← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 100

Sashe 11

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Wani tsaki wacce aka kira da sürey ta ‘karayı a ‘kufule cikin ‘kyan’kyami take bun yan aikin da wani mugun kallan tsana “ Hearty  bazaki gane yadda na tsani talaka a rayuwa ta ba , duk banzaye ne mara sa aikin yi gida dawa dan ni ko a mutane bana d’aukarsu , “ yanzu kam dariya yagowar yan matan suka saki cikin ‘kara fankamata suke furta “ Up up surry” wacce batayi magana a cikin ba ce tun d’azu ta d’an ya mutsa fuska “ Ni dama tun wannan shashanci a gefe kuka ajje sa , kun ga kuwa samarin da sukazo? Kun ga yadda hutu da kwanciyar hankalin da tsantsan kudi yake fitowa daga jikinsu ?” Hearty ce ta d’an sauke nunfashi “ Reada ni zan fad’a miki wannnan maganar , ban ta’baji san wani saurayi ya kamani lokaci d’aya ba kamar wannan guy d’in , da alama shine Babba a cikin su , yadda tsarin shigar sa take da ban ma abun kwatance ne , ga wasu shegen kaya da ya saka masu tsad’an gaske , gabaki d’aya na kasa fasalta kyaun su, hatta samarin Biyun da nagani kamar sune ‘kananan sai mai biya babban , wayyo Allah , gaskiya bazan ta’ba ha’kura ban samu d’aya daga cikin su ba , ko ana ha maza ana ha mata sai na auri d’aya daga cikin su “. Itama surry murmushi tayi kafun ta d’an tsuke face “ Amma nifa farar yarinyar da nagani gabaki d’aya bata burgeni ba musamman da naga yadda suke mata magana , ki duba kiga har ri’ke mata hannun babban cikin su yayi “. Dakatar da ita hearty tayi “ ba dole kiga suna bata kulawana ba , ‘kanwar suce fa baki ga yadda kyaun ta ya fito ba sosai ? Ko dai kina kishi ta fiki kyau ?” Amaimakon surry ta amsa mata sai harara da ta sakar mata , phone d’inta kawai ya d’auka ta bar wajan cikin sauri mai aikin da suka zo tare tabi bayanta kamar zata tsugun nata . Tsaki Reada tayi tana bun bayan Surry da harara “ banza ita gani take komai ta iya , mtsww “ daga haka suka ci gaba da gulmar Abla da Big Boss . 

***** 6:5pm prince yashigo part d’in tun d’azu da ya shigo yake jiran ganin Abla amma babu ita babu alamar ta hatta bedroom d’inta sai da ya duba bata ciki , kamar zai bar falourn sai kuma wani tunani ya ‘kara fad’o masa , d’akunan falourn ‘kasa ya soma duddubawa ko tana ciki gabaki d’aya sai ya tarar da bakowa a cikin su, har zai juya ya hango d’an hasken da ya ‘bullo a kitchen shiyasa ya nufi wajan direct , yana shiga ya tarar da Abla akwance da sauri ya ‘karasa yana kiran sunanta “ Hey! Hey ! Sister tashi mana , me ya sameki haka ? Ki tashi please “ ganin bata motsine yayi saurin d’aukan ruwa a fridge duk da sanyin da yayi haka ya fesa masa , wata irin doguwar ajiyar zuciya Abla ta saki lokacin da ta bud’e idanuwanta . Cike da tsantsan mamaki take kallan kanta ganin yadda ta kwanta , shima prince da mamaki a face d’insa ya furta “ me ya sameki lil ? Na ganki a kwance?” Kanta Abla ga dafe sosai sabida wani irin mugun sara mata da yake kamar zai cire , a hankali ta furta “ Nima bansani ba yaya prince , tun da na shigo zan muku fruit ban ‘kara sanin komai da ya faru ba “, kallan yadda take ri’ke kai yayi sosai “ me ya samu kanki haka ?” Yanzu kam d’an ya mutsa face tayi tana ‘ko’karin tashi saura kad’an ta zube a kasa “Be care ful , sister ko baki da lapiya ne ?” Kanta ta girgiza masa “ No lapiya ta ‘kalau nasan inayin sallah zan dawo daidai , Please karka fad’awa Lil kaji ?” Bazan fad’a masa ba amma kema with one condition zaki sha magani , kin yadda ?” Da kai Abla ta amsa masa dan ko magana bata sanyi, har wajan d’akin ta ya karata , bai tafi ba sai da yaga shigewarta. 

    Abla kamar ta d’ora hannu aka haka take jin kanta , gabaki d’aya batajin dad’in jikinta kwata kwata , yadda take tafiya kamar me lahi da ‘kyar ta iya watsa ruwa tayo alwala . A wajan sallama haka tana sallah kafafuwanta suna hard’e mata sabida mugun jirin da take ji. Tana idar da sallah tayi kwanciyarta akan daddumar hawayen da bata san ko na menene ba suna sakko mata a kumatu , a ‘ban gare d’aya kuma hannunta na ri’ke da ‘kafar gabaki  d’aya ji take duniyar ta tsaya mata , bakin ta yayi mata nauyin da ko addua ta kasa . Ana kiran sallah isha’i da ‘kyar tayi yin ta , tazo zatayi shafa’i da wuturi jiri ya fad’ar da ita dole sai ha’kura tayi.
Chapter 11 · 0% Book details