Sashe 24
Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A na kiran sallah asuba Abla ta farka daga baccin ta kamar kullum , sai da tayi sallah tayi wankan ta kafin ta gyara ko ina na cikin d’akin da kanta , tana san fitowa falour amma gabaki d’aya bata san had’uwa dashi shiyasa ta koma ta d’auki azkar d’in ta tanayi, da ta tuno maganar auran da ya furta sai ta ya mutsa fuska duk da bata yadda da wani maganar aure da ya fad’a ba , a tunanin ta yayi hakane kawai sabida ya razana mutanan gidan shiyasa bata saka abun sosai a cikin ranta ba . Tana zaune har wajan ‘karfe 8:00am Daidai taji anyi knocking kamar bazata kula ba sai kuma ta furta”wanene?” Cikin ‘kasa ‘kasa da murya, Jennifer dake jikin ‘kofa ne ta amsa mata da “ Nice Ma’am “, d’an ajiyar zuciya Abla ta saki kafin ta bud’e mata ‘kofa , murmushi akan face d’inta ta gaishe da Ablan ga hannun ta da yake d’auke da babban tray da alama breakfast d’in tane a ciki, “ Na gode “ cewar Abla , murmushi Jennifer tayi mata kafun ta furta “ your welcome Mah “ ta ‘karasa zata fice daga cikin d’akin , itama Abla da Sauri tabi bayanta sabida tana san kulle wa , tun kafin ta saka hannu akan Handle d’in ’kofar Daddad’an ‘kamshin turaransa ya cika ko ina tun kafin mamallakin turaran ya bayyana, da ‘karfi zuciyar Abla ta harba , iriin harbawar da bata ta’ba ji tayi ba shiyasa tayi saurin dafe sai tin zuciyar ta , cikin Sauri ta saka hannu zata tura ‘kofar ya danno kai zuwa cikin d’akin. Kamar ba ita ba tana ganin sa ta had’e face d’in ta tare da juya masa baya ta koma kan kujera, tray d’in Abinci ta bud’e , lafiyayyiyar masar da ta gani ne yasa ta d’an murmusa kad’an dan ba ‘karamun tafiya tayi da Ita ba , guda d’aya Kawai ta saka cikin plate batare da ta kalle saba ta soma cin abunta. Cikin d’akin ya shigo kan d’aya daga cikin sofa d’in d’akin ya zauna da yake facing d’in ta , tana gani ya zauna a wajan ta ajje masan daniyar tashi daga wajan , “ Go back !” Ya furta a hankali kamar bada kowa yake magana ba , Zata musa masa ya had’e ransa sosai kamar asalin yadda ta san sa a Big Boss d’in sa , a hankali ta koma ta zaunan ba tare da ta kalle saba , d’au lips d’insa ya ciza kad’an yana lumshe eyes d’insa , “ Ina kwana…” ta fad’a a hankali sarai ya jita amma ko motsawa beyi ba ballantana ya nuna yasan da zamanta , hakan da yayi kuwa ba ‘karamin ‘kular da Abla tayi ba shiyasa a zuciye ta tashi zata bar Wajan ya finciko hannunta ta fad’o jikin sa , a tare zuciyoyin su suka garba musamman Abla ta rufe idanuwanta gagam gabaki d’aya Tuna’nın ta ya bata fad’uwa zatayi , ‘kamshin turaran sa da taji daf da ita ne yasa ta bud’e idanuwan ta , da Sauri ta yün’kura zata mi’ke yayi hugging d’in ta a jikinsa “ Me yasa bakya jin magana ne ? Huh! You’re really stubborn , yanzu fushin me ake dani ?”, kawar da kanta Abla tayi gefe “ ka sake ni” amaimakon ya saketan sai ya ‘kara matseta a jikin nasa , “ Baki iya gaisuwa ba ?” Shiru Abla tayi masa , ganin yana matso da face d’in sa kusa da ita tayi saurin furta “ Ina kwana ?” Shiru Big Boss yayi mata kusan tsawan mintuna biyu kafin ya had’e lips d’insu ya bata wani irin bazatan kıss , Daidai saitin kunnan ta ya furta “ İrin wannan kaisuwar nake so”, a tunanin ta bazai ji abinda yace ba dan duk a zatan ta cikin zuciya tayi maganar “ ‘Dan iska , mayan mata kawai” wani irin mugun kwalla Big Boss ya jefa mata , cikin Sauri ta toshe bakin ta da duka hannayen ta ganin yadda jijiyoyin kansa suka soma fito ba sosai , cikin tsananin ‘bacin rai ya kalleta “ Ni kike cewa Mayan mata Sabida ya ta’ba ki ?” Narai Narai Abla tayi masa da idanuwa kamar me shirin yin kuka , kawar da kansa yayi daka side d’in ta kafin ya sake ta gabaki d’aya a jikin sa, cikin sauri Abla ta mi’ke tsaye tana kallan sa cike da tsoro , babu abunda yace mata sai gashin kansa da ya d’an ta’ba kad’an , ko sau d’aya be ‘kara d’ago face d’insa ya kalletaba ya bar d’akin.
Yana ficewa a cikin d’akin ta fad’a nan gado , bata san dalili ba jin kuka tayi na zuwar mata ga zuciyar ta da take ji ba dad’i shiyasa ta rufe idanuwanta cikin duvet d’in gadon tana cigaba da yin kukan ta .
****
Big Boss kuwa yana fitowa daga cikin d’akin direct part d’in ya bari gabaki d’aya , cikin Sauri Victor ya bud’e masa farar Chevrolet da sai faman shining take ko alamar datti babu a jiki , a hankali ya ‘karasa cikin motar yau ko da sojojin sa bazai fita dasu ba shiyasa yana shiga ciki Victor yayi saurin zagayawa driving seat ya zauna tare da tada motar.
daga inda yake yana iya hango yadda su Harry suka ta aske flowers d’in wajan ko sai kunbure Kunbure yake ga wajan da suka ‘bata gabaki d’aya , Surry sabida haushi da sun aske flowers d’in zata bugesu da ‘kafa duk su tarwatse a filin wajan , Hatta Madam Sarah da taje ta tattauro su babu abunda tace musu har suka gaba ‘bata filin wajan. Jin gina kansa yayi yana ‘kara lumshe idanuwan sa har suka bar cikin gidan .
Sai da Madam Sarah ta tabbata sun jigata sosai ga filin wajan da suka ‘bata sannan ta saka a basu tsintsiyoyi, d’an Hararar ta Yasmeen tayi kafun ta furta “ ke kuma wai wacece da zaki ce dole sai munyi abunda kike so ? Karki manta kema fa kamar baiwa kike ..” tasss Madam Sarah ta tsinka mata mari kafin ta nuna mata filin wajan “ fara tsanlan kwad’o”, sakin baki yan matan sukai gabaki d’ayan su jin abunda Madam Sarah tace , Yasmeen zata kuma magana Madam Sarah ta fito da wani ba’kin belt na sojoji ba shiri yasmeen ta soma tsallan kwad’o abunda ko uwar ta bata ta’ba sata ba kenan , fuskar Madam Sarah ba fara’a ta nunawa su Harry compound d’in wajan, “ Minti talatin na baku ku irga gabaki d’aya abubuwan nan da suka zubar ,” ta ‘karasa tana nuna musu shokokin Wajan . Itama Harry a zuciye ta mi’ke tana nuna ta da yatsa “ wai me kike ta’kama Dashi ne ? Ance miki mu dabbobine kamar ki da zamu zauna muna yin abunda kika ce mana ?” Itama tasss madam Sarah ta d’auke fuskar ta da fari kafin ta nunata “ ki d’age ‘kafarki d’aya sannan ki d’aga kanki sama “ wani irin yawu Harry ta had’iye ganin rashin mutum cin Sarah, ga Yasmeen da gabaki d’aya ta galabaita sabida bata saba yin tsallan kwad’an ba , cikin sauri su Kübra suka soma tsince ganyan da Dagaske sun fahimta Sarah ba raga musu zatayi ba , sun fi 20 minutes suna abu d’aya da Harry ta saukar da ‘kafarta zata ji saukar belt , itama Yasmeen gabaki d’aya fuskar ta ta ‘bacı da hawaye Sabida yadda taji ‘kafafun ta suna mata zafi , amma ko kusa babu me gigin bata hakuri a cikin su ganin yadda take hukunta su.
Amal ganin tana ‘ko’karin mutuwa ta tsugunna itama ta soma kuka “ Dan Allah Dan annabi badan muba kiyi hakuri , ni wallahi bazan iya yin komai ba , kashi nake ji kuma ko a Wana lokaci zan iya yinsa , Nidai wallahi nabi Allah da manzan sa na biku ni daga yanxu ma da charbi zan dunga yawa amma dan Allah kuyi hakuri “, itama Yasmeen da face d’inta tayi jina jina ne ta rarrafo wajan ta itama “ Nima gaskiya bazan iya ba kiyi hakuri , Indai tarbiyya ne daga yanzu mun d’auka ko kyankyaso bazasu ‘kara yi wa magana ba balantana masu aiki “, a wannan Karan harda Harry a masu bata hakuri dan dagasken gaske sai da ta cirewa Harry iskancin da ke kallanta , fuskarta tata sai naso take yi , sun dad’e suna bata ha’kuri kafun ta furta musu “ follow me “ da sauri suka bita a baya kuwa , part d’in da suka ga an nufa ne suka soma rarraba idanuwa kowa yana tunanin abunda zai biyo baya . Cikin ‘kayataccen falourn part d’in su Abla suka shiga , gabaki d’ayan su sakin baki sukai suna kallan yanayin cikin d’akin da ko kwatan kyau nasu bai kai ba “ seat “ cewar Madam Sarah , Harry da saurinta ta nufi d’aya daga cikin kujerun zata zauna M. Sarah ta daka mata tsawa “ on the floor ,” ba musu kuwa su Amal tun kafun ta kallesu suka zauna a ‘kasa idan ka kallesu sai sun baka dariya da tausayi dan duk ado da attachment d’in da suke sakawa yau ya ‘baci sai suka fito sak masu aiki.