← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 100

Sashe 53

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune Abla take cikin doguwar rigar material ash colour , fuskarta fiyau babu abunda ta saka sai rolling d’in mayafin ta da tayi, tun d’azu take kallan lokaci, time to time kuma tana kallan agogon d’akin , sosai ta ‘bata fuskarta kamar zatayi kuka, tunda tace batasan zaman nan yace zai maidata gida idan ya gama wani aiki har yanzu bataga shigowarsa ba, gashi gabaki d’aya ta shirya, ‘kara kallan lokaci Abla tayi akaro na barkatai ganin har yanzu bai shigo ba , ga kiran sallah da aka soma yasa ta nufi toilet a hankali tayi alwalarta,ko da zata tayar da sallah sai da ta ‘kara duba time ko zata ga shigowarsa amma har lokacin bata gansa ba , kwallar data tarar mata a ido ta share kad’an tana had’e fuskarta. Tana idar da sallan bata kuma zama a d’akın ba ta fito falourn. Babu kowa a falourn sai kamshi da sanyi Ac da yake tashi tako ina , sosai falourn yayi mata kyau amma sai tayi saurin cire hakan aranta dan so take ta koma gida, har yanzu tsoron abunda yayi mata mai fita daga ranta ba , hanyar da tafi tunanin ‘kofar fita ne ta nufa cikin takunta da har yanzu bai gama dawowa dai dai ba . A dai dai lokacin da take saka hannunta a kan handle zata bud’e, shima a lokacin Big Boss ya saka hannun sa yana ‘ko'karin bud’ewa , lokaci d’aya sukai karo da juna , da Sauri Abla ta furta “ Ouch “ tana dafe kanta , hannun ta ya ri’ko yana kallan inda ta dafe “ Sorry Sunsine, bari na duba miki ko kin bige “, ‘bata rai Abla tayi tana kawar da fuskanta , “ Ni banasan kamayar dani “ ya fahimci abunda take nufi shiyasa ya kawar da zancan ta hanyar ri’ke mata hannu “ bari kici abinci sai kisha magani, it’s like ciwan ya dena zafi ,let’s go “, kamar zatayi kuka taka ta soma tafiya ganin ya ri’ke mata hannu , idan tace zatayi musu kuma yace zai ‘kara ji mata ciwo har ‘kwalla ya soma sakko mata a fuskarta. Suna shiga d’akin waigawar da zaiyi yaga hawaye na sakko mata a fuska , cikin sauri ya kalleta “ Bakyasan zama dani shiyasa kike kuka ? It’s okay wipe your tears zan mayar da ke idan kika dena kukan “ cikin sauri Abla ta goge hawayenta ba tare da ta kalle saba , “ Bari nayi wanka first sai kici abinci ko ?” Pink lips d’inta Abla ta tsuke ba tare da tace komai ba , ‘karamin murmushi Big Boss ya saki kad’an “ ko zakiyi mun Nima ? Kinga jiya Nima nayi miki da baki da lapiya “ langwabar da kanta Abla tayi tana ‘bata fuska , hancin ta Big Boss ya ja kad’an “ Babyn nan kin iya shagwa’ba, amma please ki zauna waje d’aya karki sa mu fama ciwan mu”, yana fad’an hakan Abla ta tsuke fuskarta tana sunkuyar da kanta ‘kasa , murmushi yayi Sabida yasan daman hakan zatayi , bai kuma cewa komai ba ya zaunar da ita kan sofa tare da ajje wayarsa akan laps d’inta  tare da diamond watches d’insa “ Am coming Baby Doll “, yana gama fad’ar hakan ya nufi toilet. 
 Cikin ‘kasa ‘kasa da murya Abla ta furta “ Wai Baby Doll , Sun shine , sai da ka kusa kasheni , Allah sai ya saka mun ai”, ta ‘karasa tana d’an murgud’a bakinta kad’an , kamar Ance ta kalli wayar da ya ajje mata, haka kawai taji tana san d’aukar ta musamman da ta baro tata a gida shiyasa gabaki d’aya ta fijin kad’ai ci, Har zata kunna screen d’in wayar sai tayi sauri kuma ta ajje masa wayar ta sa , duk da haka idanuwanta na kan wayar haka kawai taji tana san kunnata, ‘kofar toilet d’in da ya nufa ta kalla sai kuma ta ‘kara kallan wayar , batare da tayi Tuna’nın zata kama ba kawai ta shafa screen d’in wayar , lokaci d’aya wani farin hannun mace ya bayyana a jikin screen d’in wayar daga ‘kasan hannun ta hannun namijine shima fari sosai ya saka fingers d’insa cikin nata lokacin da ya ri’ke, ‘karamin tsaki Abla taja kad’an zata ajje wayar idanuwanta suka sauka kan agogon hannun sa da zoban sa , kallan agogon tayi ganin dai shine , cikin sauri ta ajje mayar tana kifa kanta da jikin sofar, lokaci d’aya taji wani irin zafi da d’aci a cikin zuciyarta “ Daman nasan ba sona yake ba , akwai wacce yake so shine har da yi musu hoton?” Ta fad’a cikin zuciyarta , ranta har ya fara ‘baci ga wasu irin kwalla da suke san sakko mata amma ta hanasu. 

   Yana tsaye a bakin toilet tun d’azu hannunsa rungume a ‘kirjinsa , tun lokacin da screen d’in wayar ya kama ya fito daga toilet amma bai yi wani motsin da zata san ya fito ba Sabida yana so yaga reaction d’inta , ganin yadda ta ajje wayar rai a ‘bace ne yasa ya d’an saki wani murmushi iya kan la’b’ba, a hankali ya soma ya kowa zuwa inda take , motsin da ta soma jine yasa tayi saurin goge ‘kwallarta tana d’ago da idanuwanta , ganin yana tun karo inda take yasa tayi saurin mi’kewa zata bar d’akin, cikin Sauri Big Boss ya ri’kota , ‘ko’karin kwace hannunta Abla tayi har yanzu ta’ki kallansa “ Are  you jealous of her ?”, a fusace Abla ta fuske hannun ta , zata kuma wuce ya ‘kara ri’ko hannunta , cikin Sauri ta furta “ Ni ruwa zan sha kuma ni ina ru..Wana da ku”, kana kallan yanayinta zaka sa a ‘kufule take , yasan idan nace zai tsokane ta zai ja wa kansa rigima ne Babba shiyasa ya komar da ita kan sofa d’in , tana ‘ko’karin juya masa baya ya jiyo da fuskarta zuwa Side d’insa , wayar da ta ajje ya d’auka tare da bud’ewa gabaki d’aya yana saka mata wayar akan laps d’inta ,bata re da ta kalla ba tayi ‘ko’karin kauce kanta ya girgixa mata kai “ Uhm Uhm fa banasan rigima , kalla kawai zakiyi , just once “, a hankali Abla ta d’ago da kanta zata kalli wayar ta ‘kara kauce kanta,girgiza kansa Big Boss yayi kad’an, “ Hey ki kalla mana “, cikin sanyi jiki Abla ta kai dubanta kan wayar cikin Sauri kuma ta kallesa tana ‘kara kallan wayar , ba hannun kowa bane face nata da nashi da alama bacci take lokacin da aka d’Suka , gira d’aya Big Boss ya d’age mata “ No more kishi right?”, cikin sauri Abla ta rufe idanuwanta tana jin wani irin yarrr a jikinta musamman yadda yayi magana . 
“ In kin gama ‘boye face d’in zo ki shirya ni”, Abla bata san lokacin da ta d’ago da dara daran idanuwanta ba ta kallesa , “ Ki dena kallo na haka  if not akwai matsala “, cikin Sauri Abla ta d’auke kanta “ Ni yunwa nake ji fa ,”shima kansa Ya jinjina mata “ Dont worry bana so ki zauna da yunwa kada mu rame, give me few minutes “ Bai jira amsar taba yabar d’akin , kallan. Wayar da ya bari Abla tayi , d’an ’karamin murmushi ne ya bayyana akan face d’inta “ Yaushe aka d’auke ni wannan hotan ?”, rashin samun mai amsa mata tanbayarta ta yasa ta share zancen gabaki d’aya daga zuciyarta. 

************
Tunda Big Boss ya basu Black Card suka fita yawa tare dasu Anthony shiyasa gabaki d’aya wunin ranar basu shiga part d’in su Abla ba sunso yi mata suprise ne idan sun dawo daga siyayyar da zasuyi mata, Big Boss kuwa sun san baya gidan shiyasa basu damu da kiran saba . 

    Ana idar da sallar magrib Little da Prince suka nufi part d’in Abla da Siyayyar da sukayi mata , gabaki d’aya mamaki ne ya kamasu ganin yadda part d’in yake zagaye da security, basu kawo komai a ransu ba suka shiga cikin part d’in. 

  Fuskar Little cike da fara’a ya soma kwalla kiran sunan “ Lil, Lil”, yana jiran fitowar ta , ganin shiru ba’a amsa masa bane ya ‘kara kiran sunanta , Jenny ce ta shigo cikin falourn cike da girmamawa ganin su Little , kallanta prince yayi tare da ta furta “ Jenny kira mana Lil”, d’an shiru Jenny tayi sai da Little ya ‘kara furta “ Jenny baki ji abunda yace bane ?” Ajiyar zuciya Jenny tayi kafun ta furta “ she’s not around “, da mamaki Little ya furta “ Akwai inda taje ne ?” Ganin basu fahimci maganar taba yasa Jenny ta furta “ Since Morning da na fito ban ganta ba and na duba ko ina bangan taba, “ mi’kewa tsaye Little tare da nufar hanyar d’akin wani corridor “ Let’s me check it by my self , am coming “ shima haka gabaki d’aya Little ya duba ‘kasa bai ganta ba Sabida rud’ewa baiyi tunanin hawa sama ba tanbayar sauran part d’in , kai tsaye Number Big Boss dialing , kusan sau biyu yana kira baya shiga , kamar zaiyi kuka ya kalli Prince “ Yaya Prince shima wayar Yaya shiga , naga kamar Yaya Bobo sun dawo please zo muje su kira mana yaya “ cikin Sauri zasu bar falourn şai kuma Little ya jiyo yana Kallan Jenny “ Ki ajje mata a d’akin and ki kulle shi “ Tom kawai jenny tace bayan ta d’aukin kayan. 
  Direct part d’in su Yaya Bobo suka nufa dan yanzu shida Sauban a part d’aya suke hatta su Little d’in wani lokaci acan Suke zama . 
Chapter 53 · 0% Book details