← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 100

Sashe 87

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Karfe 11am na safe Abla ta farka daga baccin da take , ganin baya cikin  d’akin ne yasa ta shirya cikin wata fitted d’in atampa da yayi matu’kar yi mata kyau, man le’be ta saka a bakinsa sai faman shinning yake ga d’ankwalin da ta d’aura sai ta fita daban Sabida bata saba yi ba amma duk da hakan ba ‘karamun kyau kayan sukai mata ba , murmushi Abla tayi sabida suprised din da take san yi masa , turarukan ta ta faffesa a jiki sannan ta sakko zuwa hanyar da Big Boss ya biyo da ita , jiya , da ‘kyar ta iya gane hanyar har zuwa part d’insu . Bata zauna cikin falourn ba ta nufi kitchen , sai da ta had’a masa favorite coffee d’insa tukunna ta nufi hanyar d’akinsa  bakinta d’auke da sallama, kanta a ‘kasa har ta shigo falourn , d’aga kan da zatayi ne idanuwanta suka sauka akan Harry da take sanye cikin wata yar iska riga da alama ‘ko’karin cirewa take sanyi , cikin tsananin ‘bacin rai Abla tayi wurgi da coffee d’in hannunta , a Daidai lokacin da Big Boss ya fito daga dressing room d’inta . Idanuwan Abla a rufe ta ‘karasa inda Harry take , da hannayenta biyu ta d’aga ta tsitstsinka mata mari , bata tsaya a hakan ba ta sha’ke mata wuyanta, babu abunda jikin Harry yake sai rawa ga wani irin waro ido da tayi sabida mugun shakar da Abla tayi mata, gefe d’aya ga wani mugun kallo da Big Boss ya jefa mata da taji wani irin gudawa na ‘ko’karin ’kwace mata.

IBTISSAM
      ( A heart touching story of love and destiny)

Story & written 
      By
Mss Lee   

    TALLA!! TALLA!!! TALLAH !!!!!!!

SHIN KUNSAN WACECE HAJIYA NUSAIBA BR~B ZURU ?❤️

HAJIYA ~ NUSAIBA DR~B ZURU

MAMALAKIYAR ZIMH ISLAMIC AND MEDICINE DAKE RINGH ROAD A KANO NIGERIA
Tazo muku da ingantattu ko sahihan magungunan mata masu inganci, ba’anan kad’ai ta tsaya ba har da na cututtuka da Turarukan wuta , Humra masu shegen ‘kaushi . Abun Alfaharin kuma tana bada sarı cikin sau’ki, sannan kuma suna aikawa duk inda mutum yake afad’in duniyar nan. 

Duk wacce ta siya magungunan Hajiya Nusaiba Dr B zuru, taga be yi mata aiki ba tazo za’a dawo miki da kudin ki . 

KA’DAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKE SIYAR WA

1️⃣ Hadin amarya
2️⃣Hadin mai jego
3️⃣Hadin sabon budurchi
4️⃣Hadin Kaza Yar’Suddan
5️⃣zuma -Tsumi- Tabaje da sauransu
6️⃣Turaren Sandal ruuu& flastic Sandal
7️⃣ Hadin Hawwi domin inganta zafafiyar kauna
8️⃣Hadin bagadad,kahlij,kajiji,gafgaf dasauransu
9️⃣Hadin humra soyaya dole ta matan aure da normal humra

DON SAMUN ‘kARIN BAYANI KU NE META TA WANNAN NUMBER KAMAR HAKA : 
    08133647913 

   KANO NIGERIA 

LOCATION: RING ROAD BAYAN GİDAN MAN NAZARGO.

       SIYAN NAGARI MAIDA KU’DI GIDA

PAID BOOK

2 PAGES NA HA’DE KAMAR YADDA NAYI AL’KAWARI , PAGE ‘DIN JIYA DA NA YAU .

BOOK 2 
         S_____ 28

Tunda Abla ta sha’keta take ka’kari kamar wacce ranta zai fita, ran Abla sosai ya ‘baci babu abunda takewa Harry sai maruka da take tsits tsinka mata, Big Boss na tsaye ko uffan bai ce musu ba, gashi kuma babu alamun zai yi maganar, wani Wawan mari da Abla tayi wa Harry sai da tayi ha’bo, jini ya soma fita ga hancin ta, Abla kuma bata da alamar sakin nata, a hankali ya soma nufo inda suke, da hannu d’aya ya saka ya ri’ke nata tare da dawo da ita kusa dashi, Harry na ganin hakan ko Hijab d’in da ta shigo dashi bata d’auka a guje ta zo fita yadda Abla ta zabura zata dam’kota sai da Big Boss ya tallafo ta cikin Sauri.
     Harry kuwa cikin tsananin tashin hankali da rud’u ta fito a guje daga part d’in, a maimakon ta nufi part d’in su sai ta güdü zuwa nasu His Excellency, a tunaninta anan ne Kawai zata iya tsira, ga wani irin tsoro da shakar Abla da yashiga cikin zuciyar ta.

****** A d’an zuciye Abla ta jiyo tana ‘ko’karin ’kwace ri’kon da Big Boss yayi mata, amma ya ‘ki sakin hannun nata , sai bin kyakkyawar face d’inta da ta had’e yake da kallo, a d’an ‘kufule Abla ta furta “ Ni ka sakar mun hannu na”, a maimakon ya sakar mata hannun sai ‘kara janyo ta da yayi jikinsa, cikin rarrashi ya furta “ Sunshine!” ‘Kara tsuke fuska Abla tayi har lokacin tana san ‘kwace hannunta daga ri’kon da yayi mata , “ Hey Sunshine , Rigima , come here “, ya fad’a yana hugging d’inta , cikin muryarta kamar zatayi kuka ta 'kara furta “ Nidai ka sakeni na tafi “, ta fad’a tana ‘kwace jikinta daga hugging d’in da yayi mata , a zuciye ta juya zata bar d’akin ya ri’ko ta , lokaci d’aya Abla kamar me aljanu ta soma kokawar ‘kwacewa amma Big Boss ya ‘ki sakinta , ganin abun nata na ‘ko’karin yin worst ne yasa ya d’auketa gabaki d’aya ya kwantar da ita akan gadon da , sai da ya ri’ke sosai tukunna ta dena motsu mutsun da take , cikin ‘kan’kanin lokaci ta fara masifa , yadda take masifar nan mutum sai yayi mamakinta, hatta Big Boss kallanta kawai yake yana ‘boye murmushin da yake san kwace masa , “ It’s okay , Matar Oumar Farooq , nace fa Sorry huh? Bakin ki zai miki ciwo fa , kinga it’s okay am yours and Only , wannan duka da kikai haka ? Aushe dai matar soja ,soja ce “, turo baki Abla tayi tare da juya masa baya , juyo da face d’inta Big Boss yayi ganin yadda ta shagwa’be ta “ Wannan matar tawa akwai ta da kishi ba” d’an murgud’a bakinta Abla tayi tare da furta “ Ni babu ruwa na da kai , mun kwance “ ta fad’a kamar wata ‘karamar yarinya , eyes d’insa Big Boss ya d’an bud’e kad’an , a hankali cikin zuciyarsa ya furta“ Rigimammiya “, sai kuma ya ‘Kara kallanta ganin yadda ta kulle idanuwanta a dole bazata kulashi ba . Shima shiru yayi mata baice komai ba sai dogon gashin manta me santsin gaske da yake shafawa, kusan tsawan mintuna biyar yana abu d’aya , ajiyar zuciyar da ta soma ne ya dawo dashi daga duniyar tunaninta , mamakinsu fall ya kamasa kwana biyun nan ya Lura bacci baya mata wahala duk lokacin da ta kwanta sai tayi bacci . Bai kawo komai a ransa ba ya gyara mata kwanciyar tata duk da ya fara wası wasin baccin da yake kwana biyu , ‘karamin iska ya fesar a bakinsa tare da lullu’beta da duvet d’insa mai shegen laushin. Lokaci d’aya kuma ya had’e ransa kamar bai ta’ba dariya ba ‘karamun lips d’insa ya taune kad’an tare da shiga dressing room d’insa , bai d’auki wani dogon lokaci ba ya fito tare da barin d’akin bayan ya rage mata hasken d’akin.

Direct part d’in ya bari yana fitowa Victor da Anthony suka ‘karaso Inda yake a tsaye , agogon hannun sa ya kalla kafun ya d’an lumshe eyes d’insa , cikin Husky voice d’insa ya furta “ Bring her here “. Sun gane wa yake nufi sabida akan idanuwansu Harry ta fito daga part d’in a har gitse , cike da tsantsan girmamawar da suke masa suka sara masa tare da nufar hanyar part d’in His Excellency. 

         Harry kuwa tun data shiga part d’in His Excellency ta ra’be a ‘kasa jikinta sai faman karkarwa yake gabaki d’aya hannayenta ta d’ora aka kamar me shirin saka ihu. Shigowar su Victor da ta gani ne yasa ta saki ‘karamun ‘kara a guje ta haura stairs , ko takan elevator bata biba ta ruga a guje, duk uban stairs din nan haka ta dinga tsallake su har ta nufi falourn da tasan zata samesu. Ko sallama batayi ba sai ganin ta sukai a har gitse ta fad’o d’akin babu Wanda bai mi’ke ba sai His Excellency da yake kishingid’e a kan kujera, Uncle ne ya kalleta da mamaki “ Harira Menene haka babu ko sallama me ya same ki?”, a rud’e Harry ta furta “ Uncle please help me ni babu abunda nayi musu Suka biyoni suna duka na,” sai kuma ta juya şaitin Dadyn ta da ya mi’ke shima “Dady please kuce su rabu dani”, ajje cups d’in hannunsa His Excellency yayi kafun ya furta “ Me kikai musu?” Kuka ta fashe dashi ko kunyar ‘karyar da take bataji “ Babu abunda nayi musu Abbu , Wallhi babu abunda nayi musu”, shigowar su Victor ne yasa Abbu kallansu , tun kafin yayi magana cike da girmamawa suka sara masa “ Mai yasa kuka biyo ta ?” Victor ya amsa masa “Umarnin Big Boss ne “,   “ Me tayi masa ? “, a yanxu Anthony ne ya bashi amsa “ Sir we don’t actually know , he just give us an order “, wani kuka Harry ta fashe dashi tana girgiza kai , d’an shiru His Excellency yayi suma su Uncle ba suce komai ba sabida shirin da Abbu yayi , daga sama tayi muryar sa “ Follow them “ ai Harry na jin hakan ta mi’ke tsaye gabaki d’aya sun d’auka binsu zatayi sai kuma ta ‘kara saka wani gudun ta bar wajan suma su Victor suka bi bayanta , Uncle ne ya kalli His Excellency” bari na duba “ yana fad’an hakan ya bi bayansu Dadyn ta kuwa babu abunda yace.

   Harry ta na fitowa part d’in su Mamy ta nufa  güdü lokacin gabaki d’aya suna zaune a falourn har su Fanan da Momyn Harry sai ganin ta kawai sukai, Mamy ce ta furta “ Subhanallahi Me nake gani haka Harira ?” Cikin Sauri Harry ta ‘karaso wajan ta tana furta “ Mamy wallahi babu abunda nayi musu “, kallan ta Baby tayi tana ta’be baki “ Daga ganin ki ruwan munafukai ne dake “, ta fad’a cikin zuciyarta ,ita Eshaal tsoro ma ta bata data ga shigowar ta , Mamy kuwa da Momy Harry sai faman tanbayar ta suke me ya faru amma ta kasa magana sai furta “ Babu abunda nayi musu “ take . 
Chapter 87 · 0% Book details