Sashe 16
Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
********Hankali a tashe Harry ta wuce part d’in su gabaki d’aya ta kasa zama sai faman cizan yatsa take , takaici duk ya bi ya isheta, “ Ahhhhhh” ta saka wani irin ihu da sai da me aikin su ta fito , tana ganin Harry jikinta ya soma rawa , “ Dan ubanki me kika fito yi nan ? salan munafurci ko kuma me ? Akwai uban da ya kiraki ne ? Shegiya me kama da mayu dallah ‘bace mun da gani kafun inci ubanki anan wajan, shegiya dan gin matsiyata “ ha’kuri mai aikin ta fara bata da ashekaru zata iya haifarta ko kuma tayi ‘kanwar baya baya da ita. Wani Wawan tsaki taku ma tare da zare d’an kwalin kanta dogon gashin attachment d’inta ya Fito waje , tsabar haushi da ta kaici bata san lokacin da ta soma jefar da fulan lukan falourn ba sai faman jifa take dasu ita kad’ai sai jan tsaki take , takaici duk ya bi ya isheta . Shigowar Hajiya falmata ne yasa tayi saurin mi’kewa tare da nufo ta “ Gaskiya Momy da sake , Dan wallahi bazata sa’buba dole dole kisan yadda zakiyi , shiyasa tun wuri nace miki ki aika wajan Bo….” Bata ‘karasa ba Hajiya falmata tayi saurin rufe mata baki tare da janta zuwa cikin d’akin ta “ Harry baki da hankali ne ? Tonan silili kike ‘ko’karin yi mana ko me ? Ba kya Tuna’nın shigowar su surayya?” Tsaki Harry taja , “ Toh sai me idan sunji , matsalar suce duka ba tawa ba , ni matsala ta a yanzu ki aika wajan bokan ki na kan dutse da kika ce zaki aika, sai faman magana nake miki kina cewa a bari ba yanxu ba , ki duba a ce shegiyar yarinyar can da zan bawa shekaru shida zuwa bakwai kiga irin wayar da ke hannun ta da ko ni bani da iriin ta , ki duba hannun ta zallar diamond ne a jiki, shegiya ga kyau kamar farar aljana dan nasan da gangan tayi wannan shigar ,Momy ki duba rigar jikin da tun da nake ban ta’ba cin karo da ita gaskiya bazai yuwa , kamata yayi ace duka wannan abun nice nake samu , nice zan samu kayan more rayuwar nan haka , gaskiya hakan ba zai yuwa ba momy , ki duba kiga yayyunta da suka shigo ko kallo bamu ishesu ba amma sai faman tarairayarta suke , ita kuma shegiyar tana narkewa kamar ta taccen albasa ,” ta ‘karasa tana hura hancin ta , itama Hajiya falmata wani irin ‘kwafar takaici tayi “ bake kad’ai ba ni kaina raina yayi mugun ‘baci , dole nasan abun yi , ba gobe ba , yau yau d’innan zan sa aje Wajan na kan dutse dan bazata ta’ba sa’buwa ba , shegen yayansu da suka fi kowa shegen ji da miskilanci ko kallo bamu ishesu ba balantana su iya zuwa su gaishemu. Ita kuma shegiyar yarinyar can banni da ita , duk abunda take ta’kama dashi sai na rabata dashi tun kafin Hajiyar America da wannan banzar Ammaran su dawo daga ingila, dan nasan suka dawo komai namu tsayawa zaiyi dan akan idanuwan mu Hajiyar America zasu dunga nuna wa yarinyar nan ‘kauna musamman tasan da zuwan yarancan duk kallan yan iska zata mata “. Kafad’u Harry ta d’aga “ Momy ni duk wannan ba matsalata bace , duk yadda zakiyi kawai kiyi , so nake yayansu ya haukace a sona ya zama duk abunda nace yayi shi zai yi , inaso gabaki d’aya ya zama ‘kar’kashin kulawa ta, dan wallahi Momy ko zanyi yawo tsirara sai na cika burina na auren d’aya daga cikin su , gwanda ma duk hanyar da zaki bi, kibi dan babu abunda ya dameni da ko mai zai faru Indai burina zai cika .” Ta ‘karasa zancanta tana barin d’akin. Hajiya falmata tun bayan futar Harry da tagani sai itama ta fara zagaye cikin d’akin dan sosai Diamond d’in Abla ya tsaya mata cikin zuciya , lokaci d’aya taji wani irin mamarin samun dukiyar na ‘kara shiga kanta , ita kad’ai sai faman tunanin hanyar da zatabi ta cimma burinta take .
*****************
A cikin wani falo kuwa wasu manyan mutane ne da Hutu da kwanciyar hankali ya gama ratsa ko waccen su, sai ‘yan mata guda uku da ko wacce taci Jeans a cikin su , d’aya daga cikin hajiyoyin me suna Hajiya sa’adatu ce ta kalli d’ayar “ Ni kam Hajiya karima kinga abunda nagani kuwa ?” Wacce aka kira da hajiya Karima ce ta saki wani makirin murmushi , cikin izza ta furta “ karkice mun diamond d’in da kika gani a hannun yarinyar can ne yake ‘ko’karin tayar miki da hankali ?”, da mamaki akan face d’in Hajiya sa’adatu ta furta “ kema kinsan dole abun nan ya bani mamaki da d’aure Kai , kina ganin diamond d’in hannun ta ba ‘karamun ma’kudan kud’i aka kashe masa ba wajan yin sa , ko ni da nake siyan gwala gwalai da ‘kyale‘Kaylen diamond d’ina ba banta’ba ganin me kyau wannan ba , na yadda gaskiya shegun yaran nan ba ‘karamun kud’i ne dasu ba, ki duba saura mazan yadda wani irin Hutu ya kwanta fatarsu gabaki d’aya babu alamar wahala a tattare da ita ,balantana me dogon gashin nan da baya kallan kowa da daraja dan tun ranar ‘karshe da Diidii ta hanasu tafiya ban ‘kara san ya su acikin idanuwana , hatta ‘kananan su sai jiya shima Sabida wannan shegiyar yarinyar “, wani murmushi Hajiya karima tayi tana kallan Hajiya sa’adatu “ Dad’i na dake kina da gazan ha’kuri, Menene abun jin haushi ko takaici a ciki ? Ki kalli Yasmeen , Amal , da Kubra da zaune yanzu , ba kamata yayi musamman hanyar da za mubi mu aura musu yaran nan ya kamata mu fara bi ba, ragowar komai me sau’ki ne sabida nasan tunda Falmata ta saka idanuwanta akan su Allah ne kad’ai yasan irin shirin da take shirin yi “ d’aya daga cikin su Mai suna Yasmeen ce ta furta “ Gaskiya ni Aunty babban cikin su nake so ko mai bi masa , sabida naji ‘Kishin ‘kishin Harry da su Surry duk harin sa suke “ Amal ce tayi saurin cewa “ Kin ma isa ? Yarinya da sake sai dai ki za’bi wani ba dai shiba danni har na fara hango irin rayuwar da zamuyi dashi, itama kuma wannan ‘kanwar tasu sai na Mayar da ita Mai aiki ta fita daraja ba “, a fusace Yasmeen ta kalleta zata Mayar mata da martani Hajiya Karima ta furta “ kull Yasmeen , bana san jin cece kucen ku yanzu , idan ba plan d’in mu kuke ‘ko’karin ruguzawa ba , yanzu nasan duk inda baban ku yake yana kan hanyar dawowa dan haka zan je in kimtsa “ mi’kewa Hajiya sa’adatu tayi tare da Yasmeen “ Shikenan sai munyi magana na barki lapiya “, tana kai ‘karshen maganar ta Suka bar part d’in ita da Yasmeen , a waje Yasmeen ta tsaya tana kallan mahaifiyar ta “ yanxu Mama kin bi bayan su Amal su fini samun me kud’i Kenan?” Wata iriyar dariya Hajiya sa’adatu ta saki “ Sha kurumin ki mana Yasmeen , ita Karima gani take ta fu kowa wayo , Ina sun kuyar da kaine sabida na gama sanin shirin ta , amma kema kin sanı bata İsa ‘ya’yan ta su fiki jin dad’in rayuwa ba .” Washe baki Yasmeen tayi “ shiyasa ai nake sanki wallahi , ya kamata mu wuce kar muna fukai su fara sa mana ido”, da haka suka nufi hanyar da zai sadasu da part d’insu.
Cikin falourn Hajiya karima kuwa , budurwar da tun d’azu bata saka musu baki bace ta furta “ yanzu Aunty sai ki bari wata daban ta samu arzi’ki ba mu ba ? Ki duba Amal , ki kalleni kinsan ba ba auren yara bane mu” wani murmushi Hajiya Karima ta saki “ ku kwantar da hankalin ku ,Kubra , Yasmeen , kada ku saka komai a cikin ranku, ku bar komai a hannu na da Sannu zanyi maganin su , Sa’adatu bata İsa samun abu ba sai na samu , sai dai in ta samu ragowa “ cikin sauri Kübra ta furta “ Amma Aunty yarinyar nan fa ? Kina kallan cikin idanuwanta zakiga bata shayin kowa sai kace rainan bariki” Hmm kawai Hajiya karima tace tare da barin falourn tana nufar d’akin ta .