← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 100

Sashe 65

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***** Bobo yana fitowa gabaki d’aya sukayo kansa musamman Prince da ya ri’ke hannunsa “ Yaya ! Little d’ina fa ? Yana lapiya ? Zan iya zuwa inganshi? Yaya fa ?”, d’an Kallansa Bobo yayi ganin yadda hankalinsa yake a tashe kuma Indai ba ganin Little din yayi ba hankalinsa bazai ta’ba kwanciya ba , “ It’s okay Little na tare da Yaya, allowed him to rest, go be zaka ganshi”. Prince zai yi magana Bobo ya girgiza masa kai “ No more complain okay?” Shiru Prince yayi yana knodding kansa , kashin kansa Bobo ya shafa “ it’s sleep kafun ka fara yiwa Little complain kai kad’ai ka kwana “, babu wanda yayi wa magana ya juya zasu bar wajan , “ Abdul “ cewar His Excellency, dakatawa Bobo yayi daga tafiyar da ya soma kafun ya d’an jiyo kad’an “He’s fine. Zuwa safiya zai dawo normal”, iya abunda Bobo yayi ce musu kenan ya bar wajan shida prince . Bin bayansu da kallo His Excellency yayi kafun ya kalli hanyar d’akin da su Big Boss suke ciki “ ka kwantar da hankalinka , duk lokacin da ciwan sa ya tashi babu Wanda yake san fara gani kamar sa , insha Allah komai zai zo da sau’ki Kai ma ba isash shiyar lapiya ce da kai ba , ga Mama itama da Didi, Na muku al’kawari komai zai zo da sau’ki insha Allah “, kanta His Excellency ya girgiza yana sakin murmushi me ciwo “ Kabeer ka manta ni na haifi Farooq ? Halinsa şak irin na mai sunan sane , na tabbata Adil na farkawa bazai ‘kara zama a cikin gidan nan ba balantana ya saurari kowa “, 
  “ a wannan karan na maka al’kawari komai zai zo da sau’ki insha Allah babu abunda zai faru sai alkairi, Dare yana ‘karayi ya kamata ku huta gabaki d’ayan ku, Dan Allah Didi , Mama ku kwantar da hankalin ku “, kansa Dadyn su Eshaal ya jinjina “ Abunda kabeer ya fad’a gaskiya ne ko ba komai suna bu’katar lokaci tunda su akai wa lefi, Ina ganin mu bar komai zuwa goben “, da haka suka bar part d’in duk da Mama da Didi Sunso zama a part d’in amma sabida yanayin jikinsu suka ha’kura da magiyar da su Mamy suke mata ita da Aunty Nusaiba. A haka gabaki d’aya kowa ya koma part d’inşa jiki a sanyaye . 
     A cikin Daren nan babu wanda ya runtsa sosai kowa da tunanin abunda zai faru gobe yake . Banda Abla da gabaki d’aya bata san abunda yake faruwa ba a cikin gidan . 

WASHE GARI

  Kiran sallar asuba da akaine ya farkar da Abla daga baccin da take, da ‘kar ta iya bud’e idanuwanta sabida yadda bacin ya soma yi mata dad’i bakinta d’auke da adduar tashi daga bacci ta ware idanuwanta “ Baya nan “ shine abunda zuciyarta ta soma ayyana mata , d’ayan side d’in ta kalla nan ma still baya nan , yar ‘karamar ajiyar zuciya ta sauke kad’an “ May be ya tafi sallah “ zuciyarta ta sake ayyana mata . Batayi tunanin komai ba ta nufi dressing room d’inta, sai da ta gasa jikinta sosai sannan tayi wanka da almara gudun kada lokacin sallar ya wuce ta . Tana idar da sallah sai da ta zauna tayi azkar d’in ta da karatun alkur’ani, lokacin gari har ya d’an soma wayewa. Wani iri Abla ta soma ji cikin zuciyar ta haka kawai itama bata san dalilin hakan ba kuma . Bata zauna sai data gyara d’akinta , tana gamawa da nata ta koma nasa , mamaki ne ya kamata sosai ganin alamar kamar babu wanda ya shigo d’akin , hatta kan gadon agyare yake alamar babu wanda ya Hau kansa . 

     ‘Dan gyarawa tayi kad’an tayi mopping bayan ta wanke masa toilet d’insa , bata bar d’akin ba sai data bar burner da take faman turara d’akin da daddad’an turare mai sanyaya zuciya , ga Ac da ta bari a kunne shima sai ‘kamshi da sanyin Ac ya had’e waje d’aya .

       “ Welcome back Ma’am “ cewar Jenny data ga Abla, itama Abla murmushi ta sakar mata “ Jenny ya kike ?” Sosai Jenny ta ‘karayin wani murmushi “ am good Ma sai kewar ki da nake “, har yanzu fuskar Abla da murmushi akanta ta furta “ Ai gani ynxu na dawo kinga kin huta da Missing d’ina “. Yes Mah”, cewar Jenny sai kuma ta ‘kara da “ Mah akwai aikin da zan taya ki dashi ne?, Mai za’a safa na breakfast?” Kanta Abla ta girgiza mata “ No karki damu yau ba wani aiki zamuyi ba , simple Breakfast ne kuma bashi da wahala nasan akwai aikin da kike yanzu , don’t mind me kawai kije kiyi aikin ki ni zanyi breakfast d’in”, Jenny zatayi magana Abla ta rigata “ babu wani magana kuma , karki damu , ni bari naje nayi abincin okay”, ta ‘karasa tana barin wajan zuwa hanyar kitchen . Tana barin wajan Jenny ta saki murmushi “ She’s the best kindest women ever , I so much like her “, zata bar wajan taji sallama kamar ana shigowa , cikin sauri ta jiyo ganin Uncle a tsaye cike da girmamawa ta furta “ welcome sir “, kansa Uncle ya Jinjina mata “ welcome Jenny, ina madam d’inki ?” Kai tsaye Jenny ta furta “ She went to the kitchen now “,   “ jeki kira mun ita “ uncle ya bata amsa lokacin da yake zama kan d’aya daga cikin kujerun, ko cikkaken mintuna biyu bata yi suka fito ita da Abla , ita kanta Abla ganin uncle a part d’in sai da Tasha Jinin jikinta “ kinyi mamakin gani na ko ?” Cewar Uncle , da Sauri Abla ta girgiza masa kai tana tsugunnawa har ‘kasa “ Uncle ina kwana “, da hannu Uncle yayi mata nuni da d’aya daga cikin kujerun, ba musu kuwa ta zauna dan tsugunnawar da tayi sai da ta d’anji zafi dan har lokacin ciwan ta ba warkewa yayi ba . “ how are you ?” Cewar Uncle , yanxu ma amsa masa Abla tayi cike da girmamawa zuciyar ta haka kawai take tsinkewa duk da batasan abunda zai fad’a mata ba , shima Uncle shiru yayi kamar bazai yi magana ba sai kuma ya furta “ Your Little is not feeling fine “, cikin Sauri Abla ta d’ago da fuskarta “ Yaya Little bashi da lapiya ? Yaushe ? Yana Ina ? Ya jikin sa yanzu ? Mai ya samesa ?” Shine abunda bakin Abla yake ambata , d’an shiru uncle yayi mata “ karki damu zuwa yanzu nasan lapiyar sa ‘kalau akan hakan ne yasa na zo wajan ki,” Uncle bai ‘boye mata komai ba ya labarta mata abunda ya faru gabaki d’aya “ Shiyasa bangan saba Kenan ?” Ta ayyana wannan tanbayar a ranta cikin sauri kuma ta kawar da zancen, haka kawai lokaci d’aya wani irin tsanar Nani Yashiga ranta , maganar Uncle ne ya dawo da ita hayyacinta “ Nasan kina da tanbayoyi da yawa da kike san sani duk da nasan babu Wanda ya ta’ba fad’a miki, kamar yadda ta fad’a hakan ne , His Excellency mahaifin sune “ cikin sauri Abla ta d’ago da kanta , shima kansa Uncle ya Jinjina mata “  Tunda naganki arai na naji tabbas ke d’in alkairi ce a rayuwar su musamman yadda suke tsananin sanki gabaki d’aya , kowa da kalar tasa ‘kaddarar a rayuwa da bazamu iya tsallake mata ba , suma hakan ce take a tasu rayuwar, nasan a sannu zaki samu labarin komai kuma zaki fahimci komai idan Kika kula kuma kikai taka tsantsan da kowa na cikin gidan nan , ciki kuwa har ni karki cire , bani da isash shen lokacin da zanyi miki bayani amma nasan kina da kwakwalwa kuma kina da fahimta , ro’kona d’aya a gareki, tunda ran mijin ki ya ‘baci nasan komai zai iya faruwa yau d’in, barin sa cikin gidan nan kamar ya bawa ma’kiyansa hanyar samun nasarar sune , amma idan har yana cikin gidan nan nasan yaro na zaki ne me tarwatsa ko wana irin d’an iska , ko ba danni ba kiyi wa mahaifinsa wannan abun gabaki d’aya zamuyi alfahari da kasancewar ku anan na ro’ke ki “. Abla mamaki ne ya kamata sosai gabaki d’aya ta rasa bakin magana babu abunda ya fi Dakar zuciyarta kamar yadda Uncle yake san tayi masa abu , wacece ita da zata ‘ki yi masa abunda yake so ? Mutanan da suka mayar da rayuwar ta kamar wata tauraruwa a lokacin da mutane da yawa suke ‘ko’karin hallaka rayuwarta ? Mutanan da take ji a duniya bata da kamar su ? Wani irin ‘karfin gwiwa ne taji yana shigarta da ita kanta bata san ta ina ba , abu d’aya ne kawai yake mata yawo a cikin zuciya , “ zata dawo musu da farin cikin su kamar yadda suka saka ta a ciki”, a firgigit ta dawo Tuna’nın ta dubawar da zatayi taga Uncle har ya tafi. ‘Karamar ajiyar zuciya Abla ta saki gabaki d’aya ta fad’a Tuna’nın ina mafita take , so take taga shigowar sa shiyasa tayi saurin kashe gas d’in data kunna ta dawo falour ta zauna.

       ‘Karfe 7:45am na safe Big Boss ya shigo part d’in , bayan da ya saka jiya bane a jikin sa ga fuskar sa da take a d’aure ta tamau ita kanta da ta ga yanayinsa sai da ta shiga taitayinta, sosai gashin kansa ya zu’bo masa a baya sunsha gyara kamar basu ba sai shinning d’in da Suka sosai na mai . Bai ce mata uffan ba ko ya nuna alamar akwai mutum a falourn ya wuce Bedroom d’insa . 
Chapter 65 · 0% Book details