Sashe 68
Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****Knocking d’in ’kofar akai a hankali ka fun a turo ta, ta canza shiga yanxu wani dogon material ne a jikinta mai flowers kala kala sai d’an kwalin kayan da ta d’aura duk da hakan uban tulun gashin kanta bai rufe ba duka. Hannun ta d’aya d’auke yake da flask d’in da tashigo da shi mai d’auke da cups akansa, “ Assalamu Alaikum”, cewar Abla, motsa bakinsa kad’an Big Boss yayi duk da sautin bai fito ba amma da alama sallamar ya amsa . Akan center d’in ta ajje tray d’in tana wasa da ‘yan ya tsunta kad’an kad’an , cikin girmamawa ta d’an du’ka duk da baya kallanta ta furta “ ina … kwana ?”, shiru Big Boss yayi mata ba tare da ya motsa ba ko kuma ya tanka mata ba, hannun ta Abla da take wasa dashi ta d’an matsa cikin ‘karfin halin da ta d’ora wa kanta ta ‘kara furta “ Ina kwana ?”, yadda ya ‘ki kulatan ne yasa Abla ta juya zata bar wajan ya ri’ke hannu nata , d’an turo baki Abla tayi kad’an tana kawar da kanta gefe , bud’e idanuwan sa Big Boss yayi akan ta , sosai yake ‘karewa shigarta kallo, yadda ta d’auke kanta akan sa ne yaşo sashi ya murmusa sai kuma ya janyo da ita jikinsa yana d’orata a laps d’insa “ Look at me “, kamar Wanda ya zugata sai ta ‘kara kawar da kanta gefe, d’an jiyo da face d’in sa yayi Side d’inta shima ta sake d’aukewa zuwa wani side d’in, “ Oaky fine ,” cewar Big Boss , lokaci d’aya ya soma yi mata cakul kulu, dariya Abla ta kyalkyale dashi tana ri’ke hannun nasa “ No please na bari fa , please ka bari “ kanshi ya girgiza mata “ No “, yanxu ma cikin dariya Abla ta furta “ Am sorry please ka dena mun cakulkulu “, tsayawa yayi da yi matan kafun ya furta “ then mene ne kike ‘bata rai uhmm ?” Shagwa’be fuska Abla tayi kafin ta furta “ Bakai bane ina gaishe ka amma ka’ki kulani” waro eyes d’insa yayi kad’an da ita kanta Abla sai da ta kawar da kanta ‘kasa “ ba ni bane , may be some one ne , “ ‘bata fuska Abla tayi “ Allah kai ne na gaishe ka fa kuma ka…”, peck yayi mata a baki da yasa ta kasa ‘karasa maganar da zatayi , idanuwansa akan fuskar ta ya furta “ İrin wannan gaisuwar nake so okay ?”, zata sun kuyar da kanta ‘kasa ya d’ago mata dashi “ Okay?”, kanta Abla tayi masa knodding ba tare da tace komai ba , da hannu ta nuna masa warmers din da ta shigo dashi “ Zasu yi sanyi,” bata bashi damar cewa komai ba ta nufi warmers d’in a maimakon ta serving d’insa anan sai ta sakko dashi kan lallausan carfet d’in sa , da ido yayi mata tanbayar zaman ta a ‘kasa , itama sai ta langwa’bar masa da nata kan tana masa alama da ya sakko shima . Top süit d’in jikinsa ya cire kafin ya sako ‘kasan kusa da ita , warmers din Abla ta soma bud’e wa , ‘kamshin da yaji ne yasa ya kalli warmers d’in “ What do you like to eat ?” Cewar Abla “ What Sunsine want to eat” shima ya bata amsa yana kashe mata ido d’aya , d’an ‘karamun murmushi Abla ta saka kafun tayi serving d’insa ‘kosai da har yanzu zafi ne dashi sai kunun da ta saka shima cikin ‘karamin cup, zata saka masa sugar ya girgiza mata kai “ it’s okay, don’t put any sugar”, ba musu kuwa bata saka sugar din ba , tana ‘ko’karin zubawa itama ya hanata , “mai za kiyi?”kallan sa Abla tayi sannan ta kalli abincin “Nima zanci “, matso da ita yayi kusa da shi yana nuna mata kosan, d’aya Big Boss ya d’auka ya kai bakinta Abla ta bud’e baki zayi magana ya saka mata ‘koşan a baki “Don’t talk while eating, okay ?” Kanta Abla tayi masa knodding , da kanshi ya dinga bata ‘koşan a baki tare da kunun duk da tace baza tasha ba babu sugar haka Big Boss ya bata har Saida ta ‘koshi. “ Kai baka ci bafa?” Amsar da ta fito daga bakin sane yasa ta ‘bata rai “ Na ‘koshi”, bata ce masa komai ba ta saka wani ‘koşan a plate tare da matsowa kusa dashi sosai “ Allah Nidai sai kaci ,” ta d’auki d’aya ta saka masa Daidai saitin bakin “ Haaaa”,bud’e mata bakin Big Boss yayi, itama da kanta ta dunga basa a baki sai da ya kawar da kansa tukunna Abla ta tsaya “ kina so nayi d’an lukuti kamar ki ? Look at your belly yadda ya cika kamar kin saka abu a ciki” ya fad’a yana shafa cikin nata , itama kallan shafaffan cikin nata tayi tana ‘bata rai, “ bari na wanke hannu na “, tana niyar fita ya furta “ to my bathroom “, ba musu kuwa Abla ta wuce toilet d’in sa ta wanke hannun nata , tana fitowa taga an had’e komai waje d’aya kamar ba’ayi anfani dasu ba , shima yana ganin nata ya mi’ke tsaye tare da mi’ka mata top d’in süit d’in sa , kallan suit d’in tayi tana Tuna’nın abunda zatayi , fahimtar hakan yasa ta hau kan sofa ta tsaya Sabida ya fita tsawo “ Yar gajeriya “, shagwa’be fuska Abla tayi “ da kad’an ka fini tsaho ai kuma idan naci taliya nima zanyi tsahon”. “Really ? Waya ce miki zaki ‘kara ? Yar ficika “, cikin sauri Abla ta furta “ Ni ba yar ficika bace “, “ yar ficika “ Big Boss ya ‘kara furtawa yana kallanta , kanta ta langwa’bar masa , a shagwa’be Abla ta furta “ Sunshine….”, yadda ta ja sunan sai da tasa ya murmusa, hancin ta yaja kad’an “ Wannan Sunshine d’in ta naso na ‘ki fita yau , your shagwa’ba is killing me, huh “ hannu Abla ta saka zata rufe kuskarta ya ri’ke hannun “ Nifa bana san wannan kunyar, stop it please , ni kin mayar dani mara kunya shine ke kuma zaki zo kina ‘boye mun fuska ? Uhmmm tun wuri ki ajjeta a gefe dan bazamu shirya da ita ba,” ‘kasa Abla tayi da kanta tana wasa da fingers d’inta, tana tsaye akan sofa din ya matso da ita kusa dashi “ I always like it when you’re in this mood , this your shagwa’ba is killing me , I will go somewhere now ko zaki bini?” Shiru Abla tayi tana Tuna’nın amsar da zata bashi kafin ta saka hannayenta a wiyansa tana shafa doğan gashin kansa “ you have important things to do out side , kaga am not a Baby zan zauna a gida ko ?” Wani irin murmushi Big Boss yayi jin abinda tace “ you’re not a Baby ? Okay let’s see sai mu tabbatar”, ganin yana ‘ko’karin ka mota Abla ta zille tana dariya “ am not a Baby”, hannu ya saka zai ka mata Abla ta ‘kara zille wa tana masa gwalo “ Am not a Baby “, da ya saka hannu zai kamata Abla zata zille, sai ta soma gudu a cikin d’akin tana san gudu, taku biyu yayi ya kamota sai faman zare ido take “ Na yarda am a Baby”, cewar Abla ganin ya kamata , hannu d’aya Big Boss ya saka ya d’alle mata goshin sa , cikin sauri ta dafe Wajan tana kulle idanuwanta kamar me kuka “, Heyyyy Sunshine zatayi kuka “, bata sauke idanuwan taba ta furta “ Ni ba kuka nake ba “, kallan yadda ta kulle fuska Big Boss yayi kafun ya furta “ cockroach “ da sauri Abla ta bud’e idanuwan , ko tsaya wa duba inda cockroach din batayi ba ta soma tsalle “ Wayyo Allah na kyankaso kyankaso “ ganin ta ‘ko’karin rud’ewa ne ya furt “ am joking “ hannu Abla ta saka ta d’an doki ‘kirjin kad’an “ Ka bani tsoro Allah “, “ Scary doll “ cewar Big Boss yana kissing forehead dinta , top din rigarsa Abla ta d’auka ta ‘kara hawa kan sofa , da kanta ta saka masa rigar tare da d’aga masa fingers guda uku “ bakayi kyau ba “, okay fine bari na cire “ yana ‘ko’karin juyawa Abla tayi saurin ri’ke masa hannu “ Allah wasa nake maka kayi kyau , Bye ! Bye “ kumatun sa ya nuna mata alamar tayi pecking d’insa , zata girgixa masa kai ya yi mata wani irin kallo da saida tsikar jikinta ta tashi, “ ka kulle idanuwan ka “ da hannunsa ya nuna kansa alamar “ Ni ?” Itama Abla ta jinjina masa kai , bai ce mata komai ba ya kulle idanuwan, sai data tabbatar ya kulle idanuwan ta zo daidai kuma tun nasa amma tun kafun tayi pecking din sa , Big Boss ya bata kyautar nashi kiss d’in a baki “Abla zata kulle idanuwa ya furta “ karma ki soma , let’s go “, ya kama hannun ta suka fito daga cikin d’akin, har yanzu hannun sa na ri’ke cikin nata bai saki ba, A haka suka fito cikin falourn. Sai da yaje tsakiyar falourn sannan ya tsaya, hannunta da yake cikin nasa yake murzawa a hankali “ Sunshine take care “ hannunta Abla ta d’aga masa tana waving kafun tayi hugging d’in sa “ Take care Sunshine “, shima Hugging d’inta yayi back “ I will , and don’t stress your self , duk Wanda ya dame ki just give me a called , okay ?” Murmushi Abla tayi tana jinjina masa “ Okay “. A haka Big Boss ya bar part d’in Abla tanayi masa waving hannu dan ko bakin ‘kofar ya hanata zuwa .