← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 100

Sashe 2

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Big Boss na shigowa suma suka mi’ke gabaki d’ayan su , ko wannan su fuskokin su ya nuna tsananin shock da mamakin wanda basu ta’ba tsan mani ko gani ba , duk cikin su babu wanda Big Boss ya kalla sai uncle da ya nufo sa shima jikinsa duk yayi sanyi.”Little ?” Cewar Big Boss yana binsa da kallo ta ‘kasan ido duk da p_cap d’in da ya kare masa idanuwa . ‘Daya daga cikin mutanan d’azu ne yayi ‘karfin halin furta “ Follow me “, kallan Big Boss uncle yayi kafin ya furta “ lets go , zasu nuna maka inda Little yake “, kansa kawai Big Boss yayi knodding , mutanan suna gaba uncle da Big Boss suna baya , sai Victor da anthony da suka bigo su baya , ganin elevator d’in bazai isa har ragowar sojijin Big Boss ba d’aya daga cikin su ya furta “ Floor 3” da haka ya nuna musu wani steps da hannunsa . A elevator ma floor 3 ya danna , cikin mintuna da be wuce Biyu ba  suka shiga wani Babban falourn da ya fi na d’azu had’uwa da ‘kayatuwa , Babu kowa acikin falourn sai Bobo da wasu manyan mutane suma maza guda biyu , shigowar Big Boss ne ya saka gabaki d’aya suka mi’ke tsaye suma suna binsa da kallo cikin da tsantsan mamakin da ya kasa ‘boyuwa akan fuskokinsu . Kallan Bobo da yayi folding hannun sa yayi , kamar wanda aka sa dole ya furta “Suna ina ?” Yasan wa yake nufi shiyasa Bobo ya nuna masa wani door dake facing d’insa, kanshi tsaye Big Boss ya nufi  cikin d’akin. A kwance ya tarar da little cikin ‘kayataccen kan gado na alfarma, ga prince dake zaune kusa dashi yana bin fuskar sa da kallo, yana ganin shigowar Big Boss ‘kirjinsa ya buga da ‘karfi, cikin sauri ya matsawa Big Boss hanya yana sunkuyar da kansa ‘kasa . Shima Big Boss d’in ko kallansa be yi ba , duk da ciwan dake jikinsa haka ya sa’bo Little ya fito dashi prince kuma na biye dashi. Kallan yadda ya had’e face d’insa Bobo yayi shima yana kawar da kansa gefe gabaki d’aya an rasa wanda zai iya masa magana a cikin mutanan wajan, ganin yadda uncle ya tsaya yana binsa da kallo yasa Big Boss ya ‘kara tsuke face d’insa yana kawar da kanshi gefe. Motsin da Little yayi ne yasa ya d’ago da kansa a hankali Little ya furta “ Yaya !” Shiru Big Boss yayi masa sai sauke shi da yayi yana nufar hanyar barin falourn , Little da prince ma cikin sauri suka biyo shi har little yana ri’ke masa hannu, tun kafun Bobo ya matsa a inda yake aka bud’e Elevator d’in da zasu shiga , Sauban ne ri’ke da hannun mutumin d’azu sai wasu maza guda uku da kana ganin su suma zaka ga kwanciyar hankali a tattare dasu, cikin tsananin ‘bacin rai Big Boss ya taune lips d’insa yana ‘ko’karin kauce hanyar mutumin ya ri’ke hannun sa , rai a ‘bace Big Boss ya fusge hannun sa , har saida sauban ya ri’ke mutumin ganin yana ‘ko’karin fad’uwa cikin sanyin murya mutumin ya furta.” Na ro’ke ba danni ba , ka ha’kura da tafiyar nan kafun gari ya waye ,” just this night kabeer , nasan kai zaka iya masa , Dan Allah “ shiru uncle yayi shima yana kallan mutumin da bazai ta’ba mantawa dashi a rayuwar saba , koda ace yana cikin magagin bacci aka anbaci sunan Dr Mohammed Taufeeq Mai Dala zai shaida ko wanene,sunkuyar da kansa da yayi ne ya saka mutumin sakin murmushi da yafi kuka ciwo ,” kai ma bazaka iya bako?”, yanzu ma lips dinsa Big Boss ya taune kafun ya jiyo cikin ‘bacin rai yana kallan su prince , ganin reaction dinsa sukayi saurin matsowa kusa dashi suna mamakin mutumin da yake pleading Big Boss . “Bamu cancanci yafiyar kaba , amma Dan Allah, dan Annabi  for his condition ko kwana ne ka bari suyi…” be kai ga rasa maganar saba Big Boss ya sha’ko wuyansa , a firgice Bobo ya karaso wajan ganin yanayin Big Boss “ Bana bu’katar sanin abunda zanyi da wanda zan bari, who the hell do you think you are “, idanuwansa gabaki d’aya sunyi ja hatta p_cap din jikinsa sai da ta fad’i, ga ciwan sa da akai masa bandage d’insa ya soma jini sabida yadda ya buge ciwan, har yanzu hannun sa na sha’ke da wuyan Suban da ya kasa koda kwakkwaran motsine , cikin taushin murya Bobo da uncle suke furta “ calm down! Big Boss please calm down ka kwantar da hankalin ka , yanzun nan zamu tafi ! Just cool down please “, hankad’asa Big Boss yayi lokacin da sauban ya soma Ware idanuwansa , dan ba ‘karamun sha’ka Big Boss yayi masa ba , cikin sauri Bobo ya mi’ke ganin yadda Big Boss yake ‘ko’karin ficewa daga hayyacinsa , gefe guda kuwa little da prince da suka  tayar da hankalinsu, shima mutumin d’azu neman silalewa yayi ‘kasa aka zaunar dashi har yanzu hannunsa ri’ke da saitin zuciyar sa. Cikin sauri Bobo ya zura hannunsa cikin aljihun Big Boss , wata allura ya d’auko cikin sauri ya had’ata tare da tsirawa Big Boss a hannunsa , d’ago da idanuwansa Big Boss yayi yana bun Bobo da wani irin mugun kallo, cikin mintunan da bazu wuce 1  ba Big Boss ya saki hannunsa akan wuyan Sauban da ya soma shure shuren mutuwa sabida irin sha’kar da Big Boss yayi masa. Ganin yadda yake lumshe eyes dinsa Bobo yayi saurin ri’ko masa hannu tare da zaunar dashi kan d’aya daga cikin kujerun wajan .

     Lumshe eyes d’insa Big Boss ya ‘karayi , cikin sauri Bobo ya d’auko wasu ruwa da yagani , murfinsu kawai ya bud’e ya soma tuttulawa  Big Boss a kansa gabaki d’aya.  har lokacin Big Boss yana zaune kan kujeran kanshi a sunkuye,Little kamar zaiyi kuka ya matso inda Big boss yake , akan gwiwowinsa yayi kneeling shima prince cikin sauri ya matso kusa da Little yayi kneeling “ We’re very sorry yaya, ba munyi haka dan mu ‘bata maka rai ba, we just missed our Lil, please karkayi fushi damu yaya”, cewar Prince da ya sunkuyar da kansa , a tsorace little ya ri’ke hannun Big Boss yana murzawa a hankali “ I’m sorry yaya , lefi nane babu yaya Prince a ciki , just punish me alone amma babu lefin yaya prince kaji dan Allah”, yanzu ma shiru Big Boss yayi musu har yanzu kansa a sunkuye yake,kallan su kawai mutanan falourn suke , gabaki d’ayan su anrasa Wanda zai iya bud’e bakin sa yayi magana hatta Dr Mohammed dake dafe da saitin zuciyarsa kasa magana yayi ga wasu irin kwalla da suka tarar masa cikin ido gabaki d’aya ya kasa kallan su Bobo musamman yanzu zantukan su Little da ya ‘kara karya Musa zuciya . Kusan tsawan mintuna 5 suna du’ke a Wajan Big Boss ya tashi, Little xai sake magana Big boss yayi masa wani irin mugun kallo, babu Wanda ya sake kalla a cikin mutanan falourn ya nufi elevator , ragowar sojojin ma gabaki d’aya sai suka mara masa baya , kansa Bobo ya dafe Sabida yadda yaji kansa na mugun sara masa baya ‘Kaunar irin shurin Big Boss haka , ga allurar da yayi amsa sai tayi 10 hours a jikinsa tukunna zata sake shi . “ Yaya bobo we’re sorry please “, ya fad’a yana ri’kewa Bobo hannu, shima Bobon zame hannunsa yayi yabi bayan Big Boss cikin sauri. 
     da Sauri Little ya karasa wajan uncle. “ uncle fushi suke dani duka harda yaya bobo , I promise bazan sake ba, please ka basu ha’kuri “,ganin yadda yake shirin yin kuka ne uncle yayi hugging d’insa “ it’s okay ! Ransune a ‘bace but you have me , zamu basa ha’kuri, just karka tayar da hankalin ka , okay”, kansa little ya jinjina masa, ko kusa babu Wanda ya mayar da kallansa kan su sauban shida little, hannun su uncle yaja zuwa d’akin da aka kwantar da little d’azu suna wucewa Sauban yayi saurin ‘karasowa wajan mutumin da ya kira da Abbu “ Abbu please nace kakwantar da hankali, na tabbata zuwa safiya Nani idan taji labarin zuwan su ko me zatayi sai tayi sabida ta Hanasu komawa and kuma na riga na turawa SITTI da DIIDII  sa’ko any moment from now nasan suna cikin jirgi.”
      “ thanks dear , yaka mata kowa ya shirya kafin a tafi masallaci,”.okay kawai sauban yace masa , lokacin da wasu daga cikin mazan da suka zodashi suka temaka masa zuwa  d’akin sa , Dan building d’insa ya sa akai su little d’azu . 

  “ who’s that man ? And Menene relationship d’insa da su yaya “ da sauri uncle ya nuna musu time “ ku ajje komai a gefe time na tafiya banasan wani tanbayar please “, cikin ‘kan’kanin lokaci  suka  shirya cikin wasu ‘kananan kaya , Allah ya temake su gabaki d’aya antaho musu da trolley d’insu shiyasa basu sha wani wahala ba . Da za’a je masallaci ma gabaki d’aya duk yadda Dr Mohammed yaso ko magana ne ya shiga tsakaninsu dasu little hakan be samu ba , musamman little da ya ri’ke hannun uncle babu Wanda ya kula a cikinsu, gwanda prince da gaisuwa ta had’asu daga nan babu abunda ya shiga tsakaninsu ,burin su kawai suga Yaya Big Boss d’insu da Yaya Boss.
Chapter 2 · 0% Book details