← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 100

Sashe 62

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

***** Baby da Eshaal suna shiga d’akin da aka saukesu wanka suka farayi , suna zama aka kawo musu lafiyayyan abinci mai rai da lapiya , sabida gajiyar hanya basu wani ci abincin sosai ba , kallan Baby , Eshaal tayi “ kina samun Abla kuwa ? Kusan 4 days yanzu bana ganin ta online “ itama Baby cikin kalar damuwa ta furta “ Abunda yake raina Kenan , bansan dalili ba haka kawai nake jina wani iri, amma bari ne kira mana Fanan Ko tasa meta “ ta ‘karasa tana kiran Fanan Vidoe call, ringing biyu Fanan ta d’aga “ Ina kuka shiga ? Gabaki d’aya kuntayar mun da hankali ? Ban same ku ba ban samu Abla ba itama kamar had’in baki Allah yasa lapiya ko kun same ta ?” Da mamaki Baby ta furta “ Baki same taba kema ? Anya lapiya kuwa? Gaskiya jikina baya bani lapiya we have to do something gashi bamusan a Wana state take ba balantana mu nemeta “ cikin sauri Fanan ta furta “ Don’t tell me you guys are in Nigeria ? Na manta gabaki d’aya fa , oh my god kuna ina yanzu ?” Eshaal ce ta amsa mata da Lagos , cikin zaro ido Fanan ta furta “ Woow  muna the same state kenan ? Let’s meet up tomorrow sai muyi maganar rashin samun Abla cikin nutsuwa right ?”  Okay cewar Baby, duk jikinta yayi sanyi  “ Ku bari zan kira ku later , yanxu nasan kuma a gajiye küke , Nima nasan Mamy yanzu nema na take , See you guys Bye “ suma bye d’in suka ce mata kafin Baby tayi hanging kiran “ Baby kamar Momy batayi farin ciki da zuwan mu nan ba ?ta’be baki Baby tayi “ Toh kar tayi mana ba Dady ne yace mana muzo ba ? Ni kinga karma ki soma yi mun ‘korafi Bacci nake ji wallahi ‘kafafuwana tsami suke mun , in bazaki iya bacci ba sai ki zauna kiyi salati” ta ‘karasa tana hawa kantameman gadon d’akin. “ Allah ya shirye ki “ cewar Eshaal itama tana hawa kan gadon. 

**********
Bobo 

    Tunda Abbu ta bar d’akin yake tuna moment d’insu dashi, bai sai Menene yake shirin faruwa ba , tun d’azu yake jin gefen idanunsa nayi masa rawa Sosai , Allah ma ya sani yana gudun abunda zai had’a Big Boss da abbu inda ba zuciyar sa ce ta sauka ba , hakan kuma da kamar wuya dan yasan wanene Big Boss , yana da zuciya sosai, kullum adduar sa Allah ya sassauta wa Big Boss fushin da yayi, yana tsoro da gudun halin da Little zai shiga idan ya gano komai , Wanda suma hakan sosai zai shafesu.

********** HAJIYAR AMERICA 

Tana zaune cikin wani ‘kayataccen falourn ta akan cushions masu shegen laushi , Sallamar da akayi ne yasa ta d’ago da fuskarta tana kallan hanyar shigowa fuskarsa cike da tsananin farin ciki sanin Wanda zai shigo , ba kowa bane face His Excellency, shima fuskarsa a sake cikin walwala musamman kasancewar da yayi da Bobo, sai yake ji kamar wani sashi ne na ciwansa ya fara warkewa. 
     A kusa da ‘kafafunta ya zauna shima “ Mama Barka da zuwa , na same ku lapiya ? Ya ‘karfin jiki ?” Murmushi Mama tayi tana kallan mafisoyiwar d’an ta a cikin idanuwanta “ Duk wannan tanbayar ni kad’ai ? Na d’auka ka manta da nine kamar yadda ‘kanwar ka bata zoba itama “, cike da girmamawa His Excellency ya furta “ tuba muke Mama, itama nasan a ko wana irin lokaci zakigan ta, mun same ku lapiya ?” Kallansa Mama tayi sosai batare da ta amsa masa ba “ Farin cikin da na gani kwance akan fuskar ka ya tabbatar mun da kana cikin tsananin farin ciki, mai ya faru ? Mai yasa tsananin farin cikin da kullum nake san gani ?huh” wani murmushi His Excellency ya saki “ ita kad’ai ce wacce take fara hango muryar na ko akasin ta , sai matar da haryau da tunanin ta yake kwana yake tashi “ uhmm ?” Cewar Mama tana jiran ‘karamin bayanı , shima maida hankalinsa yayi sosai akanta kafun ya furta “ Mama daga ‘karshe na gansu, na gansu Mama “ kallan rashin fahimtar maganar sa Mama tayi fahimtar hakan yasa kai tsaye ya furta “ Yarana Mama , na gansu suna tare da ni cikin gidan nan “ mi’kewa zaune Mama tayi sosai kwallar har ta soma tarar mata “ Kanaso kace mun jikokina? Jikokina suna gidan nan ? Mai yasa baku fad’a mun ba tuntuni sai yanzu ? Ina san ganin su yanzu ko zuciya ta zatayi sanyi , Dan Allah ka kaini wajan su “ yadda yağa tana san Tashine yasa ya ri’ke mata hannu, “ Na ro’keki Mama ki zauna , ki fara hutawa tukunna , kınsan jikinki yana bu’katar Hutu , zuwa anjima nayi miki al’kawari zaki gansu insha Allah “ sai a lokacin Mama ta saki a jiyar zuciya , Sabida tsananin farin cikin da ya kasa ‘boyuwa aka fuskarta sai da tayi sujjada tana ‘kara godewa Allah , ita kad’ai sai faman addua take tana share ‘kwallar farin ciki. Shima Abbu murmushi Kawai yake ganin tsananin murna akan mahaifiyarsa da ya dad’e bai gani ba . Ya dad’e a wajan ta kafin shima ya koma ‘bangaransa. 

********
            ************
                          ***************
Chapter 62 · 0% Book details