Sashe 20
Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
“Sandilu! Sandilu! Sandilu!” Shine abunda take faman furtawa gabaki d’aya kamar a hargitse take sai faman kiran sunan Sandilu take hankali a tashe ga wani irin ba’kin hayaki data turnu’ke d’akin dashi, wani irin dariya ne mara dad’in ji ya karad’e ko ina na cikin d’akin “ kinyi sake , kinyi saken , karo na farko da kika kasa cika aikin ki , tabbas wannan karan aikin ki ba mai sau’ki bane kamar yadda kike tunani, yarinyar nan hatsabibiyar kanta ce itama a kwai Wanda ya bata kariya da ace tayi wannan ihun da babu makawa zata haukace, ‘kafar ta da aka tura jariri yayi feshi da ta sosai cikin daran nan tabbas sai ta zama gurguwa, kinyi babban sake sabida tana da mai Kareta Wanda baki isa ki ta’bashi ba ko ki ta’ba wani nasa idan har yananan , kiyi gaggawar fuskarta matsalar ki dan tabbas idan yarinyar nan ta farga sai ta zamar miki babban bala’in da bazaki iya tsallakewa ba , tabbas shigowar ta cikin ahalin nan kamar wani kariya ne ya shigo musu dan tabbas cikin ‘kan’kanin lokaci zata tarwatsa ko wana irin mugune , ita d’in garkuwace ga ahalin, hahahahah hahahaha “ ya ‘karasa yana ‘kara washe wa da wani dariya , cike da firgice matar da take sanye cikin jajayen kaya ga fuskarta da take rufe da jan kyalle shima ta furta “ Tuba nake sindilu, kaine me share mun hawaye, kai ne me cikamun burina, cikar bu’katuna suna hannunka , ya sindilu, a hallakata kawai ko kuma wanda yayi gigin shiga gonata , ba ma ita kad’ai ba , ina so a kashe mun ‘karamun cikin su Wani irin tsawa Sandilu ya daka mata da yasa ta firgita kad’an “
Hakan kamar ganganci kike da rayuwar ki , idan har garkuwar su tana rabe bazaki ta’ba cin galaba akan suba baki da za’bi sai abu d’aya , tabbas sai kin kawar da yarinyar nan sannan zaki samu cikar burin ki, a cikin ‘yan kwana kinnan Jini zai zo mata , ki tabbata kin kawo jinin al’adarta na tsawan kwana kin da zatayi shi,idan ba haka ba tabbas zaki saka cikin babban hatsari dan tabbas tafiki hatsabiban ci , bata da tsoro sannan bata shakkar kowa “,
A razane ta furta “ Tuba nake sandilu, na tabbata idan na kashe yayan su aikina zai zo da sau’ki wani dariya Sandilu ya ‘kara saki “ babu abunda kika isa kiyi masa ko kuma sauran masu binshi da sharri da hatsabibine shi da ya wuce duk wani tsabibanci naku, mutum me ri’ko da addina kamar ‘yan uwan sa dan haryafi yan uwansa ri’ko da addini, baya bacci sai ya shirya kullum da ido d’aya yake bacci d’ayan kuma yana kan kowa , kiyi taka tsantsan dashi , duk lokacin da kika shiga gonar sa babu mai iya fiddaki dan ba’karamun mummuna aiki zai yi miki ba , ki tabbata kincika aikin da na Sakaki idan ba Haka ba zaki
Rushe masarautar da kika d’auki dogon shekaru kina ginawa da sauran Wanda suka fiki buri, dan ina hango wasu taurari guda biyar da zasu bayyana a lokaci d’aya , bayyanar su kamar matakin rushe mugun ayyukan kune dan tabbas zasu zama garkuwa, abunda aka bunne zai fito fili , musamman idan Jini da Jini suka had’u tare da bayyanar Jini a cikin Jini, hahahaha had’uwar Jini , had’uwar Jini , tabbas wani Jini zai samar da Jini kamar yadda Jini da Jini zasu had’u su bayyanar da wani jikin, hhhhhh”, Cikin ‘kan’kanin lokaci kuma d’akin yayi tsit sai kururuwan ta da yake tashi ta ko ina “ bazai yuba , bazai yuba , tabbas zan cika burina ko hakan zai zama silar zubar Jini bazan ta’ba bari hakan ta faru ba dole na samu abunda nake so , dole, dole “ cikin ihu take magana kafun ta murza Jan zoban hannun ta, lokaci d’aya ta ‘bace gabaki d’aya daga cikin d’akin duhun.
A ‘bangaran su little ma gabaki d’aya hankalin su a kwance yake , yau a part d’in Friend suka kwana batare da sanin Bobo ko Big Boss ba , tun bayan lokacin da sauban ya kirasu har zuwa yanzu da Suke bacci hankali a kwance cikin ‘kayataccen Bedroom d’in His excellency da babu Wanda ya ta’ba shigo masa cikin bedroom d’in sai su Little suke kwance kan king size bed d’insa . Sosai ya zuba musu ido yana kallan yadda suke bacci ga al’kuranin dake hannun sa , d’an ‘karamun murmushi ya saki har yanzu yana kallan Little kafun ya gyara masa duvet d’in sa,daga gefen sa kuma wani daddad’an karatun Shureim ne ya ke tashi a hankali, “ I hope you can forgive me a little one day “ ya ‘karasa yana lumshe idanuwansa kamar yadda Big Boss yake , sosai ya raba dare a wajan su lokaci zuwa lokaci yana sakin murmushi , ga kyakkyawan fuskar sa me cike da dattako da annuri da tafito sosai akan face d’insa .
****** Abla kuwa da’kar ta iya fitowa ta daga cikin dressing room d’in ta duk a tunanin ta Big Boss na cikin d’akin , sai da ta gaji da tsayuwa dan kanta sannan ta ha’kura cikin sand’a ta le’ko da kanta , ganin baya cikin d’akin ne yasa ta saki a jiyar zuciya mai ‘karfi kafun cikin Sauri ta ‘karasa wajan ‘kofar d’akin sai da ta tabbatar ta sawa ‘kofar lock tukunna ta iya kwantawa tana hararar ‘kofar “ sai naga ta inda zaka shigo , “ ‘Dan isk…” bata ‘karasa fad’an abunda zata fad’awa ba sabida tuna warning d’in da yayi mata , cikin Sauri ta rufe bakin ta kafin ta janye tana d’an ta’be face d’inta “ Oho dai koma menene Allah sai ya saka mun ai ..” .
〰️〰️〰️〰️〰️
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
WASHE GARI
Kamar yadda Big Boss ya bada umarni gabaki d’aya tsarin gidan sai da su Victor suka canza shi , tundaga kan tsarin securities d’in gidan har kan zuwa wasu daga cikin ‘yan aikin gidan sai da suka canza hakan kuwa ba ‘karamun tayar da hankalin wasu daga cikin mutanan gidan yayi ba .
***** Hajiya karima ce tsaya a cikin falourn ta sai faman zagaye take ita kad’ai ga waya dake kare akan kunnan ta , ita kad’ai sai faman bala’I take “ Ni d’an iskan yaran nan zai yi wa haka ? Me yake nufi da canza securities d’in gidan nan? Ni duk ba wannan ne ma ya ‘bata mun rai ba taya za’ai a ce an canzamun masu aiki gaskiya hajiya sa’adatu dole muyi wani abu,” Ban ji me aka ce mata ba sai wani tsaki da ta kuma ja kafun ta nunfasa “ kina ganin yaran nan baya ganin kowa da daraja ai , ga idanuwansa da kallo ya yi maka sai zuciyar ka ta buga sabida fargaba , idan ke bazaki d’auki mata ki ba gaskiya ni zan d’auka , idan babu masu aikin taya zamusan abunda ke faruwa a cikin gidan ? Ai yayi kad’an wallahi ,ki bari anjima tunda ana had’uwar cin abinci agaban uban nasa zanyi maganin sa “, ta ‘karasa tana kashe kiran ta , kamar tayi hauka haka take jinta musamman ‘yar le’ken ta da aka canzawa waje Wanda ita kad’ai ta yadda da ita a cikin masu aiki Sabida ta fi kowa kawo mata rahotan abin da yake faruwa .
**** A ‘bangaran Hajiya sa’adatu ma rai a’bace ta ajje wayarta sabida ba’kin ciki da ya cika ta fall ko ta kan Yasmeen da ke magana bata biba yayi wucewarta d’aki tana dialing wata number .