← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 100

Sashe 22

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

✨✨✨✨✨✨
‘Karfe 8:20pm zazzaune mutanan gidan suke cikin ‘kayataccen falour me d’auke da set d’in kujeru har guda uku, tundaga kan ‘yan matan gidan har kan sauran iyayensu mata da maza daga gefe guda ma Diidi zaune da Nani suna tattaunawa kowa ka gani zaka ga face d’insa a sake kamar babu damuwa a tattare da shi, Little da prince ma suna zaune kan wani sofa Diidii ta saka su agaba a dole sai sunyi hira ga masu aiki da suke faman zarya da abubuwan sha kala kala , shigowar su Bobo ne yaja hankalin ‘yan gidan da Sauri Little ya furt “ Yaya Bobo , Yaya sauban please help me , ta’ki barina na tafi” ya fad’a yana ‘ko’karin mi’kewa ,sandarta ta d’aga yayi saurin komawa ya zauna , d’an murmushi Bobo ya saki kafun su zauna shima “ Don’t Worry Little , Soon za’a kawo maka Simba , Okay? Wani irin shegiyar dariya Little ya furta “ Yawwa Yaya Bobo that’s why I love you “, Nifa ?” Cewar sauban , “ I also love you so much Yaya Sauban”, shima prince kallansa yayi kafun ya furta “ Nifa ?” ‘Dan gwalo Little yayi masa cike da tsokana ya furta “ $50,000” harararsa Prince yayi yana d’auke Kai , shigowar His excellency dasu uncle Adam ne yasa gabaki d’aya mutanan falourn Suka mi’ke banda Bobo da ko kallan side d’in da yake beyi ba , suma su Little kallansa suke amma bazasu iya zuwa wajan saba Sabida basaso ran Bobo ya ‘baci “Shima His excellency bai ce musu komai ba dan sarai ya fuskanci yanayin su, akan wata white chair ya zauna kafun ragowar mutanan gidan su zauna suma ,  Su Yasmeen sai faman satar Kallan su Bobo suke yadda suka ga shigar sa ba’karamun tafiya da imânın su yayi ba kowa addua yake Allah yasa Big Boss ya shigo falourn . Kusan mintuna 10 da shigowar His Excellency wata siririn murya tayi sallama , gabaki d’aya mutanan gidan d’ago da kansu sukai zuwa inda suka ji muryar tana tsaye cikin wani black d’in abaya da ta zo mata har ‘kasa sai golden golden d’in ado dake falan walwali a jikin rigar gabaki d’aya kallan ta suke kamar zasu cinyeta yadda tayi rolling mayafin ta sai ta fito sak kamar balarabiyar, Little na ganin ta yayi saurin mi’kewa tare da nufo inda take “ am so sorry Lil tun d’azu naso zuwa wajan ki amma bakiyi fushi ba ko?” ‘Kin Kallansa Abla tayi kafun ta furta “ Ni fushi nake da kai yau gabaki d’aya ban ganku ba fa “ hannu Little ya saka wajan kunnan sa “ we’re sorry Lil kinji ?” Kanta ta d’aga masa “ Ai na ha’kura “ murmushi Little ya sakar mata “ you look more than beautiful Lil “, d’an kunya ne ya kama Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa , muryar prince ne ya sa tayi saurin d’ago da face d’inta “ You look so gorgeous Lil , kinyi kyau sosai “, da Sauri ta ‘kara sun kuyar da Kai ganin idanuwan gabaki d’aya gidan suna kallan ta , kasa motsawa tayi gabaki d’aya ta tsargu, hannun ta Little ya kama suma ‘karaso cikin falourn , akan kujeran kusa dashi ya zaunar da ita, cike da girmamawa Abla tayi saurin sakkowa ‘kasa tana gaishe da His Excellency, murmushi His excellency yayi sosai kafin ya furta “ Allah ya albarkaci rayuwar ki “ cikin zuciyarta ta amsa da amin kafun ta gaishe da sauran mutanan falourn , su Harry sai faman bankamata harara suke daga nesa dan a ganin su munafurci ne kawai Abla take . 

“Are you okay Lil ?”cewar Bobo , cikin Sauri Abla tayi knodding kanta “ Lapiya ta ‘kalau Yaya Bobo”, okay have your seat “ cewar Bobo, kasa zama akan kujerar Abla tayi ganin duk manya ne akan kujeran shiyasa ta samu waje ta zauna a ‘kasan, gabaki d’aya sai suka ‘kara kallanta ganin sabon abu dan hatta yaran gidan babu ruwan su da wasu manya zama suke akan kujera. Little ne ya matso kusa da ita cikin ‘kasa ‘kasa da murya ya furta “ Lil ki Tashi ki zauna akan kujera mana “ kanta ta girgiza amsa alamar ah’ah , itama Cikin ‘kasa ‘kasa da murya ta furta “ idan manya na zaune akan kujera ba’a zama a kai sai azauna a ‘kasa , haka malam Şule yace mana “, wani irin murmushi His excellency da Diidi sukai dan karaf sunji abunda tace lokaci d’aya wani irin soyayyar yarinyar ya shiga zukatansu, hatta Bobo da sauban sarai sunji abunda tace shiyasa Bobo yayi murmushi kad’an , juya wa Little yayi Wajan prince ya rad’a masa abu a kunne  “ okay “ cewar prince kafun shima ya sakko ‘kasan sai gabaki d’aya suka zauna a ‘kasan shi da Little , “ Thank you Lil “ cewar little , wata me aiki ce ta ‘karaso Wajan hannun ta d’auke da drinks , Daidai saitin su Abla ta ‘kasa tare da zuba musu, guda d’aya little ya d’auka ya mi’kawa Abla , “ oya you need something cool and karma kice mun bakyaso no more excuse “, Zatayi musu Little ya Harare ta “ Na gode “ ta fad’a a hankali Abla ta d’auki cup d’in zata saka a bakin ta kamar daga sama taji saukar muryarsa cikin dodon kunnan ta “ Drop da drink “ ba ita kad’ai ba gabaki d’aya mutanan falourn kallan sa sukai kowa da kalar kallan da yake binsa dashi , sa’banin d’azu yanzu ba’ka’ken kayane a jikin sa na kafanin prada da suka yi mugun amsar sa ydda Harry take kallansa kamar wata tsohuwar mayya ita kad’ai sai faman had’i yar yawu take , cike da mamaki suke kallan sa babu Wanda ya kalla a cikin mutanan falourn ya soma takowa cike da izza batare da ya kalli kowa ba ya furta “I  change the rules “, Hajiya saudatu da tafi kowa ‘kulawa ta mi’ke tsaye “ Me kake nufi ne ? Haka ka canza mana masu aikin mu akan Wana dalili ? “ cikin husky Voice Big Boss ya furta “ Sabida abunda nace kenan ya ‘karasa yana binta da wasu irin kallo “, itama a zuciye ta furta “ akan Wana dalili zaka canza mana su ? Karka manta yan aikine talakawa ne kuma dole su bauta mana bawai ace za’a nuna musu tausayi ba dan haka dole su bauta mana sabida sud’in ‘kan ‘kan tattune “ wani irin kallo Bobo da sauban suka jefa mata hatta His Excellency kallan ta yayi batare da ya furt uffan ba , “ ‘ ya’yan ku fa ?” Sai faman hura hanci Hajiya saudatu take kafun ta furta “ kai ma kasan sudin yarane da suka taso cikin daula da jin dad’i jikin su basu yi maka kala da masu shan wahala ba ai “, kansa Big Boss yayi kad’an kafun ya furta “ Abdulmaleek Bobo!” Mi’kewa Bobo yayi tare da sara masa “ Yes sir “ d’an matan dake zaune duk gabaki d’aya akan ku jera ya nuna da hannu kafun ya furta “ duk yaran nan da suke zaune kan kujera inaso daga yau su zasu dunga yin aikin gidan , masu aikin gidan kuma sun samu ‘yancı , “ gabaki d’aya sai su Harry suka zube ‘kasa iyayan su kuma suka mi’ke zasu fara magana Big Boss ya furta “ Add Some manners to them “ ran Hajiya falmata ne ya soma ‘baci itama ta furta “ me kake ta’kama dashi ne ? Yayan namu kake san Mayar wa bayi kome “, lips d’insa Big Boss ya cije kad’an , Diidii na zaune itama ko uffan bata ce ba dan itama so take ya koya musu hankali Sabida sam basu san darajar talaka ba ,” masu kula da flowers suma su dakata yaran gidan zasu yi” gabaki d’aya sai suka saki baki suna kallansa , “ if some dare ya karya mun doka “ ya ‘karasa yana juyawa , a ‘kufule Hajiya Karima ta furta “ Me kake nufi da ‘ya’yan mu ? Ita kuma wannan shegiyar yarinyar mai kama da aljanu fa ? Wacce ita da ko sanin ta bamuyi ba , wani irin murmushi Uncle ya saki yana Kallan Big Boss da ya d’ago ya jefa wa Hajiya karima wani irin kallo, “ A rufe account d’in kowa , duk mai bu’katar anfani da kud’i sai ya nemi izinin ta “, yanxu ma a zuciye Hajiya Karima ta furt “ sabida wacece idan banda ‘kas “ kalmar da ya fad’a ne ya hau tsina kowa da yake falourn , cikin ido ya kalli Hajiya karima kafin ya furta “ Sabida Matata ce ita “…

IBTISSAM
      ( A heart touching story of love and destiny)

Story & written 
      By
Mss Lee   

 09134652921

    TALLA!! TALLA!!! TALLAH !!!!!!!

SHIN KUNSAN WACECE HAJIYA NUSAIBA BR~B ZURU ?❤️

HAJIYA ~ NUSAIBA DR~B ZURU

MAMALAKIYAR ZIMH ISLAMIC AND MEDICINE DAKE RINGH ROAD A KANO NIGERIA
Tazo muku da ingantattu ko sahihan magungunan mata masu inganci, ba’anan kad’ai ta tsaya ba har da na cututtuka da Turarukan wuta , Humra masu shegen ‘kaushi . Abun Alfaharin kuma tana bada sarı cikin sau’ki, sannan kuma suna aikawa duk inda mutum yake afad’in duniyar nan. 

Duk wacce ta siya magungunan Hajiya Nusaiba Dr B zuru, taga be yi mata aiki ba tazo za’a dawo miki da kudin ki . 
Ft

KA’DAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKE SIYAR WA

1️⃣ Hadin amarya
2️⃣Hadin mai jego
3️⃣Hadin sabon budurchi
4️⃣Hadin Kaza Yar’Suddan
5️⃣zuma -Tsumi- Tabaje da sauransu
6️⃣Turaren Sandal ruuu& flastic Sandal
7️⃣ Hadin Hawwi domin inganta zafafiyar kauna
8️⃣Hadin bagadad,kahlij,kajiji,gafgaf dasauransu
9️⃣Hadin humra soyaya dole ta matan aure da normal humra

DON SAMUN ‘kARIN BAYANI KU NE META TA WANNAN NUMBER KAMAR HAKA : 
    08133647913 

   KANO NIGERIA 

LOCATION: RING ROAD BAYAN GİDAN MAN NAZARGO.

       SIYAN NAGARI MAIDA KU’DI GIDA

PAID BOOK

BOOK 2 
         S_____ 7

      NOT EDITED
Chapter 22 · 0% Book details