← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 100

Sashe 33

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abla kuwa tana koma wa d’akin ta wayar da ta saka a charge ta d’auka da tsohon wayarta da little ya bata , wani irin farin cikine ya kama Abla lokacin da ta soma d’aukan number su Eshaal, sosai farin ciki ya kamata ba kad’an , cikin sauri ta bud’e data zata yi musu magana taga message d’insa dukda babu suna a number tasan shine “, Take care ”, shine abunda ya gani sai wani ‘karamun red rose da ke gefen message d’in, d’an ’karamin murmushi Abla ta saki batare da ta bashi amsa ba , Numbers d’in su Eshaal ta soma duddubawa , gabaki d’aya tayi musu sallama sai akaci sa’a Eshaal tana online , cikin sauri Abla ta furta “ Eshaal “ lokaci , itama Eshaal amsar “ Wake magana “ ta turawa Abla , d’an murmushi Abla ta saki kafin tayi mata reply da “Abla “ Eshaal na ganin message d’in ta bugowa Abla vidoe called ,Abla na d’aga wa Eshaaal ta saki wani ihu , daga cikin wayar tana iya jiyo sautin muryar su Baby suna tanbayar ta Menene , tana ce musu Abla , itama Baby ta fuske wayar , bata ce komai ba ta saki wani ihun itama , Same abunda Fanan tayi kenan su kad’ai sai faman ihu suke , Abla kuwa babu abunda take banda dariya ganin yadda gabaki d’aya sun kasa magana suma , da ‘kyar ta iya furta “zaku kashin dodan kunne na fa “ tsagaitawa sukai kafun Fanan ta d’an harare ta “ Allah Abla baki da mutumci, kınasan yadda kika d’aga mana hankali kuwa ? Babu irin nemanki da bamuyi ba fa , “ d’an murmushi Abla tayi mata “ Am sorry Aunty Fanan , lokacin da na koma d’auko Book d’ina naga wasu guys d’in su biyo ni naso nazo inda suke amma ganin su da nayi suna da yawa yasa na gudu na bar makarantar Aushe akwai Wanda suke bina a waje, in short wata mata ce ta temakamun ta tafi dani a cikin motar ta “, ajiyar zuciya suka saki gabaki d’ayansu kafin baby ta furta “ Amma yanxu kina ina please? Naga kinyi fresh sosai har ‘kiba da kumatu kin soma , brothers d’in ki sai neman ki suke “ ,  kallansu Abla tayi ta cikin waya ganin yadda suka zuba mata idanuwa gabaki d’ayansu “ karki damu muna tare da su already “ da mamaki suka furta “ kuna tare ?” Kusan lokaci d’aya , kanta Abla ta jinjina musu , da sauri Eshaal ta furta “saura 2 days a yi hutu fa kuma kina America amma bazaki iya kiran muba plx? Gabaki d’aya fa mun shiga damuwa “,  kuyi hakuri “ cewar Abla kafun ta cigaba da magana “ Bana America ynxu , muna Nigeria gabaki d’ayan mu” yanxu ma kusan lokaci d’aya suka furta “ Nigeria ?” Kanta Abla tayi knodding da Sauri Fanan ta furta “ Nigeria a wani state ?” Hannu Abla ta d’aga alamar itama bata sani ba , d’an hararar ta farar tayi “ Allah Abla wani lokaci kema d’innan ko ? Taya kina gari bakisan Garin da kike ba ? Muma ai mun kusa zuwa nigeria , gamuwata dake baza tayi kyau ba “ gabaki d’aya sai suka ‘kyal’kyale da dariya jin abunda Fanan tace , cikin ‘kan’kanin lokaci Suka soma hirar su da suka dad’e basu yi ba , idan ka kalli fuskokinsu gabaki d’aya zakaga farin ciki da annashuwa a tattare dasu. Gabaki d’ayan su babu Wanda beyi missing moment d’insu da suke tare ba shiyasa saka ci gaba da hiran su cikin so da ‘Kaunar junan su , suna yi suna tsokanar juna kamar yadda suka saba , cikin tsokana Baby take furta “ Abla nifa naga kinyi kumatu kin murmure Anya ba d’an Baba bane”, harara Abla ta banka mata , lokaci d’aya gabaki d’aya suka ‘kyal’kyale da dariyarsu, kafun su cigaba da hiran da suke gwanin burgewa.

*************
******************
Karfe 5:10 pm Big Boss ya shigo cikin gidan , direct part d’insa ya wuce yana shiga ya tarar da Bobo da Sauban a kan kujera suna jiran dawowar sa , dan suma basu dad’e da shigowar ba , babu Wanda ya kalla a cikin su zai wuce sauban yayi saurin dakatar Dashi “ Bata part d’in “ dakata wa da tafiy Big Boss yayi tare da juyowa , wani irin dariya sauban ya kyal’kyale da ita hatta shima Bobon murmushi yake yi , ganin sauban ya’ki tsayawa ne yasa ya dakatar Dashi cikin sauri ganin yadda Big boss ya had’e face d’insa “ Sorry Big Boss , Nanni da Diidii sun d’auketa sunce sai ka kawo musu lefe da sadaki”ta’be baki Big Boss yayi kafun ya furta “ Matata ce ko matar su ?”, sakin baki Bobo da Sauban sukai jin abunda yace , cike da mamaki sauban ya furta “ Yaushe kayi zurfi haka ? Ai kasan part d’insu, sai kaje ka d’akko ta amma please kayi hakuri mana , saura 1 week ayi taron family atleast zuwa nan nasan su Didi zasu dawo maka da ita , cikin tsuke fuska Big Boss ya furta “ matsalar su ce wannan bamu da had’i dasu , itama tsohuwar nan zanyi maganin ta “, Didi cewar Bobo, lips d’insa Big Boss ya taune kafun ya d’auki phone d’insa yayi dialing wani number , ringing d’aya d’aya kuwa , bai jira Wanda ya kira yayi magana ba ya furta “ Akawo Simba “ daga haka ya Kashe kiran yayi wucewarsa ya barsu baki bud’e , wani irin dariya bobo ya ‘kyal’kyale da ita lokacin da Big Boss ya bar wajan sannan ya kalli sauban “ dagasken fa so yake ya haukata mutanan gidan nan , Zakin sa zai kawo wa Didi, da alama lokacin komawar ta saudiya yayi”, shima sauban dariya ya saki yana hango scene din su da Hajiya Diidi.

   ****Big Boss na shiga cikin d’akı button d’in rigarsa ya soma ‘balle wa rai a ‘bace , number d’inta yayi dialing Daidai lokacin da tafito daga wanka tun bayan d’akko ta da Nanni sukai suka dawo da ita nan , cikin sauri ta d’auki Hijab d’inta ta saka fuskarta sai d’igar da ruwa take, sai da kiran ya tsunke gabaki d’aya takasa d’aga wa , a karo na biyu kiran ya shigo wayarta , shahada kawai tayi ta d’aga kiran duk da bata kallesa sosai ba taya yadda ya had’e ransa sosai, ‘kara tsuke fuskarsa Big Boss yayi kafun ya furta “ take that hijab off “, waro masa ido Abla tayi dan towel ne Kawai a jikinta , shiru tayi batare da tace masa komai ba , cikin ‘bacin rai ya furta “ Don’t make me repeat my self”,
Abla cike da taurin kai ta’ki cire Hijab d’inta dan bazata yadda yaganta babu kaya ba , ‘kasa ‘kasa ta furta “ Nifa banasan takura, haka mutum bai san komai ba sai dai ya ta’ba jikin mace , wallahi bazan cire ba “ da kamaki Big Boss ya kallesa , ranshi ba ‘karamun ‘baci yayi ba shiyasa ya daka mata tsawan da saura kad’an wayar hannun ta ta fad’i gabaki d’aya ya rikid’e ya koma mata asalin Big Boss d’insa , yadda yake magana zaka gane yadda ranshi ya ‘baci sosai “ Ni kike cewa babu abunda na saki sai ta’ba jikin mace ? Jikin kine ko?I will never touch it again , wait and see , in 3 weeks time zan kawo miki Macen da tasan daraja da kiman mijinta, my marriage will be in next 3 weeks time “, yana gama maganar sa ya kashe called d’insa , hankali Abla ba ‘karamun tashi yayi ba jin abunda yace gabaki d’aya sai taji ta tsani kanta , “ Aure ?” Shine abunda ya ‘kara Dakar mata zuciya , juwar ce ta fad’ar da ita ,lokaci d’aya ta soma kuka , ‘kirjinta sai sama da ‘kasa yake babu abunda yake kuwwa a cikin kunnanta sai kalmar Auren da yace mata , ta kasa göğe moment d’in yanzu musamman yadda taga ransa ya ‘baci , irin ‘barin ran da bata ta’ba gani ba ya fi komai d’aga mata hankali, cikin Sauri ta janyo phone d’insa zata bashi ha’kuri, tana dialing number ta jita a kashe, “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” shine abunda Kawai take iya furta wa Sabida yadda taji kanta na sarawa , zuciyarta na mata ba dad’i kamar wacce ake caccaka da wu’ka, wani irin murd’awa cikin ta yayi da ‘karfin gaske, da ‘karfi ta saki ihu tana dafe cikin ta dake mata tsananin ciwo, cikin ‘kan’kanin lokaci period d’inta ya ‘balle mata ,ta fad’i a wajan sumammiya….

IBTISSAM
      ( A heart touching story of love and destiny)

Story & written 
      By
Mss Lee   

                     09134652921.

    TALLA!! TALLA!!! TALLAH !!!!!!!

SHIN KUNSAN WACECE HAJIYA NUSAIBA BR~B ZURU ?❤️

HAJIYA ~ NUSAIBA DR~B ZURU

MAMALAKIYAR ZIMH ISLAMIC AND MEDICINE DAKE RINGH ROAD A KANO NIGERIA
Tazo muku da ingantattu ko sahihan magungunan mata masu inganci, ba’anan kad’ai ta tsaya ba har da na cututtuka da Turarukan wuta , Humra masu shegen ‘kaushi . Abun Alfaharin kuma tana bada sarı cikin sau’ki, sannan kuma suna aikawa duk inda mutum yake afad’in duniyar nan. 

Duk wacce ta siya magungunan Hajiya Nusaiba Dr B zuru, taga be yi mata aiki ba tazo za’a dawo miki da kudin ki . 

KA’DAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKE SIYAR WA

1️⃣ Hadin amarya
2️⃣Hadin mai jego
3️⃣Hadin sabon budurchi
4️⃣Hadin Kaza Yar’Suddan
5️⃣zuma -Tsumi- Tabaje da sauransu
6️⃣Turaren Sandal ruuu& flastic Sandal
7️⃣ Hadin Hawwi domin inganta zafafiyar kauna
8️⃣Hadin bagadad,kahlij,kajiji,gafgaf dasauransu
9️⃣Hadin humra soyaya dole ta matan aure da normal humra

DON SAMUN ‘kARIN BAYANI KU NE META TA WANNAN NUMBER KAMAR HAKA : 
    08133647913 

   KANO NIGERIA 

LOCATION: RING ROAD BAYAN GİDAN MAN NAZARGO.

       SIYAN NAGARI MAIDA KU’DI GIDA

PAID BOOK

BOOK 2 
         S_____ 11
Chapter 33 · 0% Book details