuwa ta samu , tundaga kan kwiwar’kafarta da take mata zafi ta soma shafawa har zuwa tafin ‘kafarta . Tafi mintuna 10 a zaune a wajan tana murmuza ‘kafarta , agogon d’akin ta kalla cikin sauri ta zaro ido ganin time na ‘ko’karin wuce wa ko fruit bata yankawa su  Little ba , cikin dauri Abla ta fito daga cikin d’akin ganin zafin da ‘kafar take mata ya ragu sosai ba kamar d’azu ba , bata sha wani wahala ba  wajan neman kitchen ba, duk da yadda ko ina na cikin kitchen d’in ya ‘kayatu da kayan more rayuwa , bata tsaya ‘kare masa kallo ba ta wuce wajan fridge d’in kitchen d’in, cikin sa’a ta samu fruit d’in kuwa da alama ba ‘a dad’e da kawo su ba dan ko sanyi basu gama yi sosai ba . Batare da tunanin komai ba Abla ta d’ebi iya amount d’in da take so tayi anfani dashi, kamar ance ta kalli fruit d’in da ta d’ebo sai taga d’aya zaga cikin su kamar ya soma lalacewa amma idan ka kallesa a waje bazaka kawo hakan ba , da knife d’in hannun ta da ta d’akko kawai ta cakawa fruits d’in lokaci d’aya ya bata sautin tasss kamar fashewar abu, cikin ‘kan’kanin lokaci idanuwan Abla suka soma kakkafewa kafun ta fad’i kasa kamar matacciya . Fad’uwar da tayi ko yan sakin ni ba’ayi ba Apple d’in data caka wa wu’ka ya ‘bace gabaki d’ayan sa . Sai wani ba’kin haya’ki da ya fito daga Apple d’in yana ‘ko’karin hawa  kanta kusan sau biyu , kafun yaja baya kad’an shima ya ‘bace.

****** Suna fitowa daga masallaci Little ya kalli sauban, kamar me tsoran masa magana ya furta “ baka fad’a mun abunda zanyi su yaya su dena fushi ba , kallansa Sauban yayi kafun ya d’an saki murmushi yana girgiza kansa , “ Ni bazaka iya cemun yayan ba ?” ‘Dan shiru Little yayi masa yana sauke kansa , wani murmushin sauban yayi “ its okay ! You dont have to, akwai 3 things da yayanka yake so sai , 1 rose flowers, Pet d’insa lion and this “ ya ‘karasa yana mi’kowa Little wani ‘karamar alawa “ cike da mamaki Little yake kallansa dan gabaki d’aya abunda ya lissafo yasan yayan sa yana so banda alawar da sauban ya mi’ka masa , ganin yadda mamaki yafito sosai akan face d’insa ne ya kara bawa sauban wani murmushin “ karka damu nasan kaima baka sani ba , ni kad’ai nasan wannan sweet d’in , zaka iya basa “ ya ‘karasa yana juyawa cikin sauri little bakin sa har yana d’an rawa ya furta “ wait “ tsayawa sauban yayi yana kallan Little da ya d’an sunkuyar da kansa , cikin rarrabewar kalla ya furta “ ka ‘batawa yaya na sosai but kana da kirki ka bashi ha’kuri zai ha’kura ,” sai kuma ya saki ‘karamar ajiyar zuciya “ Ya..ya sauban” waro idanuwansa Sauban yayi akan little yafun ya ‘kara matsowa kusa dashi “ Me kace ? ‘Kara maimaita mun please!” A karo na biyu Little ya ‘kara furta “ Yaya sauban”, hannun sa d’aya sauban ya mi’ko masa “ can i have a hug please?”fuskar little d’auke da murmushi yayi hugging Sauban, shima sauban hugging d’insa yayi sosai a jikinsa kafun ya furta “ I really missed you!”gudun kar Little yaga yadda eyes d’insa ya soma ja ya kawar da kansa “ So are you happy ?” Kansa Little yayi masa knodding yana murmushi , shima sauban martanin murmushin yayi masa “ okay zo muje na baka rose flower “ dagaske kana dashi ? Kasan favorite rose flower d’in sa ?” Hannunsa Sauban ya ri’ke lokacin da suka soma tafiya “ Ni nake d’aukar masa su duk lokacin da mukaje su yi su , I really like it with perfume inside and no more questions okay?” Shima Little okay yace masa yana ‘kara sakin wani murmushin. 
   ************
Cikin wani garden da ya gaji da had’uwa mai d’auke da kalolin flowers masu sanya ya zuciya , wasu yan matane zazzaune kan wasu chairs ko wannan su akwai abun ciye ciye agabansu , ga wasu yan aiki da gabaki d’aya suke a tsugunne, d’aya daga cikin su da take sipping wani smoothie ne ta ya tsuna fuska , a daidai fuskar d’aya daga cikin masu aikin ta watsa tana jan dogon tsaki , a masifance ta furta “ wannan wana irin iskanci da gida dumanci? Dan ubanki haka a ka koya muku yin abu ? Ku komai baza kuyi shi in a class way ba sai kun ‘bata ? Banza yan gidan matsiyata da baku gaji komai ba sai tsiya, dallah malama tashi kije ki had’o mun wani “ cikin sauri yar aikin da ashekaru zata girmeta nesa ba kusa ba ta soma bata ha’kuri , wani tsakin matashiyar budurwar taja “ idan baki matsa a nan ba sai na tsinka wa wannan shegiyar fuskar taki me kama da ta buri mari, banza d’iyar talakawa “ d’aya daga cikin ‘yan matan da ta kai yankan Apple bakin tane ta ‘kyal’kyale da dariya “calm down Surry , kinsan duk abunda aka had’a da matsiyata dole ran mutum ya ‘baci musamman idan kika yi duba da tsiyar dake tattare da su “ gabaki d’aya ‘yan aikin sun kuyar da kansu ‘kasa sukai sabida irin mugun kalamar da suke jefa musu , duk da bayau ne farau ba idan da sabo ya ci a ce su saba da kalan wula’kanci da yan matan nan suke musu kala kala . 
Chapter 10 · 0% Book details