← Book details Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 100

Sashe 64

Ibtissam Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******
“Little ka tashi zan kira maka Yaya kaji? It’s a Lie abunda ta fad’a please ka bud’e idanuwan ka, zan kira maka Yaya Big Boss , zan goya kama please ka bud’e idanuwan ka ,” shine  abunda Prince yake iya furtawa hannun sa na cikin na Little da ya ri’ke gam a hannunsa , cikin sauri Bobo da ya ‘karaso wajan ya ta’ba ‘kirjin Little da Sauri  yana danna masa shi, yana dannawa yana furta “ Hey Öpen your eyes “, sosai ya ke danna ‘kirjin Little babu Wanda jikinsa baiyi sanyi ba , kowa kaga yanayinsa zakaga tashin hankali kwance a fuskokinsu, Uncle ma kasa zama yayi sai zamewa da yayi ya zauna akan kujera. yana ‘kara dannawa nunfashin Little ya dawo , cikin Sauri Bobo ya kalli prince da yi masa ya kawo masa ruwa , zai tashi Abdul-Samad yayi saurin ‘karasowa wajan yana bud’e masa ruwan, kallan Little , Bobo yayi sosai sabida yadda yake sakin a jiyar zuciya idanuwansa a kulle har lokacin , Shima Bobo a jiyar zuciya ya sauke kad’an yana ri’ke hannun Little guda d’aya “ Little ?”, Uhmm kawai Little ya bashi amsa yana ‘ko’karin bud’e idanuwansa , “ Yaya dagaske ne abunda suke cewa ?”,kamar Wanda aka ri’kewa murya dan da’kyar yake iya magana,shirun da Bobo yayi masa ne yasa ya fara bud’e idanuwansa “ Yaya”, kai tsaye Bobo ya bashi amsa “ They are not our family, we don’t share are bones with them “, 
   Cikin sauri Little ya mi’ke tsaye , bai tsaya a ko ina ba sai a gaban Nanni da farfad’owar Little ya ‘kara tunzura zuciyarta, a tunanin ta shikenan mutuwa zaiyi aikin ta zai dawo cikin sau’ki sai taga ba hakan bane , kallan Little da ya ‘karaso Wajan ta tayi “ Dagaske ne abunda kika fad’a? Shine wanda ya haifemu? Nan kuma Familyn süne gabaki d’aya?” Shiru Nanni tayi masa tana Kallan sa, kowa na cikin falour ita yake kallo musamman Bobo da Sauban da ransu ya soma ‘baci ba kamar Bobo da ya hassala sosai , wani shegen murmushi Nanni ta saka tana kallan Little , tana ‘ko’karin yin magana His Excellency ya daka mata tsawa “ Na haneki da furta ko wace kalma AINA’U, idan kika kuskura naji sa’banin umarnina zanyi mugun sa’ba miki”, ko da Nani taji His Excellency ya kira sunanta ya zuciyarta sai data buga amma duk da hakan zuciyarta a bushe take da san cinma burinta ta ko wace hanya, “ Little Dare yyi let’s go , okay ?” Cewar Bobo yana mi’ko masa hannu, kallan Bobo yayi sannan ya kalli Nani da take kallansa kuma , Uncle kallansa yayi yana jiran jin me zai ce “ Yes Lil dare yayi and kasan dokar yayan ka ko?”, ‘bata fuska Little yayi fuskar sa ta soma yin jaa sosai kamar ba Little d’in su ba “ Am sorry Yaya babu Inda zani sai kun fad’amun abunda kuke ‘boyewa ..” bai ‘karasa maganar saba Sabida muryar Big Boss da sukaji kamar daga sama “ How Dare You ?huh” gabaki d’aya falourn sai kowa ya Mayar da kallansa kan wanda yayi magana , su Eshaal suna ganin sa Suka zaro idanuwansu gabaki d’aya kamar munafukai suka ‘buya a bayan Mamy da Momy , suma sauran yaran gidan gabaki d’aya mi’kewa tsaye sukai kowa yana gudun abunda zai faru, hatta His Excellency da Uncle sai da suka mi’ke tsaye , Ran Big Boss sosai yake a had’e kamar bashi ba dan yayi bala’in had’e fuskarsa, jijiyoyin wuyansa sosai suka fito waje ga gashin kansa da ya saki gabaki d’aya a gadan bayan sa , Bobo na ganin shigowar Big Boss ya mayar da kallansa zuwa saitin Prince , cikin Sauri prince ya d’auke fuskarsa ganin irin kallan da Bobo yake jefa masa . 

   “ Yaya” cewar Little , batare da Big Boss ya kallesa ba ya furta “ To your rooms now .” Zai yi magana yayi saurin yin shiru da bakinsa sabida kallan da Big Boss ya jefa masa da jajayan idanuwansa , Prince ma cikin Sauri ya ri’ke hannun Little , gabaki d’aya mutanan falourn Big Boss suka zubawa idanuwa musamman Mamy da Dadyn su Eshaal da suke mamakin canzawar Big Boss . Babu Wanda ya kalla a cikin falourn zai juya Nani da take tunanin bai isa yayi mata komai ba ta furta “ Ina zakaje Farooq ? Mai yasa kuke ‘boyewa yaran nan a salin iyayansu? Ko kana so ko bakaso dole Susan cewa nan d’in ahalinsu ne , mutumin dasuke rayuwa dashi mahaifinsu ne sannan mahaifiyarsu ma..” wani iriin gigitaccen tsawa Big Boss ya daka mata cikin tsawar ya furt “ I said to your rooms “ ganin yadda su Little suka tsaya, itama Nani cikin d’aga murya ta furta “ Ko kana tsoran Little yasan mahaifiyarsa ta gujesa tun yana ‘karami ko d’aukarsa bata ta’ba yi ba?” Cikin sauri Little da prince da suka soma tafiya suka dakata a hargitse , Big Boss da jijiyoyin wuyansa suka gama fitowa bai san lokacin da ya kai mata wani irin sha’ka ba , Bobo na tsaye ko sau d’aya bai motsaba sabida sha’kar da yayi wa Nani, Sauban na ‘ko’karin ’karasa wa Wajan Bobo yayi saurin ri’ke masa hannun sa . Cikin kakkausash shiyar murya Big Boss yake. Furta “ Me yasa dole sai kin ‘kure ni ? Mai yasa kuke san ‘küre ni ?” Nani babu abunda take sai zare idanuwa Sabida sha’kar da Big Boss yayi mata , cikin ‘karfin hali Dadyn su Eshaal ya nuna su Abdul - Samad “ mai kuka tsayayi? “ sai kuma ya juya yana Kallan Big Boss “ Farooq karka kashe ta mana , kayi hakuri komai a bishi a sannu, ka sake ta kaji “, amma ina Şam ko kusa Big Boss bai sake tanba sai ma kara sha’ke tan da yayi Nani sai faman san kwace wuyanta take dan ba ‘karamun mugun sha’ka Big Boss yayi mata ba , cikin sauri Sauban ya fusge hannun sa ya nufi Big Boss , amma yana zuwa Big Boss ya hanka d’asa sai da ya kusa fad’uwa cikin sauri Bobo ya tare sa , Abdul_Samad ma da yayi ‘ko’karin zuwa wajan sa lokaci d’aya Big Boss ya Sauke masa nashi kasan marin. Gabaki d’aya d’akin sai ya nemi hautsinewa His Excellency babu abunda yake furtawa sai “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”,  ‘kara Prince ya saki da ya ja hankalin kowa na gidan banda Big Boss da ko saud’aya bai jiyo ba , cikin d’aga murya Prince ya furta “ Yaya Big Boss, Little “,  juyowa Big Boss da Bobo sukai lokaci d’aya ganin yadda Little yake aman jini ne yasa Big Boss ya saki wuyan Nanni tare da hankad’ata baya tana shure shure Sabida mugun sha’kar da Big Boss yayi mata , Little na ‘ko’karin fad’uwa ’kasa cikin zafin nama Big Boss ya tare sa ya fad’o jikinsa a sume. Gabaki d’ayan sa Big Boss ya d’aga sa kamar yaro kafun ya jefawa Nani wani irin mugun kallo da sai da ta d’auke fuskarta a har gitse , cikin zafin nama ya bar part d’in, Bobo da prince suka yi saurin bin bayansa, Uncle da His Excellency ma cikin sauri suka biyo su shida su Uncle Adam, har ya zo fita ya jiyo da fuskarsa saitin Nani “ Na rantse da Allah idan ran d’ana ya salwanta sai na ki ya salwanta kamar yadda kika yi ‘ko’karin yi , daga yanxu ba sai gobe ba na haramta miki anfani da ko kwandalata Sabida kudin ya rana ne da kike san halakawa “, zabura Nani tayi zata yi wa His Excellency magana ya bar Wajan , cikin Sauri ta mi’ke ta nufi Mama da itama take ‘ko’karin Bin bayansu, kafin ta yi magana Mama ta d’auke fuskarta da maruka har guda uku “ Sha sha sha kawai, ki jira hukunci na “, kasa motsi Nani tayi a Wajan , Mamy ma kallansu Eshaal tayi “ Yarana ku zauna , idan kuna jin bacci kuje ku kwanta , ga ‘kawa ma nayi muku yanzu zamu dawo “, a sanye gabaki d’aya suka amsa mata kowa da abunda yake masa yawo cikin zuciya , kallan budurwar Baby tayi tana sakar mata murmushi , itama martanin murmushin ta mayar mata, gabaki d’aya a falourn zugun zugun suka zauna suna Tuna’nın abunda zai faru. 

****** ABLA 
Tunda ta koma part d’in wanka kawai tayi ta zauna, haka kawai taji komai na gidan yayi mata girma shiyasa ta ki zaman baya mata dad’i gabaki d’aya , har zata d’auki wayarta sai kuma ta Fasa ta kwanta , Ita kad’ai sai faman juyi take akan gado , da ‘kar bacci ‘barawo yaci ‘karfinta. 

**********
***************

Big Boss direct wani waje ya nufa a cikin gidan ,yadda tsarin komai yake mutum sai ya sha mamaki dan gabaki d’aya part d’in sai yayi kamar da asibiti Sabida kayayyakin Wajan ga warin magunguna Suma. Bai tsaya a ko ina ba ya nufi sama ko takan Elevator bai biba sai steps da yayi cikin Sauri. ‘Dakin farko Big Boss ya shiga da Little tare da kwantar dashi a Wajan da ya fi kama da d’akin asibiti sa’banın gadon d’akin da yake babba yanda mutum zai huta sosai, yana kwantar da shi bai tsaya cire masa Rigaba ya ‘barkata da hannunsa biyu, Bobo na shigowa taimakon gaggawa ya soma bawa Little har saida nunfashin sa ya dawo Daidai,cikin ‘kan’kanin lokaci suka dawo da nunfashin Little normal sai vantilatör d’in da suka saka masa a hanci yadda nunfashin sa zai tafi Daidai. 

     Tunda Bobo yaga yanayinsa bai ce masa uffan ba sai barin d’akin da yayi dan yanzu ran Big Boss a ‘bace yake sosai, barınsa a wannan lokacin shi kad’ai ne Alkairi. Har Bobo ya fita bai zauna ba bai kuma dai na kallan Little da yake kwance ba har lokacin, hannu d’aya ya saka yana ramutsa gashin kansa , ga lips d’insa da yake ciza da ‘karfi da har saida ya fasa le’ben nasa . 
Chapter 64 · 0% Book details